Yadda kotu ta wanke Diezani daga laifukan rashawa

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An fara binciken Diezani ne a shekarar 2013, yayin da aka kama ta a London a shekarar 2015
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Wata kotu da ke birnin London ta wanke tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga dukkan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi mata bayan shafe shekaru ana gudanar da bincike da shari'a kan lamarin.

An wanke ta daga zargin karɓar cin hanci daga attajiran masu harkar mai ta hanyar zama a gidaje na alfarma da kuma bushasha da kuɗaɗe masu yawa a Birtaniya.

Hakan ya kawo ƙarshen ɗaya daga cikin manyan shari'un da Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Birtaniya (NCA) ta shafe sama da shekara goma tana bi, kuma aka wanke ta daga zarge-zarge biyar da ake mata.

Masu gabatar da ƙara sun zargi Diezani, mai shekaru 65, da karɓar cin hanci daga attajiran masu harkar mai, ciki har da kayayyaki da darajarsu ta kai fam miliyan biyu daga shahararren kantin Harrods, da rayuwa a gidaje masu tsada da kuma wasu alfarma a Birtaniya.

An fara binciken Diezani ne a shekarar 2013, yayin da aka kama ta a London a shekarar 2015.

A lokacin tana daga cikin manyan jami'an gwamnatin Najeriya da suka yi fice a harkar mai, inda ta riƙe muƙamin minista tsakanin 2010 da 2015. Haka kuma ita ce mace ta farko da ta jagoranci ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.

Dama dai tun a farkon shari'ar a watan Janairu, lauyoyinta sun yi ta jaddada cewa akwai muhimman takardun da za su iya tabbatar da ba ta da laifi da suka ɓace a Najeriya. Sun kuma yi suka kan tsawon lokacin da aka ɗauka kafin gurfanar da ita a gaban kotu.

Kotun ta kuma wanke ɗan'uwanta, Doye Agama, mai shekaru 69 kuma babban limamin wata cocin Pentecostal a Manchester, daga zargin haɗa baki wajen aikata rashawa, da kuma wani attajira a harkar mai, Olatimbo Ayinde mai shekaru 54.

Ministar da ake wa laƙabi da 'Madam D' saboda bin ƙa'ida

Diezani ta ce tsananin bin ƙa'idojin aiki ne ya sa aka yi mata laƙabi da "Madam Due Process"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Diezani ta ce tsananin bin ƙa'idojin aiki ne ya sa aka yi mata laƙabi da "Madam Due Process"

A yayin shari'ar da ta ɗauki hankalin jama'a a birnin London, , Diezani ta yi ta ƙoƙarin kare kanta daga zarge-zargen rashawa ta hanyar bayyana kanta a matsayin mace mai bin doka da oda da kuma mai yaƙi da cin hanci da rashawa, inda ta ce tsananin bin ƙa'idojin aiki ne ya sa aka yi mata laƙabi da "Madam Due Process".

Diezani, wadda aka fi sani da "Madam D", ta shafe kwanaki goma tana bayar da shaida a gaban kotu, yayin da masu kallo suka riƙa cika ɗakin sauraron shari'ar, ciki har da baƙi daga Najeriya.

Kafin shigarta siyasa, Diezani ta samu gagarumin ci gaba a harkar gudanar da kamfanonin mai, inda a shekarar 2006 ta zama mace ta farko da aka naɗa cikin kwamitin gudanarwa na kamfanin mai da gas na Shell a Najeriya.

Da take bayyana irin ƙalubalen da ta fuskanta, Diezani ta shaida wa kotu cewa kasancewarta mace a irin wannan babban matsayi a fannin da mafi yawa maza ne ya jawo mata tsana daga wasu mutane.

"Diezani ta ci duniyarta da tsinke"

Masu gabatar da ƙara sun ce a fiye da siyyaya 50 da ta yi a shagon Harrods na London, Aluko ne ya kashe kusan fam miliyan biyu wajen biyan kuɗin kayayyakin da Diezani ta saya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu gabatar da ƙara sun ce a fiye da siyyaya 50 da ta yi a shagon Harrods na London, Aluko ne ya kashe kusan fam miliyan biyu wajen biyan kuɗin kayayyakin da Diezani ta saya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu gabatar da ƙara sun zargi tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, da rayuwa cikin alfarma ta hanyar amfana da kuɗaɗen wasu attajiran masu harkar mai da ke da kwangiloli da gwamnatin Najeriya.

Babbar mai gabatar da ƙara, Alexandra Healy KC, ta shaida wa kotu cewa Diezani tana da "sha'awar saye-saye", kuma ta bari wasu manyan ƴan kasuwar mai su ɗauki nauyin rayuwarta mai cike da alfarma.

Duk da yake an ambaci sunayen mutum shida a cikin tuhumar, babu ɗayansu da aka gurfanar a gaban kotu.

Daga cikin waɗanda aka ambata akwai attajirin ɗan kasuwar mai, Kolawole Aluko. Masu gabatar da ƙara sun ce a fiye da siyyaya 50 da ta yi a shagon Harrods na London, Aluko ne ya kashe kusan fam miliyan biyu wajen biyan kuɗin kayayyakin da Diezani ta saya.

Haka ma a wata ziyara ta tsawon sa'o'i biyu da Diezani ta kai a kantin Knightsbridge a watan Nuwamban 2013, ta zaɓi kaya masu darajar kusan fam dubu 500, inda takardun biyan kuɗi suka nuna cewa Aluko ne ya biya kuɗin tare da amfani da katinsa na Harrods.

