Masu zanga-zanga sun yi wawaso da sa wuta a gonar tsohon shugaban Kenya

Asalin hoton, OTHERS
Wani gungun masu zanga-zanga ya sanya wuta a wasu sassan gonar iyalan tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a abin da ake gani kamar wani martini ne ga mummunar zanga-zangar da ‘yan hamayya ke yi.
Wakilin BBC da ya kasance a gonar lokacin da masu zanga-zangar suka far mata, a wajen babban birnin kasar Nairobi ya ce ya ga yadda mutanen ke da kwasar tumakai inda wani ya ce zai sayar da wadda ya dauka dala 23.
Babu ‘yan sanda a wurin kuma wasu daga cikin masu zanga-zangar na dauke da adduna, inda suka rika sare bishiyoyi da sauran shuke-shuke, bayan sun kori ma’aikatan da suka tarar a gonar.
Masu harkokin kasuwanci da ke kusa da gonar da kuma wadanda suke tsakiyar birnin na Nairobi sun rurrufe.
Mutanen sun lalata wani gidan mai da aka ce na jagoran ‘yan hamayya ne
Raila Odinga.
Mista Odinga, wanda ke kawance da tsohon shugaban kasar Uhuru Kenyatta, ya gaya wa BBC cewa gamnati ce ta yi hayar masu zanga-zangar da suka lalata gonar tsohon shugaban kasar.
Sai dai gwamnatin ta Kenya ba ta ce komai ba game da wannan zargi.
Rikicin bayan zabe dai ba wani sabon abu ba ne a Kenya, to amma kai hari a kan kadarorin shugabannin siyasa abu ne da ba a saba gani ba a kasar ta gabashin Afirka.
Rahotanni sun ce an kashe akalla mutum daya a zanga-zangar a birnin Kisumu na yammacin kasar, inda yanki ne da ‘yan hammaya suke da karfi, lokacin da ‘yan sanda suka rinka harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa mutanen da suka rika kona taya da datse tituna.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An kashe akalla mutum uku tun bayan da zanga-zangar da barke a makon da ya gabata.
A unguwar Kibera da ke babban birnin kasar Nairobi inda Mista Odinga yake da magoya baya sosai, ‘yan sanda sun rika harbin masu zanga-zangar da ke jifa da duwatsu, da hayaki mai sa hawaye.
Da farko Mista Odinga da wadanda suka yi hadaka da shi Azimio la Umoja sun bukaci jama’a su fita su yi zanga-zanga ne a farkon watan nan a kan gazawar gwamnati wajen shawo kan tashin farashin kayayyaki.
Da kuma abin da ya kira magudin da ya bai wa Shugaba William Ruto nasara a zaben da aka yi na shekarar da ta gabata.
Duk da cewa kotun kolin Kenya ta amince da zaben, Mista Odinga ya kafe cewa an yi masa magudi ne inda ya bukaci jama’a su rika yin zanga-zanga a duk ranar Litinin da Alhamis.
Dukkanin jagororin siyasar da ke wannan dambarwa sun taba aiki tare a wani lokaci a can baya.
Mista Odinga tsohon firaminista ne wanda sau biyar yana takarar shugaban kasar ba tare da ya yi nasara ba.
Yayin da wa’adin mulkin tsohon shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya zo karshe sai shugaban ya zabi ya mara baya ga tsohon babban abokin hamayyarsa Mista Odinga maimakon mataimakinsa Mista Ruto.
A shekarar 2007 Mista Ruto shi ne mataimakin Mista Odinga a zaben shugaban kasar na wannan shekara, wanda a lokacin Mista Kenyatta ya ci.
Iyalan gidan su Kenyatta suna daga cikin wadanda suka fi mallakar filaye da kadarori a Kenya.
Manyan ‘yan kasuwa da ‘yan siyasar kasar kusan suna da alaka ta kut da kut.
Kusan za a iya cewa akwai tamkar wata yarjejeniya bayan duk wani wa’adi na shugabacin siyasa a tsakanin bangarori masu hamayya da juna na karba-karba.
Yanzu dai harin da ake kai wa kadarorin manyan ‘yan siyasa na kasar ya sa ana ganin kamar wannan yarjejeniya ta samu rauni.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka kai hari gonar su Shugaba Kenyatta sun tafka asara ne a dalilin zanga-zangar da Mista Odinga ya kira, wadda kuma suke zargin cewa Mista Kenyatta ne ya dauki nauyi.
Ana ganin wadannan kalaman da hare-haren kamar sun tabbatar da abin da shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin kasar Kimani Ichung'wah, ya furta a karshen mako cewa:
‘’Muddin aka barnata dukiya ko kadarar wani dan Kenya su ma za su mamaye gonakinsu kuma wadanda ba su da gonaki za su samu damar mallakar gona.
‘’Za ku dandana kudarku idan kuka ci gaba da angiza mutane su tayar da hankali da zubar da jini a kasar nan.
Kuma wannan shi ne sakona ga Uhuru Kenyatta, wanda shi ne mutum daya tilo mai daukar nauyin Azimio da sojan-haya shi ne Raila Odinga," in ji dan majalisar.
Da BBC ta tuntubi Mista Ichung'wah a ranar Litinin ya musanta wata alaka da mamayar da aka yi wa gonar ta su Uhuru Kenyatta.
Sannan kuma ya kasa bayar da wata sheda da ke tabbatar da zarginsa na cewa Mista Kenyatta ne ke daukar dawainiyar Mista Odinga.
Haka shi ma Mista Odinga ya muanta hannu a duk wata barna kan wata kadara.










