Man City ta sha kash da ci 5-2 a hannun Leicester a gasar Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Jamie Vardy ne ya ci kwallo uku daga 5-2 da Leicester City ta caskara Manchester City ta kuma dare mataki na daya a teburin Premier League.
Duk da cewar minti hudu da fara kwallo Riyad Mahrez ya ci wa City, ba a samu dogon lokaci ba, Leicester ta mayar da martani.
Vardy ne ya farke kwallo a bugun fenariti tun kan hutu daga baya ya kara biyu suka zama uku rigis kuma karo na biyu da ya yi wa City irin wannan yankan kaunar.
James Madison ne ya ci wa Leicester City kwallo na hudu kuma karon farko da ya zura a raga tun 1 ga watan Janairu.
Sabon dan wasan City, Ake ya zare kwallo daya shi ma na farko da ya ci wa kungiyar tun da ya koma kungiyar daga Bournemouth a bana kan fam miliyan 40.
Daga karshe Leicester City ta samu fenariti na uku a wasan kuma Youri Tielemans ya buga, bayan da an riga an canji Vardy a karawar.
Wannan ne karon farko da Leicester City ta ci wasan farko uku a jere na Premier League a tarihin kungiyar.
Haka kuma Pep Guardiola ya ci karo da wasa mafi muni da aka casa shi a Etihad a matsayin kocin Kungiya da yanzu take tsakiyar teburin gasar bana.











