Waiwaye: Tsintar Hamdiyya a dajin Zamfara da zargin Zulum kan masu rura rikicin Boko Haram

Asalin hoton, Abba Hikima/Facebook
Za a iya cewa babban abin da ya ja hankalin mutane a Najeriya a makon jiya ne ɓacewa da tsintar matashiya Hamdiyya Sidi Shariff.
Tun ranar Talata ne aka bayar da rahoton ɓatan Hamdiyya Sidi Sharif, bayan ta fita domin zuwa kasuwa, lamarin da ya sanya ta kasa bayyana a zaman kotu kan shari'ar da ake mata a ranar Laraba a Sokoto.
A watannin baya ne dai gwamnatin jihar Sokoto ta shigar da matashiyar ƙara a gaban kotu, bisa zargin ta da aikata laifin tunzura tayar da zaune tsaye, shari'ar da har yanzu ake gudanar da ita.
A tattaunawarsa da BBC, lauyan da ke kare Hamdiyya, Abba Hikima ya ce yanzu haka tana wani asibiti da ke ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara "cikin mummunan yanayi."
Me zargin da Zulum ya yi wa ƴansiyasa da jami'an tsaro da hannu a rikicin Boko Haram ke nufi?

Asalin hoton, Borno Gov/X
Haka kuma a makon ne ƴan Najeriya suka riƙa tsokaci game da kalaman da Gwamnan jihar Borno ya yi, cewa akwai hannun wasu daga cikin 'yansiyasa da jami'an tsaron kasar wajen tsegunta bayanai da kuma hadin baki da 'yan kungiyar Boko Haram.
Masanan na ganin ya kamata a rika daukar ire-iren wannan zargin da matukar muhimmanci, kuma a bi sawunsa, har gano bakin zaren, domin a magance matsalolin tsaron ta hanyar tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya furzar da wannan kakkausan zargi ne a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta News Central.
An ruwaito gwamnan na cewa: ''Ina kuma so in shaida maku, cewa a cikin jami'an tsaro da 'yansiyasa da kuma jama'ar gari akwai masu tsegunta bayanai da hada baki da 'yan kungiyar Boko Haram.
Dakatar da kallo finafinan Hausa masu dogon zango
A makon ne dai hukumar tace finafinai ta Kano ta sanar da matakin dakatar da wasu finafinai masu dogon zango.
Lamarin ya janyo muhawara game da matakin da Gwamnatin jihar Kano ta ɗauka na dakatar da nuna wasu fina-finan Hausa masu dogon zango guda 22, waɗanda hukumar ta zarga da saɓa ƙa'idarta.
Lamarin wanda ya zo makonni kaɗan bayan gwamnatin jihar ta Kano ta dakatar da watsa shirye-shiryen siyasa na kai-tsaye ya jawo muhawara sosai, musamman a kafofin sadarwa, inda wasu suke nuna jin daɗinsu da matakin, wasu kuma ke kushewa.
An ƙirƙiri hukumar tace finafinai ta Kano ne domin tabbatar da an bi ƙa'idoji ɗab'i da harkokin fasaha a jihar Kano, wanda hakan ya sa aka fi ganin ayyukan hukumar a kan masana'antar Kannywod.
Hakan ya sa BBC ta yi waiwaye kan lokuta biyar da aka samu takun-saƙa tsakanin masana'antar da gwamnati.
Da gaske alƙawarin ta-zarce ke haifar da guguwar sauyin sheƙa a Najeriya?

Asalin hoton, PRESIDENCY
Haka kuma guguwar sauyin sheka da 'yan siyasar Najeriya ke yi daga jam'iyyun adawa zuwa jam'iyyar da ke kan gwamnati na cigaba da jan hankali da raɗe-raɗi tsakanin masu zargin ruwa ba ta tsami banza.
Bayanai daga galibin al'umma na ƙara fitowa, inda wasu ke cewa ƴan adawa masu sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki a Najeriya suna yin haka ne a bisa alƙawurra daban-daban da aka yi masu.
Sai dai mafi yawan masu sauya sheƙar dai suna kafa hujja ne da rikicin cikin gidan jam'iyyun su, wanda suka ce ya tilasta masu ficewa domin samun mafita.
Amma bayanan da ɓangarorin da lamarin ya shafa ke yi na nuni da cewa kowa da irin hanyar da ya bi domin kaiwa ga matakin da ya ɗauka.
Allah Ya isa duk wanda ya ce APC nake yi wa aiki - Damagum

Asalin hoton, FACEBOOK/Umar Iliya Damagum
A makon kuma, wani babban abu da ya ɗauki hankali shi ne yadda Shugaban babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, Ambasada Umar Iliya Damagun, ya musanta zargin da wasu ke yi masa cewa yana yi wa jam'iyya mai mulkin kasar, APC aiki ne shi ya sa rikicin PDP din ya ki ci ya ki cinyewa.
A hirarsa da BBC Ambasada Damagun ya ce shi kam tsakaninsa da masu zargin cewa shi ɗan-amshin-shata ne na jam'iyyar APC, ba a bin da zai ce sai, ''Allah Ya isa.''
Ya ce : ''Allah ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan Kazafi, kuma Allah Zai yi mana shari'a, in da zan shiga jam'iyyar APC da tun lokacin Buhari da na shiga.
''Kuma ina da tarihi tun da na shiga jam'iyyar PDP a 1999 ban taɓa sauya sheka ba. Dole wanda ba ya so na zai nemi yanda zai yaɓa min zargi don ya samu biyan buƙatarsa. An ce ma na je na yi mitin da Tinubu, a Ingila, wannan duk masu yin wannan na bar su da Allah.'' In ji shugaban na PDP.
Manyan ayyukan da aka zargi ƴan majalisar Najeriya da cusawa cikin kasafin 2025

Asalin hoton, BBC/Pidgin
A wani labarin da ya tayar da ƙura a makon kuma, wata ƙungiya mai sanya ido kan kasafin kuɗi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka da ake kira da 'BudgIT' ta fitar da rahoton da ya ce ya gano wasu ƴan majalisar dokokin Najeriya na cusa kwangiloli marasa alfanu ga ƙasa a cikin kasafin kuɗin ƙasar na 2025, ƴan Najeriya ke ta fama mayar da martani.
Ƙungiyar ta BudgIT ta ce ta gano kwangiloli har 11,122 waɗanda za su lashe kuɗin da ya haura naira tiriliyan 6.93 da aka saka a cikin kasafin kuɗin 2025 da Majalisar ƙasa ta cusa ba tare da la'akari da cancanta ba.
BudgIT ta ƙara da cewa an cusa irin waɗannan ayyuka ne a kasafin hukumomi da ma'aikatun gwamnati waɗanda ba su da wata alaƙa da ayyukan ma'aikatun.










