Man United da Aston Villa na zawarcin David, Al-Ettifaq za ta yi wa Henderson ƙafar-ungulu

Jonathan David

Asalin hoton, GETTY IMAGES

An wallafa

Manchester United da Aston Villa na sha'awar sayen matashin ɗan gaban Lille Jonathan David ɗan Kanada mai shekara 23. (Football Transfers)

Al-Ettifaq ta Saudiyya ba ta son rabuwa da Jordan Henderson, na Ingila a watan nan na Janairu, kuma daman har yanzu ba ta samu wani tayi ba a kansa. (Ben Jacobs)

Matashin ɗan wasan tsakiya na Liverpool Fabio Carvalho, na Portugal, mai shekara 21 zai tafi ƙungiyar Hull City ta ƙasa da Premier, aro na sauran watannin da suka rage a kakar bana. (Athletic )

Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Manchester City da Newcastle a kan cinikin ɗan wasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips. (Rudy Galetti)

West Ham za ta yi zawarcin tsohon ɗan wasan gaba na Tottenham Steven Bergwijn, wanda yanzu yake taka leda a Ajax. (Evening Standard)

Wolves na sha'awar matashin ɗan gaban Paris St-Germain Hugo Ekitike, na Faransa mai shekara 21. (L'Equipe )

PSV Eindhoven ta gabatar wa da Manchester United buƙatarta ta sayen ɗan gabanta na Uruguay Facundo Pellistri, mai shekara 22. (Fabrizio Romano)

Brighton za ta nemi sayen matashin ɗan bayan Boca Juniors Valentin Barco, ɗan Argentina, mai shekara 19, wanda farashin raba shi da ƙungiyar shi ne yuro miliyan 10. (Fabrizio Romano)

Bayern Munich ta bi sahun Tottenham a fafutukar zawarcin ɗan bayan Romania Radu Dragusin, mai shekara 21, daga Genoa. (GSP)

Ɗan bayan Ingila Djed Spence, na atisaye da tawagar Tottenham ta ƴan ƙasa da shekara 21, kuma bisa ga dukkan alamu zai koma zaman aro bayan ya baro Leeds a farkon kasuwar saye da sayar da ƴan wasa ta kakar nan. (Football London)

AC Milan na sha'awar ɗan gaban Hellas Verona Cyril Ngonge, ɗan Belgium mai shekara 23 wanda kuma ake danganta shi da Aston Villa. (Tutto Mercato)