Ajax ta tsuga farashin Anthony, yaya batun zuwan Jong United?
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
- Kauce wa X, 1Ya kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Kauce wa X, 2Ya kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Gunners na son daukar Martinez kan fam miliyan 35
Bayan da Arsenal ta kammala auna koshin lafiyar Gebriel Jesus a shirin da yake na komawa kungiyar da taka leda.
Daily Mirror ta wallafa cewar Gunners tana shirin daukar mai tsaron bayan Ajax, Lisandro Martinez kan fam miliyan 35.
To sai dai kuma Manchester United na fatan daukar dan wasan mai shekara 24 dan kwwallon Argentina.

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da aka kamma kakar bana, dan wasan West Ham United, Declan Rice mai shekara 23 yana daga cikin wadanda ake ta rade-radi kan makomarsa - sai dai yanzu shiru kakae ji ba a yin batun da ya shafi dan wasan.

Asalin hoton, re
Wai ian Divock Origi ne ?
Divock Origi fitatcen dan wasa ne da ya taka rawar gani a Liverpool, sai dai kuma a watan jiya yarjejeniyarsa ta kare a Anfield.
A karshen watan Yuni yarjejeniyasa ya karkare a Liverpool, ko ina dan wasan mai shekara 22 ya shiga kawo yanzu?
Wasu jaridu na rade-radin cewar dan wasan na Italiya a shirin da yake na komawa AC Milan da taka leda, an kuma kusan kammala cinikin dan wasan domin ya koma buga Serie A.

Asalin hoton, Getty Images
Ko Erling Haaland zai ci kwallaye da yawa a Man City?
Manchester United ta dauki Erling Harling daga Borussia Dortmund da zai fara buga mata wasanni a kakar da za a fara.
City ta lashe Premier League a kakar da aka kammala ba tare da fitatcen mai cin kwallaye ba, tun bayan da Sergio Aguero ya koma Barcelona daga baya ya yi ritaya.
Shin kwallo nawa kuke ganin Haaland zai ci a kakar farko a City?
Shin zai iya lashe takalmin zinare a kakar farko a Premier League kuwa?

Asalin hoton, Getty Images
Labaran da jaridu ke wallafawa da suka shafi cinikin 'yan kwallo, Daga Jaridu
Tottenham da abokiyar hamyyarta Chelsea da dukansu ke zaune a birnin London na gagayya da juna domin daukar dan wasan gaban Everton Richarlison, mai shekaru 25.(Sky Sports)
Sai dai Everton ta sanar cewa ba ta shirya sayar da dan wasan tsakiyarta Gordon ba ga kowace kungiya.(Liverpool Echo)
Spurs na kuma kan gaba wurin kokarin sayen dan wasan bayan Barcelona Clement Lenglet, duk da Roma ma na son kulla ciniki kanshi.(London Evening Standard)
Ita kuwa Real Madrid ta ce babu dan wasan da take son kawowa kaka mai zuwa kamar matashin dan wasan Ingila Jude Bellingham da ke wasa a Borrussia Dortmund.(AS, via Mail)
Chelsea na son yi wa 'yan wasan Manchester City Raheem Sterling da Nathan Ake cinikin goro don kara wa gaba da bayansu karfi.(Telegraph - subscription required)
Chelsea ta tuntubi Man City ko za a sayar mata da Sterling
Chelsea ta tuntubi Manchester City ko za a sayar mata da Raheem Sterling. Sterling, wanda ya koma Etihad daga Liverpool a 2015 ya ci kwallo 131 a wasa 339, yana daga cikin fitatun yan wasan da Chelssea ke son dauka kan fara kakar bana.
Saura kaka daya yarjejeniyar Sterling ta kare a Etihad, ana kuma tunanin da kyar ne idan zai ci gaba da zama a City.
Tun bayan da Pep Guardiola ya zama kociyan City a 2016, ba dan wasan da ya ci kwallaye da yawa kamar Sterling mai 120, bayan Sergio Aguero mai 124 a Premier League.

Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa za ta yawan wurin zaman 'yan kallo a Villa Park
Aston Villa ta fitar da tsarin yadda za ta kara wurin zaman 'yan kallo a Villa Park, domin ya haura mutum 50,000.
Kungiyar na fatan kara wasu gine-ginen a daf da filin wasan da ke Birmingham, wanda aka bude tun 1897 wanda ke cin 'yan kallo 42,682.
Villa na fatan fara aikin fadada wurin zaman 'yan kallo a shekara mai zuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Wolfsburg ta dauki dan kwallon tawagar Croatia, kyaftin din 'yan kasa da shekara 21, Bartol Franjic kan yarjejeniyar kaka biyar daga Dinamo Zagreb, kamar yadda kungiyar da ke buga Bundesliga ta sanar ranar Litinin.
Franjic, mai shekara 22, shi ne na hudu da Wolfsburg tasaya a bana karkashin koci, Niko Kovac.
Wolfsburg za ta fara karbar bakuncin Werder Bremen ranar 6 ga watan Agusta a gasar Bundesliga ta bana da za a fara.
Ajax ta yi wa Anthony farashin fam miliyan 70
Times ta wallafa cewar Manchester United za ta kara matsa kaimi kan daukar dan kwallon Brazil mai taka leda a Ajax, Anthony.
Sai dai kuma kamar cinikin zai yi wa United tsada kamar yadda Daily Mirror ta wallafa cewar Ajax ta yi wa matashin dan wasan mai shekara 22 farashin fam miliyan 70.

