Pogba zai ci gaba da jinya har bayan watan Fabrairu

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ole Gunnar Solskjaer ya tabbatar cewar Paul Pogba zai ci gaba da jinya har bayan watan Fabrairu, ba zai buga wa kungiyar wasa da Real Sociedad ba.

Wasu 'yan wasan da ba za su yi wa United gasar zakarun Turai ta Europa League ranar Alhamis ba sun hada da Donny Van De Beek da kuma Edinson Cavani.

United za ta ci gaba da buga Europa League wasannin kungiyoyi 32, bayan da ta yi ta uku a Champions League a bana.

Kungiyar ta Old Trafford za ta buga karawar a Turin wato filin Juventus maimakon San Sebastian, bayan da Spaniya ta sa dokar hana shiga kasarta don gudun yada cutar korona.

Pogba dan kwallon tawagar Faransa wanda ya koma kan ganiya a fagen taka leda a bana a yi rauni ne ranar 6 ga watan Fabrairu a wasan da United ta tashi 3-3 da Everton a gasar Premier League.

Kawo yanzu Pogba ba zai buga wasan da United za ta kara da Sociedad a Italiya da wanda za su fafata a Old Trafford ba a gasar ta Europa League.

Haka kuma dan kwallon ba zai yi wa United wasan da za ta yi gumurzu da Newcastle United da kuma Chelsea, watakila ba zai je Etihad wasan hamayya da City ba.