'Tasirin da NYSC ta yi a rayuwarmu'

Asalin hoton, Facebook/NYSC
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
Matasa ɗalibai a Najeriya da dama za su yarda da ni idan na ce da yawansu ba su taɓa saka ƙafarsu a wata jihar da ba tasu ba sai a dalilin shirin yi wa ƙasa hidima - ko kuma bautar ƙasa - na NYSC.
Da ma manufar gwamnatin Najeriya ke nan lokacin da ta ƙirƙire shi shekara 50 daidai wadaida da suka gabata da zimmar haɗa kan ƙasar da ta fuskanci yaƙin basasa daga shekarar 1967 zuwa 1970.
Ni kaina da nake magana ban taɓa kwana a Jihar Katsina ba kafin 2018, lokacin da aka tura ni don zaman sansanin NYSC na Jihar Borno. Mun yi sansani a Katsina ne saboda rikicin Boko Haram da ake fama da shi a Borno.
Gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gawon ta kafa dokar da ta tanadi tsarin ne a ranar 22 ga watan Mayun 1973 don "sake shiryawa, da ginawa da kuma sasanta" 'yan Najeriya bayan yaƙin na basasa.
Akan tura ɗaliban da suka samu shaidar karatu ta digiri ko babbar difiloma (HND) zuwa jihohin da ba nasu na haihuwa ba don yi wa ƙasa hidima. Akasari ana tura mazauna kudanci zuwa arewaci, su ma 'yan arewa haka.
Da yawan ma'abota shafukan BBC Hausa a dandalin sada zumunta sun bayyana alfanun da suka samu sakamakon shiga shirin, kama daga samun abokin aure, da samun aiki, da shiga sabuwar rayuwa, zuwa sauya wurin zama da kuma samun sabbin abokai.
Baya ga aikin yi wa ƙasa hidima, corpers - kamar yadda ake kiran su a Turance - kan yi wasu ayyuka kamar na zaɓe, da ƙidayar 'yan ƙasa da kuma aikin rajistar zaɓe.
Masu yi wa ƙasa hidima kusan 200,000 ne suka yi aikin wucin-gadi a babban zaɓe na 2023 da aka kammala a watan Fabarairu.
'Ba don bautar ƙasa ba ba zan iya zama a ƙauyen da na je ba'

Asalin hoton, NYSC
Ya zuwa watan Agustan 2019, fiye da ɗalibai miliyan huɗu da 700,000 ne suka ci gajiyar tsarin kamar yadda shugaban hukumar na lokacin, Janar Shuaibu Ibrahim, ya bayyana.
Duk da cewa ba ta bayyana shekarar da ta kammala tata hidimar ƙasar ba, Hafsat M. Auwal ta ce ta dalilin NYSC ta je wani ƙauye.
"Dalilin NYSC na bar garina, na je wani garin. Wani garin ma ƙauye ne wanda ba don bautar ƙasa ba babu abin da zai zaunar da ni a ƙauyen," kamar yadda ta bayyana a Facebook.
Shi ma Ibrahim Aliyu Dankawu a Facebook ɗin, ya ce a dalilin NYSC ya "fara jin Fulatanci, ya hau Tsaunin Mambila, ya je garin sanyi na Saradauna".
Ya ƙara da cewa "ni kam na ji daɗin wannan lamari".
'Har yanzu muna hulɗar kasuwanci da budurwata da muka haɗu a Fatakwal'

Asalin hoton, Facebook/Comrade Teekay Yakasa
Ga wani wanda ya kira kan sa Comrade Teekay Yakasai a Facebook, har yanzu yana cin arzikin hidimar ƙasar da ya je garin Fatakwal na Jihar Rivers.
Comrade ya ce har yanzu yana hulɗa da wata budurwarsa da suka haɗu a sansani, inda har ya yi nasarar hana ta shan giya, kamar yadda ya yi iƙirari.
"Tun da muka gama kowa ya tafi ƙauyensu," in ji shi. "Sai dai tabbas yanzu haka duk wani kaya da nake saya daga Fatakwal ita take turo min, sannan duk abin da za ta saya daga Kano ni nake tura mata."
'Ta dalilin NYSC na iya Turanci'

Asalin hoton, NYSC
A gefe guda kuma, wani ma suna Mansur Sarauta Dansadau a Facebook ya ce shi ba hidimar ƙasa ya je ba amma duk da haka ya ci amfanin NYSC a garinsu.
"NYSC ta yi tasiri sosai a rayuwata lokacin ina ƙaramar sakandare ta Dansadau.
"Ta hannun corper a wannan lokacin na iya Turanci bakin gwargwado; Corper Abdulrashid da corper Samuel."
'Har yanzu ina aiki da abin da na koya a wajen NYSC'

Asalin hoton, Facebook/NYSC
Idan muka leƙa dandalin Twitter kuwa, wani mai suna Abu Hanan ya ce har yanzu yana ci gaba da aiki da abin da ya koya a wurin da aka tura shi aiki.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Nura Sani Aja kuma cewa: "Saka uniform kamar jami’in tsaro."
Dan Babba kuma yana ganin NYSC ɓata masa lokaci ya yi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2










