Tinubu ya tafi hutu zai kuma wuce Saudiyya Umrah - Kakakinsa

Wannnan shafi ne dai kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Bankwana

    To jama'a a nan ni Muhammad Annur Muhammad da na karɓi ragamar jagorantar wannan shafi da ke kawo muku labarai kai tsaye, waɗanda suka shafi Najeriya da sauran sassan duniya, nake cewa mu kwana lafiya Allah Ya ba mu alheri.

    Ga masu azumi kuwa sai na ce a yi sahur lafiya, Allah Ya sa an shiga watan a sa'a.

    Mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa ''Daɗin fitsari ke kawo tusa''

  2. An yanke wa ƴan tawayen Chadi ɗaurin rai da rai saboda kisan Shugaba Déby

    Sojoji ɗauke da akawatin gawar Idriss Deby Itno

    Asalin hoton, Idriss Deby Itno

    Bayanan hoto, An kashe Idriss Déby ne a fagen daga lokacin da ya ziyarci dakarunsa

    Wata kotu a Chadi ta yanke wa mayaƙa ƴan tawaye sama da 400 hukuncin ɗaurin rai darai saboda kisan tsohon shugaban ƙasar Idriss Idriss Déby.

    A shekarar 2021 ne tsohon shugaban ya rasu sakamakon raunukan da ya ji a fagen daga a wani artabu da ƴan tawayen a arewacin ƙasar.

    Ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi daɗewa a kan mulki inda ya shafe sama da shekara talatin a mulkin bayan ya ƙwaci mulkin daga kasancewarsa ɗan tawaye.

    A watan Fabarairu ni aka fara shari'ar ƴan tawayen sama da 465 daga ƙungiyar Front for Change and Concord in Chad (Fact), a babban birnin ƙasar N'Djamena, a asirce.

    Ƙungiyar ta soki shari'ar wadda ta bayyana da lulluɓe da cewa tana cike da saɓa ƙa'idoji.

    Wani lauyan ƴan tawayen ya nuna alamun cewa za su ɗaukaka ƙara.

  3. An dakatar da lafiri saboda amfani da waya a matsayin VAR ya hana ci

    Vitor Pereira lokacin yana alkalin wasa

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Vitor Pereira shi ne ya gaji Mark Clattenburg a hukumar alkalan wasan Masar

    An dakatar da wani alƙalin wasa a Masar saboda ya yi amfani da wayar salula ta ɗan kallo ya haramta wani ci da aka yi a wasan gasa.

    Ƙungiyar Al-Nasr ce ta farke cin da Suez ta yi mata ana kusa da tashi daga wasan na gasar rukuni na biyu na ƙasar a ranar Juma'a da ta gabata, sai dai kasancewar ba a amfani da na'urar VAR mai taimaka wa alkalin wasa a gasar rukuni na biyu a Masar, sai alkalin ya karɓi wayar wani ɗan kallo ya duba hoton bidiyon ya kuma hana cin bayan da ƙungiyar ta gida ta yi ƙorafi cewa an taɓa bal ɗin da hannu.

    A sanarwar da ta fitar hukumar ƙwallon ƙafa ta Masar ta ce Vitor Pereira (tsohon alkalin wasan Portugal) wanda ya maye gurbin mark Clattenburg a matsayin shugaban alkalan wasa na ƙasar a farkon watan nan ya yanke shawarar dakatar da dukkanin jami'an alkalancin wasan har zuwa wani lokaci.

    Daga baya Suez ta ci bal ɗinta ta uku bayn an hana wannan da aka farke inda suka tashi wasan da nasara 3-1 a kan bakin nasu.

    Ƴan sanda ne suka raka alƙalin wasa Farouk sakamakon barazanar da 'yan wasa da shugabannin ƙungiyar Al-Nasr suka yi masa, inda suka ce za su ɗauki matakin shari'a a kansa saboda saɓa ƙa'ida.

  4. Tinubu ya tafi hutu London da Paris, zai kuma wuce Saudiyya Umrah — Kakakinsa

    Tinubu

    Asalin hoton, BOLA TINUBU/FACEBOOK

    Sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tafi Turai domin ya hutu, daga can kuma zai nufi Saudiyya domin aikin Umrah.

    Kakakin Tinubun Tunde Rahman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

    A sanarwar kakakin ya ce, Tinubun ya fita ne domin ya je ya huta daga gajiyar kakar yakin neman zabe da kuma zaben sannan kuma ya tsara shirinsa na karbar mulki kafin ranar kaddamarwarsa ta 29 ga watan Mayu na shekarar nan ta 2023.

