Dabbobi 10 mafiya muni a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Kallon dabbobi musamman ma na daji abu ne mai samar da nishaɗi da ban-sha'awa, wanda hakan ya sa masu hali kan shiga dazuka domin kallon su da irin ɗabi'unsu.
Sai dai ba kowace dabba ce take da daɗin kallo ba.
Za a iya cewa 'ba su da daɗin kallo' ko kuma suna da muni, amma dai duk da haka suna da nasu ɗabi'un na burgewa.
Akwai halittu da dama a dazuka da kuma cikin ruwan teku ko tafkuna waɗanda za mu iya cewa halittarsu ta yi matuƙar shan bamban da waɗanda muka saba gani.
Mutane da dama na son kallon dabbobin daji masu siffa irin ta yaran bil'adama - kamar manyan idanu, ƙaramin hanci da fuska mai siffar da'ira, hakan na faruwa ne saboda yadda yara ke burge mu.
To amma hakan na yin tasiri kan yadda muke kallon dabbobi.
Ga jerin wasu dabbobi waɗanda siffarsu ba su cika burge ɗan'adam ba:
Madagascar Aye-aye

Asalin hoton, Nomis Simon/Wikipedia Commons
Dabbar tana da dogayen yatsu, da gashi mai fari da baƙi, haƙoranta kamar na ɓera sannan idanunta dara-dara, waɗannan kamanni ne daban da dabbar aye-aye take da su.
Dabbar ana samun ta ne a tsibirin Madagascar da ke nahiyar Afirka. Aye-aye na ƙwaƙular bishiya ne domin neman ƙwarin da take kalaci da su.
Sai dai wani abin damuwa shi ne yanzu haka dabbar na cikin waɗanda ke fuskantar barazanar ƙarewa a doron ƙasa kasancewar ana lalata dazukan da take samun mafaka.
Haka nan kuma wasu na farautar ta bisa wasu camfe-camfe, kan cewa dabbar wata alama ce ta mutuwa ko kuma faruwar mummunan abu.
A baya an yi tunanin cewa dabbar ta ƙare a duniya, kafin daga baya a shekarar 1957 aka sake ganin ta.
Yanzu akwai wasu dokoki da aka gindaya domin kare ta.
Biri mai dogon hanci

Asalin hoton, /Wikipedia Commons
Birran Proboscis na daga cikin birrai waɗanda kamanninsu suka sha bamban da saura, ba kawai saboda dogon hancinsa ba wanda ke iya kaiwa tsawon santimita 17 (inci 7).
Yana kuma da jan gashi a kansa da kuma jiki mai launin ruwan ƙasa yayin da ƙafafunsa ke da gashi mai launin ruwan toka.
Irin wannan nau'in birran sun kuma ƙware wajen iyo a ruwa kasancewar suna da ƙafa kamar ta agwagwa, lamarin da ya sanya sukan iya tsere wa kada a ruwa.
Sai dai cikin irin wannan birin yana yawan motsi a lokacin da yake niƙe abinci, wani abu da ya sanya yake yawan yin gyatsa.
Mazan birin Proboscis sun fi matan tsawon hanci, kuma girman hanci na ƙara wa maza samun karɓuwa wajen mata.
Ƙaton hanci na nufin namijin yana da ƙarfi da lafiya, kuma zai samu mata cikin sauri.
Ɓeran rami maras gashi

Asalin hoton, Getty Images
Fatar wannan nau'in ɓeran a tattakure take sannan yana da haƙora masu launin ɗorawa, wanda hakan ya sanya ba lallai ne a ce yana da kyau ba.
Sai dai idan ka ce za ka ƙaurace ma wannan ɓera saboda muninsa kawai, ba za ka san sauran kyawawan abubuwan da ke tattare da shi ba.
Misali, yana da wahala irin wannan nau'in ɓera ya kamu da cutar kansa a lokacin da yake tsufa, ba kamar sauran ɓeraye ba.
Hakan na faruwa ne saboda bugawar zuciyarsa a hankali da kuma halittar ɓeran, inda yake iya rage saurin sarrafa abinci a cikin cikinsa a lokacin da yake cikin halin matsi.
Haka nan ɓeran ba ya buƙatar shan ruwa, domin ruwan da ke cikin abincin da yake ci ya wadace shi.
Kifin Blobfish

Asalin hoton, Robert Zugaro/Museums Victoria
Wannan kifi na rayuwa ne a yankin teku mai matuƙar duhu, wurin da ya kai zurfin tsakanin mita 600 zuwa 1,200, wanda hakan ke nufin yana da jiki da kuma ƙashi mai matuƙar laushi.
Hakan na nufin idan aka fitar da shi daga ruwa jikinsa zai langwaɓe ba kamar idan yana cikin ruwa ba.
Kifin Goblin shark

