Tsohon ɗan ƙwallon Jamus Franz Beckenbauer ya rasu

Asalin hoton, Getty Images
Gwarzon ɗan ƙwallon tawagar Jamus, Franz Beckenbauer ya rasu, yana da shekara 78 a duniya.
Ya ɗauki kofin duniya a matakin kyaftin ɗin Jamus a 1974, da kuma a matsayin koci a 1990.
Tsohon mai tsaron baya ya buga wa Bayern Munich wasa 582, kuma ya lashe babban kofin gasar Jamus a matakin ɗan wasa da kuma a matsayin koci.
Ɗan ƙwallon wanda ake yi wa laƙabin Der Kaiser, ya lashe European Championship a matakin ɗan wasa a 1972, kuma ya lashe Ballon d'Or karo biyu.
Beckenbauer, wanda ya fara taka leda a matakin ɗan wasan tsakiya ya fuskanci Sir Bobby Charlton a gasar kofin duniya a 1966, inda Ingila ta lashe kofin da ci 4-2 daga nan ya koma buga gurbin ɗan baya.
Ya kuma ci ƙwallo hudu a gasar kofin duniya a 1966, lokacin yana da shekara 20, shi ne kuma ya lashe kyautar matashin ɗan ƙwallo a gasar.
Ya buga wa tawagar West Germany wasa 103.
A matakinsa na ɗan wasa a Bayern Munich ya lashe kofin babbar gasar Jamus huɗu da European Cup a 1974 da 1975 da kuma 1976.
Ya kuma ɗauki Bundesliga a ƙungiyar Hamburg.











