KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa daga 17 zuwa 23 Agusta

Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni ne daga sassan duniya, kasuwar musayar 'yan wasa da kuma manyan sauye-sauyen da ke faruwa a fagen

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Vicario zai tafi wasan aro daga Tottenham zuwa Juventus

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta amince da tayin aro daga Juventus kan mai tsaron raga Guglielmo Vicario, wanda ya haɗa da zabin saye na dindindin.

    Dan wasan kasar Italiya mai shekaru 29 zai yi tafiya zuwa Turin domin kammala komawarsa Serie A, inda yarjejeniyar ta kunshi zabin sayensa kan fam miliyan 8.6, amma ba wajibi ba ne a aiwatar da sayen.

    Wannan na zuwa ne bayan yunƙurin Juventus na daukar mai tsaron ragar Aston Villa, Emiliano Martinez, ya rushe, yayin da Aston Villa ke dab da kammala daukar mai tsaron ragar Parma, Zion Suzuki.

    An san cewa Martinez yana fama da rauni a ɗan yatsansa, kuma a halin yanzu ba ya cikin yanayin da zai iya buga wasa.

    A gefe guda kuma, Vicario ya rasa matsayinsa a cikin tawagar Spurs a karkashin koci Roberto de Zerbi, wanda ya bai wa mataimakinsa Antonin Kinsky damar zama zabin farko a ragar kungiyar a kakar da ta gabata.

    De Zerbi ya tabbatar cewa Kinsky zai ci gaba da kasancewa mai tsaron raga na farko da aka fi zaɓa a sabuwar kakar, yayin da Burnley ta ɗauki Martin Dubravka kyauta a watan Yuli domin maye gurbin mai tsaron raga.

    A tarihin kungiyar ta Arewacin Landan wannan kakar na cikin wadda ta fi kashe kudi cikinta, wanda ya riga ya ɗauki sabbin 'yan wasa shida tare da neman ƙara wasu 'yan wasan gaba guda biyu.

    Haka kuma sun sayar, sun ba da aro ko kuma sun sallami wasu tsoffin 'yan wasa da dama, ciki har da kyaftin Cristian Romero, ɗan wasan Ingila Djed Spence da kuma Yves Bissouma.

    Vicario ya buga wa Spurs wasanni 117 bayan ya koma ƙungiyar daga Empoli kan kuɗi fam miliyan 17.2 a shekarar 2023.

  2. Me yasa magoya bayan Chelsea ke yi wa Enzo ihu?

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan Chelsea sun riƙa yi wa Enzo Fernandez ihu da zagi a ranar da Morgan Rogers ya ci ƙwallo a wasansa na farko da ya buga wa Chelsea, yayin da Chelsea ta doke Real Sociedad da ci 3-1.

    Joao Pedro shi ma ya ci gaba da nuna ƙwazon da yake yi a wasannin share fagen shiga kakar wasa, inda ya zura ƙwallaye biyu, yayin da koci Xabi Alonso ya nuna irin tsarin wasan da zai iya amfani da shi a kakar wasa mai zuwa.

    Sai dai abubuwan da suka faru a filin wasa bayan shigowar Fernandez sun nuna rashin jin dadi a kansa, kasa da sa’o’i 24 bayan wa’adin sayer da shi da Chelsea ta sanya wa kanta ya kare.

    Fernandez ya kasance yana son komawa Real Madrid a farkon wannan bazarar, amma kulob din na Spain ya janye sha’awarsa ga ɗan wasan na Argentina.

    Daga baya, wakilansa sun tattauna da Manchester City, amma babu tayin da aka gabatar da zai kai darajar fam miliyan 120 da Chelsea ta sanya masa kafin ƙarfe 5:00 na yamma (BST) ranar Juma’a.

    Wasu daga cikin magoya bayan da suka iso a Stamford Bridge sun yi masa ihu lokacin da aka ambaci sunansa minti 45 kafin a fara wasan.

    Daga baya kuma an sake jin ihu lokacin da Fernandez ya shiga wasa a minti na 62.

    An ga cewa magoya bayan Chelsea sun rabu gida biyu kan lamarin, domin yayin da wasu ke yi masa ihu, wasu kuma suna rera sunansa suna nuna goyon baya.

  3. Mun fi ƙoƙari idan duniya na adawa da mu - Dan Burn

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan Burn ya yi 'yan watanni kaɗan ne ba tare da zuwa filin atisayen Newcastle United ba.