Asalin hoton, Getty Images
Kifin goblin shark ƙalilan ne ke rayuwa a duniya kuma sun samo asali ne sama da shekaru miliyan 125 da suka gabata.
Hancinsa na da tsawo sosai kuma haƙoransa na da matuƙar ƙarfi, sannan yana iya ƙara tsawon hancinsa a lokacin da yake farauta.
A wasu lokutan yakan iya amfanin da leɓɓansa wajen rufe haƙoransa masu tsananin kaifi.
An fi samun irin wannan kifi ne a gaɓar ruwan Japan, duk da cewa an taɓa ganin shi a tekuna daban-daban a faɗin duniya.
Yana da matuƙar wahala a gan shi kasancewar yana rayuwa ne a can ƙasan teku, inda zurfin ya kai daga mita 100 zuwa 1,300.
Goblin shark na daga cikin dabbobin da ke fuskantar haɗarin ƙarewa.
Kwaɗo mai launin shanshanbale

Asalin hoton, Alamy
Purple frog, kamar yadda ake kiran shi a Ingilishi ko kuma kwaɗo mai hancin alade na da ƙatoton baya.
Ƙirar jikinsa na ba shi damar iya ginan ƙasa domin samar da ramin da kusan kodayaushe yake rayuwa a ciki.
Ba kamar sauran kwaɗi ba, purple frog na amfani da ƙafafunsa masu ƙarfi ne wajen ginar rami, ba domin tsalle ba.
Kasancewar yana rayuwa ne a ƙarƙashin ƙasa shi ya sa ba ya buƙatar manyan idanu domin ganin abubuwa, shi ya sa yake da ƙananan idanu, kuma dogon hancinsa na taimaka masa wajen tafiya a ƙarƙashin ƙasa da kuma kama cinnaku waɗanda su ne abincinsa.
Mazan irin wannan kwaɗi na da wani kuka da suke yi idan suka hauro saman ƙasa domin neman matan da za su yi barbara.
Duk da cewa an gano wannan nau'i na kwaɗi ne a shekarar 2003, yawansu ya yi ƙasa sosai, wanda hakan ya sanya suke cikin halittun da ke cikin haɗarin ƙarewa.
Aladen daji

Asalin hoton, Getty Images
Wannan dabbar ba za ta taɓa shiga gasar kyau ta dabbobin duniya ba, amma wannan ƙahon da ke bakinta na kare ta daga miyagu.
Duk da wannan ƙaho da take da shi wanda mugun makami ne, amma shi kansa aladen ba mugu ba ne, kuma yana rayuwa ne ta hanyar cin ƙwari da ƴaƴan itace.
Wannan dabba na rayuwa ne a dajin wasu ƙasashen Afirka, kuma yana fuskantar matsin lamba daga zakuna da damisa har ma da dan'adam.
Sai dai yana da ɗan karen gudu, inda yake iya fecewa a gudun kilomita 48 cikin awa ɗaya, wanda hakan yake da amfani sosai gare shi wajen tsere wa magauta.
Biri mai sanƙo

Asalin hoton, Getty Images
Wannan biri ne mai jar fuska. Yana da ƙaramin jiki kuma yana rayuwa ne a dajin da ke kusa da rafin Amazon, manyan siffofinsa su ne jar fuska, sanƙo da dogon gashi.
Jar fuskarsa wata alama ce ta ƙoshin lafiya.
Sai dai sanƙonsa na sanay shi ya kamu da cutar maleriya da wuri, wanda hakan kan sanya fuskarsa ta koma fari-fari.
An lissafa wannan biri cikin dabbobin da ke fuskantar barazanar ƙarewa sanadiyyar sare dazuka.
Ƙurungun jemage

Asalin hoton, Dr Sarah Olson/WCS
Wannan jemage da ake kira Hypsignathus shi ne jemage mafi girma a Afirka, kuma na uku mafi girma a duniya.
Namijin wannan jemage ya fi mace girma, kuma kansa ya fi girma fiye da na macen.
Haka nan namijin yana da wata irin ƙara maras dadi wanda yake amfani da ita wajen neman mace domin barbara.
Irin wannan jemagu na rayuwa ne ta hanyar cin ƴaƴan itace da ƙwari a wurare dazuka masu duhu.
Kada mai kalar kunkuru

Asalin hoton, Getty Images
Kasancewar tana da fata mai tsini-tsini da goshi mai tsini da wata ƙugiya a baki, wannan dabba na kama da kada.
Ana samun ta ne a rafukan da ke Amurka kuma tana da haƙora masu ƙarfin gaske da take amfani da su wajen cin kifaye da ƙananan halittu, inda take amfani da harshenta wajen kama abin farauta.
Ita ma wannan dabba na cikin wadanda ke fuskantar barazanar ƙarewa sanadiyyar raguwar yawanta dalilin masu farauta da kuma rashin kyakkyawan muhalli.