    Tunde ya ce zaɓaɓɓen shugaban ya tashi daga filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Ikeja, a Lagos zuwa Turai a jiya Talata da daddare, inda zai je Paris da kuma London domin ya huta, sannan kuma ya wuce Saudiyya domin Umrah da azumin Ramadan da za a fara a gobe Alhamis.

  5. Ranar Ruwa ta Duniya: Matashin da ya taimaka wa ƙauyensa da ruwan sha mai tsafta

  6. Tsohon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya musanta zargin yi wa majalisa ƙarya

    Boris Johnson

    Asalin hoton, PA Media

    Tsohon firaministan Birtaniya, Boris Johnson, ya musanta zargin yi wa majalisar dokokin kasar karya, a lokacin zaman sauraron bahasi kan keta dokokin kullen korona.

    Kwamitin majalisar ne ya gudanar, da bincike da nufin tantance gaskiyar lamari game da ko ya fadi abin da ba haka yake ba ga ‘yan majalisar, kan batun taron shagalin da ya halarta a lokacin kullen na korona.

    An ci tarar Mista Johnson, tare da wasu jami’ai sama da 80, bayan da suka karya dokokin yaƙi da Korona wadanda gwamnatinsa ce ta kafasu.

    Tsohon firaministan ya amince cewar ya rudi majalisar, sai dai ya ce, bai yi hakan da gayya ko kuma da mummunanr aniya ba.

    Mista Johnson ya ce “Kamar yadda kuka bayyana, manufar wannan binciken, ba domin sake bude ce-ce-ku-ce kan batun halartar taron ba ne, abin da kawai ake so shi ne a gano ko na yi wa majalisar karya ko ban yi mata ba.”

    Mista Johnson dai ya ce, ko kadan bai yi wa majalisar karya ba, hasali ma dukkan abubuwan da ya furta ya fade su ne da kyakkyawar niyya.

  7. Ƙarancin Naira : NLC za ta rufe dukkanin ofisoshin Babban Bankin Najeriya

    ƴan ƙwadago na NLC

    Asalin hoton, OTHERS

    Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta umarci ma'aikata su fara zanga-zanga a dukkanin ofisoshin babban bankin ƙasar tun daga mako mai zuwa saboda ƙarancin takardun naira da ake fama da shi.

    Shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, wanda ya yi wa manema labarai a Abuja bayani game da shirin, ya ce daga jibi Juma'a ne za su fara haɗuwa sannan kuma su fara rufe dukkanin harkokin kasuwanci daga ranar Laraba mai zuwa a faɗin ƙasar.

    A ranar 13 ga watan nan na Maris ne ƙungiyar ta NLC ta bai wa gwamanatin tarayyar Najeriya wa'adin kwana bakwai na ta ɗauki matakan sassauta matsalar da ake fama da ita ta ƙarancin takardun kuɗin ƙasar na naira da kuma ƙarancin mai, ko kuma ta kira yajin aiki na ma'aikata.

    Shugaban ya ce, matakin zanga-zangar shi ne abu na ƙarshe da ƙungiyar za ta ɗauka kasancewar ta bi dukkanin matakan da ya kamata ta bi na ganin an samu sassauci kan tsananin wahalar da ma'aikata da sauran ƴan Najeriya ke sha saboda ƙarancin takardun kuɗin amma abin ya gagara.

  8. Gwamnatin Najeriya ta sha kaye a shari'ar ƙwato naira tiriliyan 70 saboda sakaci

    Abubakar Malami

    Asalin hoton, OTHERS

    Bayanan hoto, Kotu ta kori ƙarar ne saboda rashin mayar da hankali da lauyoyin gwamnati suka yi

    Babbar kotun tarayya a Lagos ta soke wata shari'a da gwamnatin tarayyar Najeriya ke neman ƙwato wasu kuɗi naira tiriliyan 70 da take zargin na ajiye a asusun bankuna 29 na wasu da take zargin sun sace su.

    Mai shari'a Peter Lifu ya zartar da cewa lauyoyin gwamnatin da kuma wasu masu zaman kansu da ta ɗauka haya ba su mayar da hankali sosai a kan shari'ar ba saboda haka ya soke shari'ar.