    Sai dai ɗan wasan bayan na Ingila ya ji kamar ya shiga sabuwar ƙungiya ne gaba ɗaya lokacin da ya dawo bayan hutunsa na bayan gasar Kofin Duniya.

    Ya ce: "A gaskiya, har yanzu ina koyon sunayen mutane." Ba abin mamaki ba ne ya faɗi haka.

    An sake fuskantar tsaka mai wuya saboda sauye-sauye a Newcastle, bayan tafiyar koci Eddie Howe da kuma wasu manyan jiga-jigan ƙungiyar kamar Bruno Guimaraes, Sandro Tonali da Anthony Gordon.

    Sabon babban koci, Matthias Jaissle, ya zo tare da kusan ma’aikata shida daga tawagarsa, yayin da Burn ma yake ƙoƙarin sabawa da sabbin abokan wasansa da suka haɗa da Lukas Hornicek, Ewen Jaouen, Aladji Bamba, Sean Steur da Bazoumana Toure.

    Baya ga haka kuma, ana sa ran ɗan wasan bayan dama Amar Dedic zai iso daga Benfica nan ba da daɗewa ba.

    Duk da haka, maimakon ya yarda da hasashen wasu masana da ke ganin Newcastle za ta sha wahala a wannan kakar wasa, Burn ya sa gaba ne ya jagoranci ƙungiyar ta koma gasar Turai a matsayin sabon kyaftin ɗinta.

    Ya ce bayan Newcastle ta yi kunnen doki 1-1 da Strasbourg a wasan sada zumunta na ƙarshe kafin fara kakar wasa: "A koyaushe muna taka rawar gani a matsayin ƙungiya idan muna da wannan tunanin cewa mu ne ke fafatawa da kowa a duniya."

  4. Barcelona za ta biya £65m kuɗin Rodri daga Man City

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ta amince da yarjejeniya domin daukar kyaftin din tawagar Spain, Rodri, daga Manchester City kan kusan fam miliyan 65.

    Dan wasan mai shekaru 30, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or a shekarar 2024, ana sa ran zai sanya hannu kan kwangilar shekaru hudu da zakarun Spain.

    Ana sa ran za a kammala cinikin a cikin kwanaki masu zuwa.

    Rodri ya buga wasanni 298 a tsawon shekaru bakwai masu cike da kofuna a Manchester City bayan ya koma kungiyar daga Atletico Madrid a shekarar 2019 kan kudi fam miliyan 62.8, wanda a wancan lokacin ya kasance mafi tsada da kungiyar ta taba dauka.

    Bai buga yawancin wasannin kakar 2024-25 sakamakon raunin da ya ji a gwiwa, ka zalika wasu wasannin kakar 2025/26 ma haka suka kasance masa.

    Sai dai ya dawo kan ganiyarsa ne a gasar Kofin Duniya da aka yi a lokacin bazara, inda ya jagoranci Spain zuwa lashe gasar karo na biyu tare da samun lambar yabo ta Mafi Kyawun Dan Wasa a Gasar.

    Rodri zai bar Manchester City da tarihin lashe manyan kofuna 12, ciki har da kofunan Premier League hudu, FA Cup biyu, EFL Cup uku, da kuma Champions League a kakar 2022-23.

    A makon da ya gabata, Manchester City ta yi watsi da tayin farko na Barcelona na fam miliyan 38.5 kan Rodri, wanda kwangilarsa a filin wasa na Etihad za ta shiga shekararta ta karshe.

    Da farko dai an yi hasashen cewa Real Madrid ce za ta zama kungiyarsa ta gaba, amma Barcelona ta kara ƙaimi wajen kammala sayen dan wasan a kwanakin baya-bayan nan.

  5. Muhammad Buhari Fagge ke fatan kasancewa da ku a wannan mako domin kawo muku labarai da rahotannin wasanni.

    Za mu kawo bayanai kan kasuwar saye da sayerwar 'yan wasan nahiyar Turai.

    Bayanai kan gasannin Turai da za a fara da wadanda aka ma fara a ƙarshen makon jiya.

    Sharhi kan wasu abubuwa da za su shige duhu ga wadanda ba su bibiyar wasanni yadda ya kamata da dai sauransu.

    Ku kasance da mu.