Shugaban Algeria Abdulaziz Bouteflika ya yi murabus

Algerian President Abdelaziz Bouteflika

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, President Abdelaziz ya shugabanci Algeria tun 1999
An wallafa

Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika ya mika takardar sauka daga mulki bayan an shafe makwanni ana zanga-zangar kin jin jinin gwamnatinsa, a cewar kafofin watsa labaran kasar.

Tuni dai dama dattijon shugaban da ya shafe shekara 20 yana mulki ya jingine burinsa na neman wa'adi na biyar, yayin da jama'a suka nuna sun gaji da mulkinsa.

Rundunar sojan kasar mai karfin fada a ji ta yi kira a ayyana shugaban mai shekara 82 a matsayin wanda ba zai iya mulki ba.

Shugaban wanda ke fama da jinya ya shafe shekara shida yana fama da shanyewar barin jiki, kuma tun lokacin bai fiya fitowa cikin jama'a ba.

Gidan talabijin din kasar ya rawaito cewa Bouteflika ya shaidawa majalisar tsarin mulkin kasar a hukumance cewa daga ranar Talata ya sauka daga mulkin kasar.

Tun da farko kamfanin dillacin labarai na APS ya ambato babban hafsan sojojin kasar yana cewa "babu sauran damar bata lokaci."

Jagororin zanga-zangar sun yi watsi da tayin da Bouteflika ya yi cewa zai sauka a ranar da wa'adin mulkinsa zai kare, wato 28 ga watan Aprilu.

Masu zanga-zangar sun kuma yi kira a yi garambawul ga gaba daya tsarin gwamnatin kasar, wacce sojoji suke da karfin fada a ji.

Mafi yawan masu zanga-zangar dai matasa ne, wadanda suka ce suna son sabuwar gwamnati.

Bayanan bidiyo, 'Yan sanda sun yi amfani da motar ruwa don tarwatsa masu zanga-zangar.

Akwai dai zarge-zargen cewa wasu gaggan masu fada a ji ne ta hadakar 'yan kasuwa da 'yan siyasa da jami'an sojoji da ake kira "le pouvoir" suka hana Bouteflika sauka domin su ci gaba da juya gwamnati.

Jam'iyyar FLN mai mulkin kasar wacce ta dage zaben da aka shirya gudanarwa ranar 18 ga watan Aprilu ta yi alkawarin shirya babban taron kasa kan sauye-sauye.

FNL ce take mulkin Algeria tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga Faransa a 1962, bayan shekara bakwai ana yaki.

Bouteflika, wanda ya fara mulki a 1999 ya karfafa mulkinsa ne bayan mummunan yakin basasar kasar, da gwamnati ta gwabza da masu da'awar kishin Islama, wanda ya janyo mutuwar mutum 150,000.

Rahotanni sun ce ana jin karar odar motoci a titunan babban birnin kasar Algiers, bayan sanarwar cewa Bouteflika ya mika takardar sauka daga mulki.

Shugaban majalisar dattijan kasar Abdelkader Bensalah ne ake sa ran zai zama shugaban rikon kwarya tsawon na wata uku.