Waiwaye: Bai wa Tinubu da Shettima lambobin girmamawa da kaddamar da matatar man Dangote

An wallafa

Waiwaye na wannan makon zai yi dauraya ne kan muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya daga 20 zuwa 27 ga watan Mayu ciki har da cikar NYSC shekara 50 da kafuwa da isar jirgin kamfanin Najeriya na 'Nigeria Air' a Abuja.

Wanke Alhassan Doguwa daga zargin kisan kai

Alhassan Ado Doguwa

Asalin hoton, TWITTER/ADO DOGUWA

Bayanan hoto, Alhassan Ado Doguwa

A makon da muka yi wa bankwana ne Ma'aikatar shari'a ta jihar Kano ta ce binciken da ta gudanar kan tuhumar da ake yi wa ɗan majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa kan laifin kisa, ya nuna cewa ba a same shi da laifin da ake zargi ba.

Lokacin da ya yi wa manema labarai bayani, kwamishinan shari'a na jihar Kano, Lawan Musa Abdullahi ya ce an samu saɓani da dama cikin bayanan da aka samu daga wurin shaidu.

Ya ƙara da cewa a yayin da suke gudanar da bincike sun gano cewa ma'aikatan asibiti ba su yi cikakken bincike kan mutanen da ake zargin an harba da bindiga ba, soboda haka ba a iya tabbatar da cewa an harbe su ba.

Kwamishinan ya ce an gudanar da bincike kan bindigogi da harsasai da ke hannun 'yan sandan da ke tare da ɗan majalisar a lokacin da rikicin ya faru.

Sai dai a bayanin nasa babu wata shaida da ta nuna cewa an yi amfani da bindigogin, kasancewar jami'an ƴan sandan sun mayar da daidai adadin harsasan da ke a hannunsu.

Mika wa Tinubu da Shettima lambobin girmamawa

Buhari da Tinubu

Asalin hoton, Buhari Sallau/Facebook

Bayanan hoto, Buhari da Tinubu

Shugaba mai barin gado Muhammadu Buhari ya bai wa Shugaban Ƙasa mai jiran gado Bola Tinubu lambar girmamawa mafi daraja a Najeriya ta GCFR.

Shugaba Buharin ya kuma bai wa zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima lamba ta biyu mafi girma ta GCON.

An ba su lambobin girmamawar yayin wani biki da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja.

Kaddamar da matatar man Dangote

Muhammadu Buhari da Aliko Dangote yayin kaddamar da matatar man Dangote

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Muhammadu Buhari da Aliko Dangote yayin kaddamar da matatar man Dangote

A ranar Litinin ɗin da ta wuce ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da matatar mai ta Dangote, wadda ke da ƙarfin tace mai ganga dubu 650 a rana.

Shugaban matatar, Sanjay Gupta ya ce ita ce irinta mafi girma a duniya.

Wasu masana na cewa matatar za ta samar da ayyukan yi ga mutane da dama a Najeriya.

Kuma za ta samar da abubuwa kamar man fetur (PMS) da man dizil (AGO) da man jirgin sama da kalanzir da ma wasu abubuwan da dama.

Shekara 50 da kafuwar shirin NYSC

A cikin makon da ya wuce ne shirin yi wa kasa hidima da ake kira da NYSC ya cika shekara 50 tun bayan kafa shi.

An gina shirin don hada kan kasar da ta fuskanci yakin basasa daga shekarar 1967 zuwa 1970.

Gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon ta kafa dokar da ta tanadi tsarin ne a ranar 22 ga watan Mayun 1973 don "sake shiryawa, da ginawa da kuma sasanta" 'yan Najeriya bayan yaƙin na basasa.

Akan tura ɗaliban da suka samu shaidar karatu ta digiri ko babbar difiloma (HND) zuwa jihohin da ba nasu na haihuwa ba don yi wa ƙasa hidima.

Akasari ana tura mazauna kudanci zuwa arewaci, su ma 'yan arewa haka.

Yan Najeriya da dama da suka shiga shirin sun bayyana irin nasararorin da suka samu sanadiyyar NYSC - wasu aiki, wasu abokan zama, wasu kuma sauya wurin zama.

Watsi da karar PDP ta neman soke cancantar takarar Tinubu

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da karar da PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar suka daukaka zuwa gabanta ta neman soke cancantar takarar Bola Tinubu da mataimakinsa na jam'iyyar APC.

