Raunin da Saka ya ji ba wani mai muni bane in ji Arteta

Asalin hoton, Getty Images
Raunin da Bukayo Saka ya ji a wasan Premier League ranar Lahadi a gidan Ipswich Town ba wani mai muni bane, in ji Mikel Arteta.
Arsenal ta yi nasarar cin 4-0, kuma waɗan da suka ci mata ƙwallayen sun haɗa da Leandro Trossard, wanda ya zura biyu a raga, sai Gabriel Martinelli da kuma Ethan Nwaneri.
Ɗan wasan tawagar Ingila ya ji rauni a minti na 32, sakamakon ketar da Leif Davis ya yi masa, wanda aka bai wa jan kati a fafatawar.
An canja Saka tun farkon shiga zagaye na biyu, wanda aka nuna shi an ɗaure masa kafa.
Arteta ya ce ya cire Saka ne, domin yin taka tsanta, bayan da Arsenal za ta kara da Paris St Germain a Champions League zagayen daf da karshe ranar 29 ga watan Afirilu.
Arsenal ta yi fama da ƴan wasa da yawa da suka yi jinya, ciki har da Saka da Martin Odegaard da Kai Havertz da kuma Gabriel Jesus..
Arsenal ta kawo wannan matakin ne, bayan fitar da Real Madrid mai rike da kofin da cin 5-1 gida da waje.
Ita kuwa PSG, wadda ta ci Manchester City a cikin rukuni a bana da fitar da Liverpool a zagaye na biyu, ita ta yi waje da Aston Villa a Champions League.
Arsenal da Paris St Germain ba wadda ta taɓa lashe kofin zakarun Turai a tarihi, kenan wannan dama ce da ɗaya daga ciki za ta iya yin bajinta a gasar.
Ranar Laraba Arsenal za ta kara da Crystal Palace a Premier ranar 23 ga watan Afirilu daga nan ta karɓi bakuncin PSG a wasan farko daf da karshe a Champions League ranar Talata 29 ga watan Afirilu.