    Alƙalin ya yi matuƙar mamakin yadda lauyan gwamnatin tarayya a shari'ar Mohammed Ndarani, (SAN) daga baya kuma Femi Falana (SAN) kwatsam suka nuna alamun ja da baya a kan shari'ar ta zargin sace kuɗin wadda ke da muhimmanci matuƙa ga al'umma.

    Gwamnatin tarayyara Najeriya da ministan shari'a su ne masu zargi waɗanda ake zargin ko kuma masu kare kansu 19 yawanci bankuna ne da kamafanin mai na ƙasar NNPC da kuma kamafanin mai na Agip.

    Bankuna su ne Zenith Bank Plc, Polaris Bank Plc, Citi Bank Ltd, Stanbic IBTC Bank Plc, Standard Chartered Bank Plc, Sterling Bank Plc.

    Sauran su ne Union Bank Plc, Unity Bank Plc, Keystone Bank Plc, Heritage Bank Plc, First Bank Plc, United Bank For Africa Plc, Fidelity Bank Plc, Eco Bank Plc, Guaranty Trust Bank Plc, Wema Bank Plc, Access Bank Plc.

  9. Jihohi shida da suka koma hannun ƴan adawa a Najeriya

  10. Labarai da dumi-dumi, Jam'iyyar Labour ta lashe zaben gwamnan Abia

    Alex Otti

    Asalin hoton, alexottiofr/Twitter

    Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta sanar da Alex Otti na Jam'iyyar Labour a matsayin zababben gwamnan jihar Abia.

    Inec ta bayyana haka ne kwana hudu bayan zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

    Dama hukumar Inec ta dakatar da sanar da sakamakon zaben ƙaramar hukumar Obingwa saboda takaddamar da ta biyo baya da kuma matsalolin da aka fuskanta a karamar hukumar.

    Da wannan sakamako, dan takarar Jam'iyyar Labour Alex Otti ya doke abokin karawarsa na Jam'iyyar PDP Okey Ahiwe bayan da ya kasance wanda ya fi samun kuri'u masu yawa.

    Otti ya samu kuri'u 175,467 yayin da Ahiwe ya samu kuri'u 88,529.

  11. Amurka ta nemi Uganda ta sake nazari kan dokar hana ayyukan masu neman jinsi

    Anthony Blinken

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya ce ƙudirin dokar da ke nuna ƙyama ga masu neman jinsi wanda majalisar dokokin Uganda ta amince da shi, take ƴancin masu halayyar ne.

    Ya kuma buƙaci gwamnatin ƙasar ta sake tunani a kai.

    Ƙudirin wanda aka yi saurin amincewa da shi ya tanadi hukuncin ɗaurin rai da rai ga wanda ya bayyana kansa a matsayin mai neman jinsi.

    Mutanen da ke cikin ƙungiyoyin da ke goyon bayan tsiraru masu wannan ɗabi'a ma na iya tsintar kansu a gidan yari.

    Ƙudirin dai na buƙatar amincewar Shugaba Yoweri Museveni kafin ya zama doka kuma shugaban ƙasar ya sha nuna adawa ga wannan halayya ta neman jinsi.

    Ƙungiyoyin kare ƴancin bil adama da ƴan siyasa daga ɓangaren hamayya sun ce ƙudirin na ƙara janyo ƙyama ne ga masu luwaɗi.

  12. Za a daɗe ba a shawo kan matsalar ƙarancin ruwa a Somaliya ba - Unicef

    Somaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    Matsalar ƙarancin ruwa ka iya janyo mutuwar dubban 'yan somaliya, sakamakon mummunan farin da ke addabar ƙasar, kamar yadda jami'in Asusun Tallafa wa Ƙannana Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana wa BBC.

    Wani sabon rahoto da gwamnatin ƙasar tare da haɗin gwiwwar Majalisar Dinkin Duniya suka fitar, ya nuna cewa mutum 43,000 ne suka mutu a shekarar da ta gabata, kuma fiye da rabinsu yara ne ƙanana.

    Rahoton ya kuma yi ƙiyasin cewar daga watan Janairu zuwa Yunin wannan shekara wasu ƙarin mutum 25,000 za su iya mutuwa sakamakon ƙarancin ruwan, in ji jami'in.

    Ya kuma ƙara da cewa har yanzu akwai sauran lokaci domin kare dubban rayukan al'ummar ƙasar, inda ya yi kira ga ƙungiyoyin agaji da su ci gaba da taimaka wa ƙasar da tsaftataccen ruwa domin buƙatunsu na yau da kullum.