Asalin hoton, Getty Images
Labaran da jaridu ke wallafawa da suka shafi cinikin 'yan kwallo, Daga jaridu
Ana sa ran dan wasan gaban Liverpool Mohamed Salah ya bar kungiyar idan kwantiraginsa ta kare a karshen kakar da ke tafe.(Mirror)
Arsenal kuwa ta mika tayin fam miliyan 35 ga Ajax, don sayen dan wasan bayanta Lisandro Martinez, duk da Manchester United ma ta nuna sha'awar daukarsa.(Mirror)
Anan kuma United din na fatan kammala cinikin daukar dan wasan tsakiyar Barcelona Frenkie de Jong, da kuma na Denmark Christian Eriksen, kafin su kuma mai da hankali wurin dauko dan wasan gaban Ajax, Antony.(Times - subscription required)

Asalin hoton, Getty Images
West Ham United ta kammala daukar Alphonse Areola
West Ham ta kammala dauakr Alphonse Areola daga Paris St-Germain.
Areola, 29, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar, bayan wasannin aro da ya buga a West Ham.
Shi ne na biyu da West Ham ta dauka a baya, bayan dan kwallon tawagar Morocco, Nayef Aguerd daga Rennes.
West Ham, wadda ta dauki Aguerd kan fam miliyan 30, ba ta fayyace kan nawa ta sayi Areola ba, amma ana cewar zai kai farashin fam miliyan 10.

Asalin hoton, Getty Images
Kalubalen da ke gaban Erik ten Hag
Ten Hag ya fara aikin horar da Manchester United don tunkarar wasannin bana na 2022/23.
Kociyan zai fuskanci kalubale da dama a kungiyar ta Old Trafford.
- Shin zai iya mayar da kungiyar kan ganiya?
- Ko zai iya kawo fitattun 'yan wasa United
- Ko United za ta dauki Premier League
- Ko United za ta koma buga Champions League yadda ya kamata
- Wane salon wasan zai dora United ---- da sauransu

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta kammala auna koshin lafiyar Gebriel Jesus
An kammala auna koshin lafiyar Gabriel Jesus a shirin da yake na komawa Arsenal kan fam miliyan 45 daga Manchester City.
Kungiyoyi da yawa daga Premier League da wasu daga nahiyar Turai na fatan daukar dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 25, amma ya zabi komawa Gunners.
Jesus ya yi wasa 236 ya ci kwallo 95 a City tun bayan da ya koma Etihad da taka leda daga Palmeiras a Janairun 2017.

Asalin hoton, Getty Images
Muhawara da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook
Ra’ayoyi kan Kasuwar Saye da sayar da yan Kwallo
Yaquba Mai Manja Funtua: Ya ce to Kungiyar Chelsea da ta Tottenham Allah Ya baiwa Mai Rabo Sa'a Wajen Daukar Richarlison.
Mua’zu Kabiru Ci-Guminka: Ya ce Tabbas ƴan wasan Man City guda biyu da Chelsea ke nema, Raheem Sterling da Nathan Ake zasu yi matuƙar ƙarfafa tawagar ƙungiyar idan sun haɗe da ita.
Kan komawar Fernandinho tsohuwar kungiyarsa, Athletico Paranaense kuwa, Babawo Mato Mai’adua cewa yayi : Ya kyauta ma kansa.
Nura Garba Karaye kuwa, Fatan Alheri ya yi masa a can tsohuwar kungiyarsa da ya koma.
Ko Manchester United ta kusan daukar Frenkie de Jong ?
Har yanzu Manchester United na fatan daukar dan kwallon Barcelona', Frenkie de Jong, wanda ya taka leda karkashin koci, Erik ten Hag a Ajax.
Shin ko United ta kusan kammala cinikin dan wasan?
Kamar yadda Times ta wallafa United na fatan karkare cinikin De Jong da dan wasan tawagar Denmark, Christian Eriksen.
Daga nan ne za ta mayar da hankali wajen daukar Anthony daga Ajax.

Asalin hoton, Getty Images
Erik ten Hag ya fara aikin horar da Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta fara atisayen tunkarar kakar bana ta 2022/23
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
- Kauce wa X, 1Ya kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Kauce wa X, 2Ya kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Kauce wa X, 3Ya kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
