Hambararren shugaban Sudan Omar al-Bashir zai gurfana a kotu

Ba a sake ganin al-Bashir tun kama shi da aka yi a Afrilu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ba a sake ganin al-Bashir tun kama shi da aka yi a Afrilu
An wallafa

Babban mai shigar da kara a Sudan ya ce a makon gobe ne hambararren shugaban kasar, Omar al-Bashir zai gurfana gaban kotu.

Al-Waleed Sayyed Ahmed ya ce ana zargin al-Bashir da laifin rashawa da kuma mallakar biliyoyin daloli da fama-famai da aka samu a gidansa, sa'o'i kadan bayan sojoji sun hambarar da gwamnatinsa.

Ya kuma ce za a gurfanar da al-Bashir ne tare da wasu jami'an gwamnatinsa 41 da ake tuhuma da laifin cin hanci da rashawa.

Sannan ana tuhumar tsohon shugaban da sa hannu a kisan masu zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa.

A farkon wannan watan gwamnan masu zanga-zanga ne aka harbe a Khartoum babban birnin Sudan.

Har yanzu an kasa samun jituwa tsakanin majalisar soji da 'yan adawa kan kafa sabuwar gwamnati bayan hambarar da gwamnatin al-Bashir.

A ranar 11 ga Afrilu ne sojoji suka yi wa al-Bashir juyin mulki bayan shafe watanni ana zanga-zangar kin jin gwamnatinsa.

Sojoji sun amsa cewa sun yi kuskure kan tarwatsa masu zanga-zangar da ke son tabbatar da mulkin farar hula bayan sojojin sun kwace mulki.

Alkalumman gwamnati sun ce akalla mutum 61 aka kashe a rikicin 3 ga Yuni, yayin da kuma alkalumman likitoci da ke goyon bayan 'yan adawa suka ce kimanin mutum 118 ne aka kashe.

Bayanan bidiyo, Yadda Khartoum ya koma kamar an yi ruwa an dauke