Zaɓuka kusan 100 INEC za ta ƙarasa a watan gobe

INEC Chair

Asalin hoton, INEC Facebook

An wallafa

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta sanya Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranar ƙarasa zaɓukan da ba su kammala ba a jihohi da dama na ƙasar.

Ta ce za ta ƙarasa zaɓukan da ba su kammala ba, na gwamna a jihohin Kebbi da Adamawa, sai na 'yan majalisar dattijai guda 5, da na 'yan majalisar wakilai 31, da kuma na 'yan majalisun jihohi guda 58.

Za a gudanar da zaɓukan 'yan majalisun dokokin ne in ji INEC a wasu cibiyoyin zaɓe ƙalilan na mazaɓun ɗan majalisa.

A ranar Litinin ne 27 ga watan Maris, hukumar zaɓe ta INEC ta yi wata ganawa don bitar wuraren da ake buƙatar ƙarasa zaɓukansu, saboda rashin kammalawa a lokacin zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun tarayya.

Wata sanarwa da INEC ta fitar ta ce tuni aka kammala zaɓukan gwamnoni a cikin jiha 26 da zaɓen sanatoci guda 104, sai 'yan majalisar wakilai 329, da kuma zaɓukan 'yan majalisun jihohi guda 935, kuma dukkansu an sanar da mutanen da suka yi nasara.

A cewarta, INEC za ta wallafa jerin sunayen tasoshin zaɓe da jihohi da ƙananan hukumomi da yankin ba da rijista da masu zaɓen da suka yi rijista da yawan katin zaɓen da aka karɓa a shafinta na intanet kafin ko kuma a ranar Laraba 29 ga watan Maris.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Ɗaya daga cikin jihohi da aka samu zaɓukan 'yan majasun tarayya masu yawa da ba su kammala ba ranar 25 ga watan Fabrairu, ita ce Sokoto, inda ake da 'yan majalisar wakilai 11 da sanatoci 3 waɗanda duk sai an ƙarasa zaɓukansu.

Masu sa-ido sun soki hukumar INEC saboda matsalolin da aka samu a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun tarayya na ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, wanda Bola Ahmed Tinubu, ya yi nasarar zama sabon shugaban Najeriya.

Haka ma a ranar 18 ga watan Maris lokacin da INEC ta gudanar da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi, an gamu da wasu daga cikin matsalolin da aka samu a zaɓen INEC na farko.

A ranar Litinin 20 ga watan Maris ne, babban jami'in sanar da sakamakon zaɓe ya bayyana Ahmad Umar Fintiri na Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya samu ƙuri'a 421,524.

Yayin da babbar abokiyar hamayyarsa ta APC, Sanata Aisha Dahiru Binani ta samu kuri'a 390,275.

Sai dai jami'in sanar da sakamakon zaɓen jihar, ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Fufore inda ya ce an samu bambanci tsakanin alƙaluman da aka sanar da kuma waɗanda aka ɗora a shafin INEC.

Zaben jihar Adamawa, na ɗaya daga cikin waɗanda suka fi jan hankali saboda shi ne karon farko da aka samu mace daga arewacin Najeriya wadda takara ta fi zafi tsakaninta da gwamna mai ci.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A Kebbi, zaɓen gwamnan jihar can ma, bai kammala ba, saboda kura-kurai da aka samu a ƙananan hukumomi 18 cikin 21 na jihar.

Ita ce jiha ta farko da aka fara ayyana zaɓen ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.

A ranar Litinin, babban jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamna a Kebbi, Farfesa Yusuf Sa'idu ne ya bayyana cewa jam'iyyar APC na da ƙuri'a 388,258 yayin da PDP kuma take da ƙuri'a 342,980.

Hukumar zaɓen ta yi kira ga dukkanin jam'iyyun siyasa da 'yan takara da da masu ruwa da tsaki su lura da rana da wuraren da za a gudanar da ƙarashen zaɓen. Haka kuma jami'an zaɓe da masu sanar da sakamakon zaɓe da masu sa-ido da kafofin yaɗa labaran da INEC ta riga ta tantance ne duk za su shiga a yi zaɓukan da su.

Hukumar zaɓen ta kuma yi kira ga jam'iyyun siyasa da 'yan takara da magoya bayansu su kalli zaɓe a matsayin takara kawai amma ba yaƙi ba, kuma su guji furta duk wasu kalamai na tunzura rikici da gangamin tada fitina ta yadda za a iya kammala zaɓukan kamar yadda aka tsara.