Hambararren shugaban Sudan Omar al-Bashir zai gurfana a kotu

An wallafa

Babban mai shigar da kara a Sudan ya ce a makon gobe ne hambararren shugaban kasar, Omar al-Bashir zai gurfana gaban kotu.

Al-Waleed Sayyed Ahmed ya ce ana zargin al-Bashir da laifin rashawa da kuma mallakar biliyoyin daloli da fama-famai da aka samu a gidansa, sa'o'i kadan bayan sojoji sun hambarar da gwamnatinsa.

Ya kuma ce za a gurfanar da al-Bashir ne tare da wasu jami'an gwamnatinsa 41 da ake tuhuma da laifin cin hanci da rashawa.

Sannan ana tuhumar tsohon shugaban da sa hannu a kisan masu zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa.

A farkon wannan watan gwamnan masu zanga-zanga ne aka harbe a Khartoum babban birnin Sudan.

Har yanzu an kasa samun jituwa tsakanin majalisar soji da 'yan adawa kan kafa sabuwar gwamnati bayan hambarar da gwamnatin al-Bashir.

A ranar 11 ga Afrilu ne sojoji suka yi wa al-Bashir juyin mulki bayan shafe watanni ana zanga-zangar kin jin gwamnatinsa.

Sojoji sun amsa cewa sun yi kuskure kan tarwatsa masu zanga-zangar da ke son tabbatar da mulkin farar hula bayan sojojin sun kwace mulki.

Alkalumman gwamnati sun ce akalla mutum 61 aka kashe a rikicin 3 ga Yuni, yayin da kuma alkalumman likitoci da ke goyon bayan 'yan adawa suka ce kimanin mutum 118 ne aka kashe.