Sojojin Algeria za su kare martabarta - Janar Ahad Salah

President Bouteflika's last known public address to Algerians was in 2014

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Rabon da Shugaba Bouteflika ya yi jawabi a bainar jama'a tun 2014
An wallafa

Babban hafsan hafsoshin Algeria ya ce sojojin kasar ba za su bari rikicin siyasar kasar ya kazancewar da yayi a shekarun alif dari tara da casa'in ba.

A wancan lokacin rikicin siyasar kasar ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da 'yan kasar dubu dari biyu.

Janar Ahmad Gaid Salah na wadannana kalaman ne bayan da sabuwar zanga-zanga ta barke a manyan biranen kasar inda masu adawa da tsawaita wa'adin mulki da Shugaba Abdelaziz Bouteflika ke son yi.

Janar Salah ya sanar da sababbin kuratan sojojin kasar ta Algeria cewa wasu jam'iyyu na son ganin kasar ta fada tsundum cikin rikici irin wanda ya taba faruwa a shekarun baya.

Amma ya ce sojojin kasar za su tabbatar da tsaro da bin doka da oda.

Wadannan jerin zanga-zangar sun fara ne kwanaki 11 da suka gabata kuma babu alamar za a daina zanga-zangar nan kusa.

A young man, wearing the national flag, holds a banner as Algerian students demonstrate in the capital Algiers on March 5, 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matasa su zargi tsofaffin kasar da mamaye komai a kasar

Dubban dalbai da malamansu sun fito bisa titunan birnin Algiers suna neman Shugaba Abdelaziz Bouteflika wanda ke jinya a wani asibitin kasar Switzerland ya fasa tsayawa takara a karo na biyar.

Masu zanga-zangar na cewa sun gaji da mulkinsa kuma suna neman ganin an kawo karshen rashin aikin yi da cin hanci da rashawa a kasar.