Man City ta yi wasa 27 ba a doke ta ba har da cin 20 a jere

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta yi wasa 27 ba tare da an doke ta ba, ciki har da cin wasa 20 a jere a dukkan fafatawa a bana.
Rabon da a yi nasara a kan City tun ranar 21 ga watan Nuwamba, wanda Tottenham ta doke kungiyar ta Etihad.
Ranar Asabar City ta doke West Ham United da ci 2-1 a wasan mako na 26 a Premier League, kuma shi ne karo na 20 da kungiyar ta jera tana cin wasanni a dukkan karawa a bana.
Cikin wadannan nasarar har da cin wasan Premier League karo 14 da na Champions League daya ta kuma yi nasarori a FA Cup da kuma a gasar Carabao Cup..
City ta bai wa ta biyu tazarar maki 13 tun ranar Asabar wato Manchester United wadda za ta fafata da Chelsea ranar Lahadi.
Kungiyar ta Etihad ta kai wasan karshe a Carbao Cup da Quarter finals a FA, za ta karbi bakuncin Borussia Monchengladbach a wasa na biyu a Champions League a Ingila.
Karawar farko da suka yi a gasar ta Zakarun Turai, City ce ta doke Monchengladbach da ci 2-0 a makon jiya.
Tun farko City ta tsara yadda za ta samu wadannan nasarorin, inda ta sayo masu tsaron baya cikin shekaru shida baya har da Ruben Dias, wanda ya zama kashin bayan kungiyar.
Kwallo 11 ne ya shiga ragar City a wasa takwas farkon kakar bana, sai dai kuma guda biyar ne ya shiga ragar kungiyar a karawa 18 da ta kara yi.
A kakar bana City na fatan cin kofi hudu da ya hada da na Premier League da FA Cup da Caraboa da Champions League.
Daga nan kuma ta yi harin UEFA Super Cup da kofin zakarun nahiyoyin duniya wato Fifa Club World Cup, amma idan ta lashe Champions League na bana kenan.











