Yadda kantin sauƙi na 'yan China ke barazana ga 'yan kasuwar Kenya

Asalin hoton, EPA
An sake buɗe wani shagon sayar da kayayyaki na China a ƙasar Kenya mai suna 'China Square' bayan da 'yan ƙasar suka nuna damuwa game da yadda ake sayar da kayyakin cikin rahusa a shagon.
Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu ke cewa irin waɗan nan shaguna na taimakawa 'yan ƙasar, yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin cutarwa ga 'yan ƙasar.
Daruruwan manya da ƙananan'yan kasuwar Kenya ne suka taru a ofishin mataimakin shugaban ƙasar a birnin Nairobi suna buƙatar gwamnati ta kawo ƙarshen abin da suka kira ''mamayar China''.
Kwastomomi kan tururuwa zuwa kantin sayar da kayyakin, saboda sauƙi da arahar kayayyakin, lamarin da ya fusata 'yan kasuwar ƙasar.
A makon da ya gabata aka rufe kantin na ɗan wani lokaci sakamakon zanga-zangar da aka gudanar kan shagon.
Makonni biyar da buɗe kantin na 'China Square' ya zama wani abin ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, zaftare farashin kayayyaki da aka yi a kantin ya sa mutane da dama sun koma yin sayyaya a shagon.
To sai dai ƙananan 'yan kasuwa a ƙasar - waɗanda suke taimakawa sosai wajen gina tattalin arzikin ƙasar - sun fara fuskantar raguwar ciniki.
"Muna buƙatar ficewar China daga Kenya. Idan China ta zama mai ƙera abubuwa, kuma ta zama babbar dila, sannan kuma mai sayar da su a ɗaiɗaikunsu, to me 'yan Kenya za su ci?'' kamar yadda wani ɗan kasuwa ya bayyana wa 'yan jarida a lokacin zanga-zangar.
Peter Sitati wani mai shigo da kayayyakin tare da sayar da su a Nairobi, na ɗaya daga cikin masu zanga-zangar.
Ya kuma ce bahon goge ƙafa da yake sayarwa dala 43 a shagonsa, a kantin China Square ana sayar da shi dala 21, ragin fiye da kusan kashi 50 kan yadda yake sayar da shi.
"Yan kasuwar Kenya da dama na shirin rufe shagunansu kuma tattalin arzikinmu zai durƙushe'' in ji Mita Sitati.

Asalin hoton, PETER SITATI
Duk da tambayar da BBC ta yi wa masu kantin China Square , ba su bayyana dalilin da ya sa suka zaftare farashin ba, to sai dai hakan zai taimakawa kantin idan za a sayi kaya masu yawa.
Masu kantin Lei Cheng na da kyakkyawar alaƙa da masu ƙera kayayyakin. Mafiya yawan 'yan ƙasuwar Kenya na saro kayyakin ne a China ta hanyar wakilai, dan haka sukan biya kuɗi masu yawa, fiye da yadda masu kantin China Square ke sayowa.
Mamallakin kantin China Square Lei Cheng ya ce abin da ya yi bai saɓa wa doka ba.
Ya ƙara da cewa ya yi cikinikin fiye da dala 157,000 a makonni biyun farko da buɗe shagon.
"Mutanen da ke faɗa da mu suna ganin kamar mun zame musu barazana ne saboda a yanzu 'yan Kenya sun san da mu, kuma ba ma tsauwala farashi.''
'Kaya masu inganci, farashi mai rahusa'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu 'yan Kenya da dama na kallon kantin a matsayin sauƙi a garesu.
"Ya kamata a bar kantin China Square ya ci gaba da gudana, domin kuwa suna sayar da kaya masu inganci kan farashi mai rahusa,'' in ji wani dan ƙasar mai suna Sharon Wanjiku.
"Tsadar rayuwa ta yi yawa a yanzu, kuma farshin da kantin ya saka shi ne abin da muke buƙata a yanzu.''
Fice da kantin ya yi sakamakon ƙorafe-ƙorafen 'yan kasuwar ƙasar ya janyo hankalin gwamnatin ƙasar, yayin wani minista ke cewa ya kamata kantin ya daina sayar da ɗaiɗaikun kaya, ya koma bayar da sari.
"Muna maraba da masu zuba jari daga China, amma a matsayin masu kafa masana'antu, amma ba masu sayar da kayayyaki ba,'' in ji ministan kasuwancin ƙasar Moses Kuria kamar yadda ya wallafa a shafinsa Twitter ranar Juma'a kafin a rufe kantin..
Kawo yanzu dai ba a san dalilin da ya sa kantin ya daina sayarwa kwastomi kayyaki ba. to ama ana zargin cewa hukumomin kasar ne suka matsa masa lamba.
To sai a sanarwar da kantin ya fitar ya ce ya rufe sayar da kayyakin ne domin sake shirya tsare-tsarensa, tare da duba yiyuwar hada gwiwa da 'yan kasuwar ƙasar.

Asalin hoton, EPA
To sai dai a ƙarshen makon da ya gabata, hukumar kula da ingancin kayayyaki ta ƙasar ta ce ta binciki ƙorafin da aka yi wa kantin na sayar da kayyaki marasa inganci, to amma ba ta samu wata hujja da ta nuna haka ba.
A ranar Litinin ƙungiyar 'yan kasuwar Kenya da ta China sun yi maraba da sake buɗe kantin bayan tattaunawa da gwamnati, to sai dai ƙungiyar ba ta yi cikakken bayani game da abin da tattaunawar ta ƙunsa.
Dokar zuba jari ta Kenya wadda ta sanya sharuɗa kan masu zuba jari daga waje, ta tanadi cewa duk jarin da za a zuba a ƙasar sai ya zama mai amfanar da ƙasar ta hanyar samar da ayyuka, da koyawa 'yan ƙasar dabaru fasahohin zamani.
Babu dai wasu alƙaluma a hukumance da suke nuna yawan 'yan kasuwar China da ke cikin Kenya, to sai dai a 'yan shekarun baya-bayan nan ana samun yawan masu kiraye-kirayen masu ƙin jinin China a ƙasar.
Wannan kuma ba ya rasa nasaba da zarge-zargen wariyar launin fata da ake yi wa 'yan ƙasar China a Kenya, tare da fargabar ƙwace sana'o'i da ayyuka a ƙasar.
Korar baƙi
A shekarar 2019, hukumomin Kenya sun tisa-ƙeyar 'yan China bakwai zuwa gida bayan sun kwashe shekaru suna kasuwanci a birnin Nairobi, bayan da ka zarge su rashin takardar izinin yin kasuwanci a ƙasar.
Haka kuma a shekarar 2020, an mayar da wasu 'yan China huɗu zuwa gida, bayan da aka zarge su da zane wani ɗan Kenya da ke aiki a wani gidan abinci mallakin 'yan Chinan a ƙasar.
Kantin China Square ba ƙaramin shago ba ne, to amma sake buɗe shi zai ci gaba yi wa ƙananan 'yan kasuwa barazana, waɗanda ke ci gaba da yin ƙorafi.










