Nottingham Forest na son sayen Delap daga Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Nottingham Forest na aiki kan yarjejeniya domin daukar ɗan wasan gaba na Chelsea, Liam Delap.
Chelsea ta bayyana cewa a shirye take ta sayar da ɗan wasan mai shekaru 23 kan kuɗin fam miliyan 50, kuma a halin yanzu yana atisaye ne daban da tawagar farko ta ƙungiyar.
Har yanzu ba a tabbatar ko tattaunawar da ake yi ta shafi saye na dindindin ko kuma aron ɗan wasan ba, amma an san cewa Nottingham Forest da Chelsea suna da kyakkyawar alaƙar aiki tsakaninsu.
Ba a fito da Delap ba cikin tawagar Chelsea da ta buga wasan Premier League da Fulham a ranar Litinin, sannan a makon da ya gabata ya rasa rigarsa mai lamba 9 inda aka bai wa takwaransa na gaba Joao Pedro.
Yiwuwar barinsa Stamford Bridge na zuwa ne bayan fiye da shekara guda kacal da komawarsa Chelsea daga Ipswich Town kan kuɗin fam miliyan 30.
Sai dai kakar wasan da ta gabata ba ta yi masa daɗi ba, domin ya kammala ta ne da ƙwallo ɗaya kacal a Premier, sakamakon raunukan kafaɗa da kuma tsokar baya cinyarsa da suka hana shi buga wasanni akai-akai.

















