BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Amurka ta fitar da sabbin takunkumai a fannoni 5 domin illata Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftanta da kuma sassan duniya na ranar Litinin 24 ga watan Agusta, 2026.
Me ya sa malaman addini suka fara nuna inda suka karkata a siyasance?
A tsawon shekaru, malaman addini na daga cikin fitattun muryoyin da al'umma ke saurare a Najeriya, musamman a arewacin ƙasar.
Su wane ne suka sace masallata a ƙauyukan jihar Neja?
Bayyanar wani bidiyo da ake zargin daga ƙungiyar Lakurawa ya sake jefa al'ummar jihar Neja cikin fargaba da tashin hankali, bayan da aka ga gomman mata da ƙananan yara tare da wasu mutane zaune a cikin wani daji.
Abin da ya sa na daina amfani da man bilicin
”Idan kin fara kina ganin a yanzu fatar ki na yin kyau, to daga baya fatar za ta zo ta lalace. Kuma zai sa ki rage kwarin gwiwar shiga mutane, har ma ya iya shafar lafiyar ƙwaƙwalwa“. 2.”Farko sai da na daina sauraron maganganun mutane, na baro Jihar Kank inda aka sanni a fara, sannan na sauya irin mayukan da nake amfani da su”
Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023
Tun bayan zaɓen 2023, an samu manyan sauye-sauye a fannonin siyasa da tattalin arziki a Najeriya, kuma waɗannan canje-canje na iya yin tasiri kan sakamakon zaɓe mai zuwa.
'Yadda aka zane ni a bainar jama'a saboda aikata zina'
BBC ta samu zantawa da biyu daga cikin mata da yawa da kotu, a ƙarƙashin gwamnatin Taliban ta yanke wa hukuncin zaman gidan yari a cikin shekara biyar kuma waɗanda tuni aka zartar masu da hukuncin da ya haɗa da bulala a bainar jama'a.
Ma'aikatun bogi huɗu da aka gano a Najeriya a 2026
A Najeriya an sake bankaɗo wata hukumar bogi yayin da har yanzu ba a gama da batun wadda aka bankaɗo tun farko ba, wadda a yanzu batun yake kotu.
Labarin yarinyar da ta fara jinin al'ada tun tana shekara 6
Balaga kafin balaga yana haifar da ci gaban halayen jima'i da wuri a cikin yara kuma yana shafar 'yan mata ba daidai ba.
Wata haɗakar malamai a Arewacin Najeriya ta amince Tinubu ya zarce
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftan ƙasashe da kuma sauran sassan duniya na ranar Lahadi 23 ga watan Agustan 2026.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 25 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 24 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 24 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 24 Agusta 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Chelsea ta doke Fulham 2-3 har gida
Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da kasuwar 'yan wasanni ta duniya daga nan BBC Hausa daga 24 zuwa 30 ga watan Agusta
'Yan wasan Najeriya da za su haska a gasar Premier League ta 2026/27
A gasar Premier League ta 2026/27, za a ganin wasu matasan ’yan wasan Najeriya, inda kusan ’yan Super Eagles tara ke wakiltar kungiyoyi biyar daban-daban.
Man City ta amince da farashin Fernandez, Balde na son tafiya Man Utd
Man City ta yarda za ta sayi Fernandez yayin da Liverpool ke tunanin tayi na uku a kan Yankuba Minteh, na Gambia shi kuwa Balde ya matsa Barcelona ta sake shi ya tafi Man Utd.
An ci tarar Messi bayan marin ɗanwasa
Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni ne daga sassan duniya, kasuwar musayar 'yan wasa da kuma manyan sauye-sauyen da ke faruwa a fagen
Alvarez na shirin zuwa Arsenal, Man Utd na son Balde
Ɗanwasan gaban Atletico Madrid Julian Alvarez a shirye yake ya koma Arsenal, Tottenham na da kwarin gwiwar kammala cinikin Omar Marmoush, yayin da Ollie Watkins ke son komawa Al-Hilal.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Me ke sa maza neman maganin ƙara girman mazakuta duk da haɗarinsa?
Mazan da aka yi musu aikin tiyatar ƙara girman mazakuta za su iya sa ran girman ya ƙaru da kashi 10 zuwa 20 cikin ɗari a tsawon wata shida zuwa tara masu zuwa -amma ana iya samun saɓani aikin ya zo da matsala.
Bidiyo, Shin zai yiwu a dawo da tallafin man fetur a Najeriya?, Tsawon lokaci 1,50
Cacar baki ta kaure bayan da ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar ADC Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa zai mayar da tallafin man fetur a ƙasar idan ya samu nasarar zama shugaban kasa a zaɓen 2027.
Muhimman sarautu 7 da ake ba mata a ƙasar Hausa
A tarihin masarautun ƙasar Hausa, mata ba ƴan kallo ba ne kawai a tsarin yadda ake gudanar da mulki, suna taka muhimmiyar rawa a harkokin fada da shi kansa gidan sarauta, ta hanya daban-daban da aka tanadar musu.
Me ya sa muke tsoron wasu abubuwa da wataƙila ba za su cutar da mu ba?
Yawancinmu muna jin tsoron abubuwan da ba sa haifar da babbar barazana. Masana kimiyya ba su yi imanin cewa tsoro abu ne na dabi'a da ake haihuwar mutum da shi ba—daga ina ake samun wannan tsananin tsoro?
Yadda yanbindiga suka abka Masallatan Juma'a suka saci mutane a Neja
Wasu yanbindiga sun kai hari a wasu kauyuka na jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya inda suka kwashi mutane da ba a san yawan su ba a lokacin da suke Sallar Juma'a.
Tinubu ya taya ƴar Najeriya murnar lashe musabaƙar Alqur'ani ta duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftan ƙasashe da kuma sauran sassan duniya na ranar Asabar 21 ga watan Agustan 2026.
Muhimman mutanen da za su jagoranci yaƙin zaɓen Tinubu na 2027
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari ne Darakta Janar (DG) na kwamitin yaƙin neman zaɓen na APC.
Me ya sa wasu yaran ba su kai saura fahimta ba a makaranta?
Masana lafiya sun ce 'Dyslexia na shafar kusan kashi 20 cikin ɗari na al'ummar duniya. Duk da haka ana ganin wannan adadi ma bai kai ainihin yawan masu fama da ita ba.
Makaman yaƙi 9 da za su sauya fasalin yaƙe-yaƙe a duniya
Yanzu salon yaƙi na ƙara karkata zuwa makaman da ba a iya ganinsu cikin sauƙi, waɗanda ke amfani da fasahar AI, fasahar laturoni da kuma tsaron sararin samaniya.
Ko Iran za ta iya kai wa ƙasashen Turai hari?
Iran na iya kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Turai idan Donald Trump ya sake kai wa Iran hari, a cewar jaridar Financial Times, wadda ta ce ta samu wannan bayani daga majiyoyin da ke kusa da hukumomin Iran.
Ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin Iran a yanzu - Pezeshksian
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftan ƙasashe da kuma sauran sassan duniya na ranar Juma'a 21 ga watan Agustan 2026.
Sinadaran gina jiki 5 da mata ke buƙata
Cin abinci mai gina jiki da kuma daidaitaccen tsari shi ne ginshiƙi mafi muhimmanci na lafiyar jiki. Saboda haka, irin zaɓin abincin da kike yi yana da babban tasiri ga ƙoshin lafiyarki da kuma yadda za ki tsufa cikin koshin lafiya.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































