Me ya sa malaman addini suka fara nuna inda suka karkata a siyasance?

Asalin hoton, Kano State Govt
A tsawon shekaru, malaman addini na daga cikin fitattun muryoyin da al'umma ke saurare a Najeriya, musamman a arewacin ƙasar.
Sai dai duk da tasirin da suke da shi a tsakanin mabiyansu, ba kasafai ake ganin ƙungiyoyin malaman addini suna fitowa tare da bayyana goyon bayansu ga wani ɗan siyasa ko jam'iyya ba.
To amma sannu a hankan na hakan na neman sauyawa, domin kuwa a ƙarshen makon da ya gabata ne wata haɗakar ƙungiyoyin malaman addinin Musulunci ta arewacin Najeriya ta gudanar da wani taro a jihar Jigawa tare da bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027.
Haka kuma, a wani lamari da ya ja hankali, fitaccen malamin Musulunci Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce tasiri da martabar Sanata Abdul'aziz Abubakar Yari kaɗai sun isa Tinubu ya samu goyon bayan Arewacin Najeriya tare da tabbatar wa jam'iyyar APC nasara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Waɗannan batutuwa sun haifar da muhawara a tsakanin 'yan Najeriya, inda wasu ke ganin cewa malaman addini suna da 'yancin bayyana ra'ayinsu a matsayin 'yan ƙasa kamar kowa.
Sai dai wasu kuma na ganin cewa irin wannan fito-na-fito na iya jefa shakku kan matsayinsu na masu wa'azi da sulhu ga al'umma.
To amma me ya sa ake ganin malaman addini na ƙara bayyana ra'ayoyinsu a siyasance fiye da yadda aka saba?
Shin canji ne a al'adun siyasar Najeriya, ko kuwa wani sabon salo ne da ya samo asali daga yadda siyasa da addini suka ƙara cuɗanya da juna?
Yaushe Malamai suka fara tsunduma harkokin siyasa a Najeriya
Dr Kabiru Danladi Lawanti malami a tsangayar koyar da aikin jarida a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya ce tun ba yau ba malaman addini suka tsunduma tsamo-tsamo cikin harkokin siyasa, sai dai a baya-bayan nan ne lamarin ya yi ƙamari.
''An fara ganin shigar malaman addini siyasa tun 2003, lokacin da Olusegun Obasanjo ya tsaya takara da Marigari Muhammadu Buhari'', in ji shi.
Malamin jami'ar ya ce a shekarar 2011 lamarin ya ƙara bayyana sosai, inda har ya ce an yi rikicn bayan zaɓen na 2011.
''To amma a shekarar 2015 babu wannan matsalar sosai, saboda wasu dalilai da suka haɗa da haɗakar jam'iyyun hamayya'', kamar yadda ya yi ƙarin bayani.
Sai kuma a 2023 da batun Muslim-Muslim ya bayyana tare da samun karɓuwa a wajen wasu malaman.
Me ya sa malamai suka fara tsoma bakinsu
Dr Lawanti ya ce babban dalilin da ya sa malaman addinin musulunci ke shiga harkokin siyasa shi ne ganin takwarorinsu na Addinin Kirista na bayyana ra'ayinsu a siyasar.
''Idan ka duba a jihar Taraba Rev. Jolly Nyame ya tsaya takarar gwamna har ma ya ci zaɓe'', in ji shi.
''Wannan ya ƙara wa malaman addinin musulunci ƙarfin gwiwa wajen shiga harkokin siyasa''.
Malamin Jami'ar ya kuma ce wani dalilin shi ne kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba su damar shiga siyasa su bayyana ra'ayinsu har ma su tsaya takara.
Ko ya dace malamai su goyi bayan ɗantakara?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Lawanti ya ce a tsarin siyasa irin ta Najeriya bai dace ba malaman addini su shiga cikinta, la'akari da yanayin siyasar ƙasar.
'"Yana da mugun hatsarin gaske, saboda a tsarin siyasar Najeriya ba wanda ya fi ƙarfin a zage shi a ci mutuncinsa'', in ji shi.
Dr Lawanti ya ce duk matsayi da girman malami bai wuce wani ƙaramin yaro ya zage a shafukan sada zumunta ba.
''Duk girman mutum da ƙimarsa mutane za su riƙa fitowa suna zaginsa saboda kawai ya bayyana ra'ayinsu a siyasance'', in ji shi.
Shiekh Sheikh Ahmad Mahmad Gumi, ɗaya daga cikin malaman da ke da wannan ra'ayi, wanda a cewar shigar malaman addini siyasa zai taimaka wajen inganta tare da gyara siyasar ƙasar.
A wata hira da BBC a kwanakin baya, Shehin malamin ya ce gara malamin da ya shiga siyasa da nufin gyarata maimako tsayawa kan buzu ana kiran gyaran.
Sheikh Gumi ya ce tsarin shugabanci, addinin musulunci ne ya zo da shi.
''Yana da kyau malaman addinin su shiga siyasa, saboda ba su da wani abun aibi da yake boye wa mutane'', in ji shi.
Shehin malamin ya ce shigar malamai siyasana daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen tsaftace siyasa Najeriya.
Ya bayar da misali da kasashen Saudiyya da Iran, inda ya ce a Saudiyya sarakunan ƙasar na aiki hannu da hannu da makamai, a ƙasar Iran kuma ya ce malaman ne ma suke tafiyar da siyasar ƙasar.
A nasa ɓangare Dakta Ibrahim Baba Shatambaya malami a sashen kimiyyar nazarin siyasa ta Jami'ar Danfodiyo da ke Sokoto, kuma mai nazari kan harkokin siyasar Najeriya ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa dama ciki har da malamai domin su shiga harkokin siyasa.
''Kamar yadda kowane ɗankasa ke da haƙƙi haka su ma malamai, musamman idan malaman za su aiwatar abin da suke yawan kiraye-kiraye a kan mumbarinsu'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa malamai mutane ne da ake yi wa kallon tsaron Allah, masu son ci gaba, masu son yin adalci, to idan suka shiga siyasa suka aiwatar da duk wannan, to ba shakka siyasar ƙasar za ta inganta.
''Matsalar da za a samu shi ne idan sun shiga siyasar sun cire rigar malunta sun saka riga gurɓatatun ƴansiyasa, to nan ne shigar malamai ke da matsala'', in ji malamin jami'ar.











