Ilkay Gundogan: Ɗan wasan Manchester City ya kamu da cutar korona

Ilkay Gundogan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ilkay Gundogan ya buga wa Manchester City tamaula a Gasar Zakarun Turai a watan Agusta
An wallafa

Ɗan wasan tsakiyar Manchester City Ilkay Gundogan ya kamu da cutar korona.

Ƙungiyar da ke buga gasar Premier ta tabbatar da cewa ɗan wasan mai shekara 29 ya killace kansa tsawon kwana 10.

Hakan ya sa ɗan wasan na Jamus ba zai buga wasan farko na gasar Premier da City za ta fafata da Wolves a yau Litinin.

"Kowa da kowa a wannan ƙungiya yana yi wa Ilkay fatan samun sauƙi cikin gaggawa," a cewar sanarwar da Manchester City ta fitar.

A baya ƴan wasan City Riyad Mahrez da Aymeric Laporte sun kamu da cutar korona amma sun warke har ma sun koma atisaye.

Ƙungiyar za ta fafata da Bournemouth a gasar cin Kofin Carabao ranar Alhamis sanna za ta gwabza da Leicester City a gasar Premier ranar Lahadi.