A hukuncin da kotun mai alkalai biyar ta sanar ranar Juma'ar da ta wuce, ta ce PDP ba ta da dama a doka ta yi kara a kan lamarin saboda a cewar kotun PDP ba mamba ce ta jam'iyyar APC ba.

Masu korafin suna ikirarin cewa zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa, Tinubu ya saba wa sassa na 29(1), 33, 35, da kuma na 84(1)(2) na dokar zabe ta kasar ta 2022.

A karar sun ce Shettima ya saba doka saboda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa da kuma kujerar majalisar dattawa ta Borno ta tsakiya a lokaci daya.

A don haka ne wadanda suka shigar da karar suke neman kotun ta soke cancantar APC da Tinubu da Shettima daga takarar wadda suka riga suka yi ta zaben shugaban.

Hukuncin kotun kolin ya kasance daidai da wanda wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi tun da farko.

Ɗan takarar shugaban kasar na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 ya ce watsi da ƙarar PDP da kotun koli ta yi ba zai karya masu gwiwa ba.

Isar jirgin kamfanin Najeriya Air

Jirgin 'Nigeria Air'
Bayanan hoto, Jirgin 'Nigeria Air'

Jirgin Kamfanin Nigeria Air ya isa Abuja, babban birnin ƙasar daga birnin Addis Ababa na Habasha ranar Juma'a.

An dai jima ana ce-ce ku-ce kan kamfanin bayan da aka yi ƙoƙarin ƙaddamar da shi a shekarun baya amma abin ya ci tura.

A baya-bayan nan ne Ministan sufuri na Najeriya, Sanata Hadi Sirika ya bayyana cewa jirgin saman kamfanin Nigeria Air zai isa ƙasar yau, wani lamari da zai kasance babban ci gaba ga shirye-shiryen soma tafiyar da harkokin kamfanin.

A watan Maris, ministan, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a ɓangaren sufuri, ya tabbatar da cewa kamfanin Nigeria Air zai soma aiki gadan-gadan kafin ƙarshen gwamnatin Muhammadu Buhari.

Sako cikamakin yan matan Sakandaren Yawuri da aka sace

Ƙungiyar iyayen daliban makarantar yan mata ta Yawuri da ke jihar Kebbi ta tabbatar da dawowar daliban makarantar biyu da suka rage a hannun ‘yan bindiga.

Ƴan matan na daga cikin dalibai 11 na kwalejin gwamnatin taryya da ake zargin Dogo Giɗe ya yi garkuwa da su, kuma ya sako su ranar Laraba.

Salim Ka'oje, shugaban ƙungiyar iyayen daliban Makarantar Yawuri da aka sace yaransa ne ya tabbatar da isowarsu gida yau Alhamis. Sannan ya ce cikin daliban da aka ceto har da wata daliba da "yan bindigar suka dauko daga Kaduna.

Ya bayyana wa BBC cewa zuwa yanzu babu wata ɗaliba da ta rage a hannun ƴan bindigar.

Ka'oje ya ƙara da cewa "akwai wata yarinya da aka kamo daga Kaduna aka haɗa da yaran amma ba ta cikin yaran ƴan makarantan na Yawuri, sai ɓangaren iyaye suka sanya ta cikin tattaunawarsu kuma sun ci nasara, yanzu haka kowa ya dawo gida."

Yajin aikin ma'aikatan lafiya na sai-baba-ta-gani

Harkokin kula da lafiya sun sake gamuwa da cikas a asibitocin gwamnati a Najeriya a , sakamakon yajin aikin da ma'aikatan lafiya suka shiga na sai-abin-da-hali-ya-yi.

Ma'aikatan wadanda ba su kunshi likitoci da jami'an jinya ba wato nas-nas, a karkashin hadaddiyar kungiyar JOHESU, sun dauki wannan mataki ne a fadin kasar saboda batutuwan da suka shafe albashi da kuma kula da jin dadinsu.

Gamayyar kungiyar ta ce ta bai wa gwamnati wa'adin mako biyu domin biya wa ma'aikatan bukatunsu amma kuma ba abin da aka yi.

Ma'aikatan su ne ke kula da bayanan marassa lafiya da dakunan gwaje-gwaje da sauran ayyuka a asibitocin gwamnati a Najeriya.

Yajin aikin ya tilasta wa wasu marassa lafiya tafiya asibitocin ƴan kasuwa, marassa hali kuwa sun rasa na yi, wanda hakan ke jefa rayuwar wasu da dama cikin hadari