Liverpool da Man Utd na zawarcin Simons, Salah 'ya dace da taka leda a Saudiyya'

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaba na Netherlands Xavi Simons na iya barin RB Leipzig a wannan bazarar kuma kulob ɗin na Jamus zai so kusan fam miliyan 70 idan zai cefanar da ɗanwasan mai shekara 21. (Sky Sports Germany)
Liverpool da Manchester United na daga cikin ƙungiyoyin da ke bibiyar Simons wanda kwantariginsa da RB Leipzig ya kai har shekarar 2027. (Sport Bild - in German)
Liverpool na tsara tattaunawa domin tantance makomar ɗanwasan gaba na Colombia mai shekara 28 Luiz Diaz da ɗanwasan Portugal Diogo Jota mai shekara 28 da kuma ɗanwasan Faransa Ibrahima Konate mai shekara 25 yayin da ake tunkarar kasuwar musayar ƴanwasa a bazara. (Football Insider)
Ministan wasanni na Saudiyya Yarima Abdulaziz bin Turki Al-Faisal ya ce ɗanwasan gaba na Masar Mohamed Salah ya cancanci ya taka leda a babbar gasar Saudiyya amma babu wata tattaunawa da ake game da ɗauko shi kafin ɗanwasan mai shekara 32 ya tsawaita kwantiraginsa da Liverpool. (ESPN)
Real Madrid na zawarcin ɗanwasan tsakiya na Sifaniya Rodri amma ba lalle ba ne ya sauya ƙungiya saboda ɗanwasan mai shekara 28 na nan a Manchester City kuma bai shirya barin ƙungiyar ba. (Sport Bild - in German)
Akwai damar sayar da ɗanwasan Fiorentina Moise Kean a kan fam miliyan 45 daga 1 zuwa 15 ga Yuli duk da cewa ƙungiyoyi da dama na zawarcinsa, matashin ɗanwasan mai shekara 25 na iya zama a Viola domin taimaka masa wajen samun damar shiga jerin ƴanwasan Italiya a gasar cin kofin duniya ta 2026. (Tuttomercatoweb - in Italian)
Everton za ta sakar wa Micheal Keane mai shekara 32 marar barin kulob ɗin idan kwantiraginsa ya ƙare a ƙarshen watan Yuni. (Football Insider)
Daraktan wasanni na Barcelona Deco ya bayar da shawarar mai tsaron ragar Poland Wojciech Szczesny, mai shekara 35 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara guda domin ci gaba da zama a kulob ɗin. (Marca - in Spanish)













