An kammala auna koshin lafiyar Gabriel Jesus a Arsenal

Gabriel Jesus

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An kammala auna koshin lafiyar Gabriel Jesus a shirin da yake na komawa Arsenal kan fam miliyan 45 daga Manchester City.

Kungiyoyi da yawa daga Premier League da wasu daga nahiyar Turai na fatan daukar dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 25, amma ya zabi komawa Gunners.

Jesus ya yi wasa 236 ya ci kwallo 95 a City tun bayan da ya koma Etihad da taka leda daga Palmeiras a Janairun 2017.

Ya lashe kofin Premier League hudu a zamansa a Etihad da karin kofi uku da ya ci a League Cups da kuma the FA Cup.

Dan kwallon ba zai samu damar buga wasanni da yawa a City ba, bayan da kungiyar ta dauki dan kwallon tawagar Norway, Erling Haaland daga Borussia Dortmund.

Jesus ya yi aiki tare da kociyan Arsenal, Mikel Arteta a lokacin da ya yi mataimakin Pep Guradiola a City.

Kociyan na fatan daukar dan wasa mai cin kwallaye, bayan da ya rabu da Alexandre Lacazette da kuma Pierre-Emerick Aubameyang.

Tuni dai Arsenal ta dauki Fabio Vieira daga Porto kan fam miliyan 34.2, ana kuma cewar tana fatan sayen dan wasan Leeds United, Raphinha.

Arsenal ta kammala a mataki na biyar a teburin Premier League da aka karkare a bana, bayan da Tottenham abokiyar hamayya ta samu gurbin Champions League.

Jesus ya yi wasa 28 a Premier League da ta karkare da cin kwallo takwas da bayar da tara aka zura a raga.

Ya buga wa tawagar Brazil wasa 56 da cin kwallo 19, tun bayan da ya fara yi mata tamaula a Satumbar 2016.