    Ya ce akwai buƙatar a haɗa hannu wajen taimaka wa mutanen Somaliya, domin su noma abincin da za su ci, tare da samun ƙoshin lafiya, ilimi da kuma kariya ga 'ya'yansu.

  13. Ethiopia ta cire ƙungiyar TPLF daga jerin ƙungiyoyin ta'addanci

    fd

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Habasha ta amince da cire sunan ƙungiyar 'yan tawayen TPLF daga cikin jerin ƙungiyoyin ta'addancin ƙasar.

    Hakan na zuwa ne watanni huɗu bayan da ƙungiyar ta sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi da gwamnatin ƙasar.

    Yarjejeniyar da aka cimma cikin watan Nuwamban bara a Afirka ta Kudu ta kawo ƙarshen rikicin da aka kwashe shekar biyu aka gwambzawa.

    Cire sunan ƙungiyar TPLF daga jerin ƙungiyoyin ta'addanci na daga cikin yarjejeniyar, wadda ta ƙunshi mayar da muhimman ayyukan gwamnati zuwa yankin tigray da ke arewacin ƙasar.

    To sai dai majalisar dokokin ƙasar ba ta cire sunan ƙungiyar 'Oromo Liberation Army' wadda a lokacin yaƙin ta bayyana mubaya'arta ga ƙungiyar TPLF.

    Firaministan ƙasar Abiy Ahmed ya sha cewa a shirye yake wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma da ƙungiyar a Afirka ta Kudu.

  14. Mesut Ozil ya sanar da yin ritaya daga buga tamaula

    ee

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon dan kwallon tawagar Jamus, Mesut Ozil ya sanar da yin ritaya daga taka leda.

    Tsohon dan kwallon Real Madrid da Arsenal ya rataye takalmansa yana da shekara 34 da haihuwa.

    Ozil ya fara taka leda a Schalke 04 daga nan ya koma Werder Bremen, sai dai ya taka rawar gani a gasar kofin duniya da aka yi a 2010.

    A wasan ne ya fito da kansa, inda Jamus ta ci Ingila 4-1 a wasan quarter finals, hakan ya sa Real Madrid ta dauke shi.

  15. Abba Gida-gida ya buƙaci masu taya shi murna su yi masa addu'a maimakon dogon tattaki

    Abba Gida-gida

    Asalin hoton, FAMILY

    Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci masu yin doguwar tafiyar ƙafa domin nuna murnarsu kan samun nasarar zaɓe da ya yi, da cewa su daina.

    A maimakon haka ya buƙace su da su yi masa addu'ar samun nasara a mulkinsa domin maido da ƙwarin gwiwar da 'yan jihar suka rasa cikin shekaru takwas da suka gabata.

    A wata sanarwa da zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa, Abba ya buƙaci magoya bayansa da 'yan jam'iyyarsa ta NNPP da su yi masa addu'ar samun nasara a mulkinsa.

    Sabon gwamnan ya ce yin addu'a kaɗai ta wadatar wajen nuna murna ga nasarar da ya yi a zaɓen na ranar Asabar, ba sai mutum ya shafe tafiyar kilomitoci masu yawa a ƙafa ba.

    Musamman a cewar sanarawar, idan aka yi la'akari da halin rashin tsaro na matsalar 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane, waɗanda ke barazana ga zirga-zirgar jama'a da kayayyaki a faɗin ƙasar.

    Yayin da yake gode wa magoya bayansa na ciki da wajen jihar Kano, zaɓaɓɓen gwamnan ya buƙaci masu doguwar tafiyar ƙafa da su daina, domin kuwa a cewarsa hakan ba zai taimaka wajen magance tarin matsalolin da ke jiran sabuwar gwamnatinsa ba, kamar yadda ya bayyana.

    A Najeriya dai matasa da dama kan jefa rayuwarsu cikin hatsari wajen yin doguwar tafiyar ƙafa domin taya wani gwaninsu murnar nasarar da ya yi ta lashe zaɓe.

    Matsan da a lokuta da dama kan ƙare doguwar tafiyar ba tare da samun ganawa da gwanin nasu ko makusantansa ba.

