NFF ta nada Salisu Yusuf sabon kocin Super Eagles ta gida

Asalin hoton, NFF Twitter
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta sanar da nada Salisu Yusuf a matakin sabon kociyan Super Eagles ta gida da ke buga gasar CHAN.
Haka kuma zai ja ragamar tawagar matasan kasar ta 'yan kasa da sheka 23 da ke buga wasannin Olympics.
Yusuf ya taba jan ragamar Super Eagles B a gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasa da ke taka leda a gida a Morocco, inda Najeriya ta yi ta biyu a 2018.
Kamar yadda NFF ta sanar a shafinta a Intanet ranar Alhamis ta ce zai yi aiki tare da Kennedy Boboye da Fatai Osho da Abubakar Bala Mohammed da kuma Fidelis Ikechukwu a matakin mataimaka.
Shi kuwa Eboboritse Uwejamomere zai yi aiki a matsayin mai tantance yadda wasa ke gudana wato Match Analyst, yayin da aka nada Ike Shorounmu da kuma Suleiman Shuaibu a matakin kociyan masu tsaron raga.
Haka kuma NFF ta ce nan gaba kadan za ta sanar da sabon kociyan babbar Super Eagles da zarar ta cimma yarjejjeni da shi, sannan ta gabatar da shi.
Hukumar kwallon kafar Najeriya ta rusa masu horar da Super Eaglees karkashin jagorancin Augustine Eguavoen, bayan da ya kasa kai kasar gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a bana - Ghana ce ta yi nasara a kan Najeriya da ci 2-1, bayan da suka tashi 0-0 a Ghana.
Sauran nade-nade da NFF ta yi a ranar Alhamis, Ladan Bosso zai ci gaba da aikinsa na jan ragamar U20 ta maza.
Zai yi aiki tare da tsohon kociyan matasan Najeriya U17 Fatai Amao, sai wadanda za su taimaka masa da suka hada da Oladuni Oyekale da Jolomi Atune Alli da kuma Baruwa Olatunji Abideen a matsayin mai horar da masu tsaron raga.
Shi kuwa Nduka Ugbade zai horar da matasa 'yan kasa da shekara 17, wanda zai yi tare da taimakon Ahmad Lawal Dankoli da Omoniyi Haruna Ilerika da Yemi Daniel da kuma Mohammed Nasiru Isah kociyan masu tsaron raga.
Ugbade ya yi kyaftin din tawagar Najeriya ta matasa 'yan kasa da shekara 16 da ta fara lashe kofin duniya a China a 1985.
Haka kuma Future Eagles ta matasa 'yan kasa da shekara 13 da 'yan 15 za ta samu jagorancin Patrick Bassey will be Head Coach and will work with Abdullahi Tyabo Umar da Mohammed Kalli Kachalla da Ifeanyi Uba da Alh. Mohammed Kwairanga, yayin da Abubakar Abdullahi zai horar da masu tsaron raga.