Haka kuma an ce Aluko ya kashe dubban fam wajen hayar motocin alfarma da direbobi, ciki har da Bentley Continental da Rolls Royce, domin zirga-zirga da Diezani da iyalanta a sassa daban-daban na Ingila.

An kuma shaida wa kotun cewa Aluko ya kafa kamfaninsa na Atlantic Energy ne watanni uku bayan Diezani ta zama ministar man fetur a watan Afrilun 2010.

A cikin shekaru kaɗan bayan haka, kamfanin, wanda ya mallaka tare da Olajide Omokore, ya samu kwangilolin haƙo ɗanyen mai da darajarsu ta kai miliyoyin daloli.

Masu gabatar da ƙara sun ce hakan ya saɓa ƙa'ida saboda matsayin da Diezani ke da shi a matsayin ministar man fetur.

Sai dai ba su gabatar da wata hujja da ke nuna cewa ta bai wa ɗaya daga cikin attajiran kwangila ne saboda cin hanci ba.

Alƙalan kotun sun nazarci ɗaruruwan bayanan hada-hadar kuɗi tare da sauraron shaidun direbobi, ma'aikatan gine-gine da masu sayar da kayayyaki. Haka kuma sun binciki saƙonnin waya da imel da aka samo daga wayoyi da kwamfutocin da aka ƙwace a Birtaniya da Najeriya.

Yadda Diezani ta kare kanta a kotu

An fara binciken Diezani ne a shekarar 2013, yayin da aka kama ta a London a shekarar 2015

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, wanda ya naɗa Diezani minista, ya ƙi zuwa kotu domin bayar da shaida

Da take kare kanta, Diezani ta ce: "Ban taɓa nema, karɓa ko neman wani nau'in cin hanci ba."

Ta shaida wa kotu cewa dokokin Najeriya ba su ba ministoci damar riƙe asusun ajiyar kuɗi a ƙasashen waje yayin da suke bakin aiki, sannan ofishin ma'aikatarta da ke London a wancan lokacin na cikin, shi ya sa ta dogara da wasu attajiran ƴan kasuwa wajen biyan wasu kuɗaɗen buƙatunta.

A cewarta, daga baya ana mayar musu da kuɗaɗen a Najeriya, kuma an ƙwace hujjojin da za su tabbatar da hakan daga gidanta da ke Abuja amma ba a gabatar da su a kotu ba.

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, wanda ya naɗa Diezani minista, ya ƙi zuwa kotu domin bayar da shaida.

Sai dai ya aike da rubutacciyar sanarwa inda ya ce a wasu lokuta wasu mutane kan ɗauki nauyin sufuri, masauki da sauran buƙatun ministoci yayin tafiyar aiki a ƙasashen waje.

Diezani ta kuma ce yawancin kayayyakin alfarma da aka saya ba nata ba ne. Ta bayyana cewa tana raka wasu attajiran masu harkar mai ne domin ba su shawarwari kan yadda za su kawata gidajensu.

Har ila yau, ta musanta ikirarin tsohon direbanta cewa ya kai mata tsabar kuɗi da suka kai fam dubu 100.

Akwai tambayoyin da ba a samu amsarsu ba

A yayin shari'ar, akwai wasu tambayoyi da dama da masu gabatar da ƙara suka kasa amsawa, waɗanda ake ganin sun yi tasiri wajen lalata shari'ar.

Lauyan kare Diezani, Jonathan Laidlaw KC, ya tambayi dalilin da ya sa ake gudanar da shari'ar a London alhali lamarin ya shafi Najeriya ne da gwamnatin Najeriya.

"Akwai ban mamaki yadda ake sauraron wannan shari'a a Landan alhali lamari ne da ya shafi Najeriya da gwamnatin Najeriya," in ji shi.

Masu gabatar da ƙara sun ce akwai buƙatar a yi shari'ar a Birtaniya saboda kada wani batun cin hancin ya ƙara yin tasiri a wani wurin. Sai dai Laidlaw ya tambayi dalilin da ya sa gwamnatin Najeriya ba ta gurfanar da Diezani Alison-Madueke gaban kotu ba.

Lauyan ya kuma ce Diezani ta shafe kusan shekara 11 a Birtaniya cikin wani hali da ya kwatanta da zaman ƙuntatawa, inda ba ta iya aiki ko yin tafiye-tafiye, yayin da NCA ta gaza kawo attajiran ƴan kasuwar man fetur shida da ake zargin sun ba ta cin hanci.

Alƙalan kotun ba su samu bayani kan dalilin da ya sa ba a gurfanar da waɗannan mutane ba.

Sai dai sun ji cewa ɗaya daga cikinsu, Kolawole Aluko, ya tsere daga Birtaniya bayan kama Diezani a shekarar 2015, kuma ba a san inda yake ba a yanzu.

Haka kuma ba a sanar da alƙalan kotun cewa a shekarar 2023, Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta ƙwato dala miliyan 53 daga kadarorin da aka ƙwace daga Kolawole Aluko da Olajide Omokore ba.

A wata sanarwa da ta fitar a lokacin, Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta yi zargin cewa Diezani ta yi amfani da tasirinta wajen taimaka wa kamfanonin Aluko da Omokore samun kwangilolin mai masu tsoka.

Sanarwar ta ce kuɗaɗen da aka samu daga waɗannan kwangilolin, waɗanda darajarsu ta haura dala miliyan 100, an yi wadaƙa da su ne a Amurka.