  16. Zimbabwe za ta yi wa ma'aikatan ƙasar ƙarin kashi 100 na albashi

    \x\

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin ƙasar Zimbabwe za ta ƙara wa ma'aikatan ƙasar albashi da kaso 100, a wani ɓangare na inganta jin daɗin ma'aikatan, kamar yadda kafar yaɗa labaran gwamnatin kasar ta ruwaito.

    A wata sanarwa da ma'aikatar kudi ta kasar ta fitar, ta ce sabon tsarin albashin ya ƙunshi ƙarin dala 250 na ƙuɗaɗen alawus-alawus ɗin korona ga duka ma'aikatan ƙasar, da kuma ƙarin dala 80 a kowane wata ga malaman makaranta.

    Sanarwar ta ce ƙarin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Maris ga ma'aikatan fannin tsaro, sai kuma 1 ga watan Afirilu ga duka sauran ma'aikatan ƙasar.

    Wakilan ƙungiyar malaman makarantar ƙasar sun ce ƙarin albashin 'abin a yaba' ne, to amma sun ce ƙarin alawus ɗin da aka yi na korona ya yi kaɗan.

    Wakilan kungiyar ma'aikatan jinya sun ce an tsara gudanar da ganawa ranar Laraba kan alawsu din koronan.

    A shekarar 2020, gwamnatin Zimbabwe ta ce ba za ta iya yin ƙarin albashi ba a daidai lokacin da likitocin ƙasar suka shafe fiye da wata hudu suna yajin-aiki, lamarin da ya ƙara kawo naƙasu ga fannin lafiyar ƙasar.

  17. Kotu ta yi watsi da buƙatar Abba Kyari

    ABBA KYARI

    Asalin hoton, @ABBA KYARI

    Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar da tsohon shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar 'yan sandan Najeriya Abba Kyari ya gabatar a gabanta, yana neman kotun ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi masa.

    Yayin zaman kotuna a ranar Laraba alƙalin kotun mai shari'a Emeka Nwite ya yi watsi da buƙatar Abba Kyari, yana mai cewa kotun na da hurumin sauraron ƙararrakin da suke da alaƙa da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi kamar yadda kundin tsarin mulki da dokar da ta kafa hukumar NDLEA suka ba ta dama.

    Abba Kyari ya faɗa wa kotun cewa hukumar NDLEA ta yi gaggawar gabatar da shi a gaban kotu, tun kafin a kammala bincike, yana mai cewa kamata ya yi hukumar ta bai wa 'yan sanda damar gudanar da binciken cikin gida, kafin ita NDLEA ta ɗauki mataki.

    Ya ƙara da cewa 'yan sanda sun gudanar da bincike kan lamarin kuma har sun gabatar da rahoton cikin gida ga rundunar 'yan sanda.

    Jami'in 'yan sanda ya ce za a gabatar da shi a gaban kotu ne kaɗai, idan 'yan sanda suka kammala gudanar da bincike.

    Ya kuma ce dokar aikin 'yan sanda ta ce hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta ƙasar na da ikon da za ta gudanar da bincike tare da ladabtar da jami'an 'yan sanda, kamar yadda majalisar ƙoli ta ayyukan shari'a ke da ikon ladabtar da ma'aikatan shari'a.

    To sai dai alƙalin kotun ya ce ikon da hukumar kula da ayyukan 'yan sandan ke da shi , bai zarta ikon da kotun tarayyar ke da shi ba.

    Kyari mai muƙamin mataimakin kwamshinan 'yan sanda, tare da wasu mutum huɗu da ke aiki a rundana ɗaya na fuskantar tuhume-tuhumen haɗin baki wajen safarar hodar ibilis da nauyinta ya kai kilogiram 17.55

  18. Magoya bayan APC na gudanar da zanga-zanga a Kano

    zabe

    Daruruwan magoya bayan jam'iyyar APC ke gudanar da zanga-zangar lumana a ofishin hukumar zabe ta INEC da ke a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Kano

    Masu zanga-zangar na buatar hukumar zaɓe ta sake nazari kan sakamakon zaben gwamnan jihar.

    sss

    Hukumar zaɓen dai ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar adawa ta NNPP a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

    zabe

    Bayan doke babban abokin hamayyarsa Nasiru Yusf Gawuna na jam'iyyar APC mai mulkin jihar

    bb

    Masu zanga-zangar sun ce kamata yayi a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba

    Jam'iyyar ta APC dai ta kuma miƙa wa hukumar INEC takardar ƙorafinta game da zaɓen

  19. Mutum biyar sun mutu sakamakon ɓullar cutar Marburg a Tanzaniya

    Tanzaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin ƙasar Tanzaniya ta tabbatar da mutuwar mutum biyar sakamakon ɓullar cutar Marburg a ƙauyukan Bulinda da Butayaibega da ke yankin Kagera a arewacin ƙasar cikin makon da ya gabata.

