Yusuf zai jagoranci Enugu Rangers a kofin kalubale

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafar Najeriya, NFF, ta sa Salisu Yusuf ya jagoranci kungiyar wasa ta Enugu Rangers a gasar cin kofin kalubale na Afirka.
Salisu mai shekara 57 zai jagoranci Enugu Rangers din ne tare da ci gaba da kasancewa mataimakin kocin Super Eagles ta Najeriya.
"Na zo nan daga hukumar kwallon kafa ta kasa domin bayar da shawarwari kasancewar Rangers za ta wakilci Najeriya a gasar nahiyar Afirka," in ji Yusuf.
"Muna bukatar mu sauya wasu abubuwa amma za a yi hakan ne sannu-sannu."
Wasan da Rangers za ta fara takawa karkashin jagorancn Yusuf shi ne wanda za ta fafata da Masar ranar Lahadi.
Enugu Rangers za ta sake fuskantar kungiyar wasa ta Nouadhibou ta kasar Mauritania sannan ta sake gamuwa da Al Masry ta Misra.
Salisu Yusuf wanda ya maye gurbin Benedict Ugwu wanda aka kora, na da kalubalen dawo wa da Rangers kimarta da ta zube inda ta yi nasara daya kacal a wasanni biyar.
Ana ganin kuma Salisu zai iya amfani da damar wajen sake gina kimarsa da ta zube sakamakon haramta masa harkokin wasanni na shekara daya da Fifa ta yi saboda karbar rashawa.
Yusuf wanda tsohon dan wasan tsakiya na El Kanemi da Ranchers Bees ne na da gogewa a matsayin kocin kwallon kafa ta shekar 15.
Ya jagoranci kungiyar Kano Pillars lokacin da ta kai gaci a gasar Premier Najeriya ta 2008 da kuma Enyimba a 2013.