    Cutar, wadda ke cikin dangi ɗaya da cutar Ebola, na da tsanani, inda marasa lafiyar da suka kamu da cutar kan fuskanci zazzaɓi mai tsanani, da zubar da jini da kuma ciwon gaɓoɓi.

    Ministar lafiyar ƙasar Ummy Mwalimu ta ce mutum uku na kwance a asibiti domin karɓar maganin kan alamomin cutar da suka nuna.

    “Muna ƙoƙarin takaita yaɗuwar cutar, kuma muna da ƙwarin giwwar cewa ba za ta yaɗu zuwa wasu yankuna ba,'' in ji Mwalimu.

    Wata babbar jami'ar lafiyar ƙasar Farfesa Tumaini Nagu ta buƙaci mazauna ƙauyukan da cutar ta ɓarke da su guji haɗa jiki da mutanen da suka kamu da cutar.

  20. Amurka ta ce Najeriya ta gurfanar da mutanen da suka aikata laifukan zaɓe

    Dan sanda na yun.kurin kama masu tayar da hargitsi

    Amurka ta yi kira ga hukumomin Najeriya su tabbatar, sun gurfanar da mutanen da aka samu da hannu, ko waɗanda suka ba da umarnin a razana masu zaɓe ko suka daƙile harkar zaɓen gwamnoni a ƙasar.

    Cikin wani rahoto da Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar ta ce Amurka ta damu matuƙa kan aika-aikar da aka yi wa masu zaɓe ta hanyar razanarwa da daƙile yin zaɓe a jihohi irinsu Kano da Lagos.

    Amurka na wannan kira ne a matsayin wani martani ga zaɓen ranar Asabar da ta wuce na gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohin ƙasa

    Haka kuma Amurkan ta ce ita ma za ta yi nazari a kan dukkan matakan ladabtarwa da take da su, ciki har da ƙarin hana bizar shiga ƙasarta ga mutanen da aka yi imani suna da alhaki, ko an haɗa baki da su wajen yin zagon ƙasa ga tsarin dimokraɗiyyar Nijeriya.

    Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya ce jami'an diflomasiyyar Amurka da suka sa-ido kan zaɓuka a Lagos da sauran wurare sun ga irin waɗannan kura-kurai da idanuwansu.

    Sanarwar ta ce amfani da kalaman ƙabilanci a lokacin zaɓen gwamnan Lagos, musamman abin damuwa ne.

    Ta yaba wa duk 'yan siyasar Nijeriya da shugabannin addinai da na al'umma da matasa da 'yan ƙasar, waɗanda suka zaɓi bijire wa waccar hanya, kuma suka nuna adawa a kan irin waɗannan kalamai na ta da hankali da tunzura rikici, abin da ke tabbatar da ƙudurin 'yan ƙasar wajen mutunta tsarin dimokraɗiyya.

    Sanarwar ta ce bayan zaɓukan shugaban ƙasa na 25 ga watan jiya, Amurka ta bi sahun masu sa-ido na ƙasashen waje, wajen yin kira ga hukumar zaɓe ta gyara kura-kuren da aka samu a tsare-tsaren yin zaɓe da kuma amfani da na'urori.

    Kuma ga alama zaɓukan da suka wuce, sun nuna an samu gagarumin ci gaba, don kuwa akasari an buɗe rumfunan zaɓe a kan lokaci kuma an ga sakamakon zaɓe da yawa a shafin latroni da ke nuna sakamakon da aka wallafa a kan lokaci.

    Sanarwar ta sake yin kira ga duk masu ƙorafe-ƙorafe game da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jiha, su bi kadi ta hanyoyin da doka ta tanada, waɗanda kuma lallai ba za a yi musu katsalandan ba.

    Sanarwar ta sake yin kira ga al'ummar Nijeriya su haɗa kai wajen aiki tare kamar yadda suka shiga aka dama da su a zaɓen sabbin shugabanni kuma su ci gaba da ƙoƙari wajen ƙarfafa tsarin dimokraɗiyyar ƙasar mai cike da kuzari.