David Silva: Ta yaya Man City za ta iya maye gurbin dan wasan mai basira?

Phil Foden da Ilkay Gundogan da David Silva da Kevin de Bruyne da kuma Bernardo Silva

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Barin David Silva tsakiyar Man City babban abu ne amma tana da 'yan wasa masu basira da yawa
    • Marubuci, Daga Phil Dawkes
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • An wallafa

A 2010, David Silva ya dira Manchester City, tare da sanya wata hula doguwa da kwalbar barasa (champagne) bayan kammala murnar lashe kofin duniya. Amma barin kungiyar a yanzu bayan kwashe shekara 10 ya bar City da wani wagegen gibi.

Zamansa na sama da shekara 10, ya samar wa da kungiyar wata nutsuwa a tsakiyarta tare da taimakawa wajen kawo karshen shekara 34 da ta kwashe ba tare da kofi ba, tare da lashe wasu manyan kofina 11.

Yanzu za su fuskanci wasannin gaba babu shi tare da fadawa wata tsaka mai wuya a yanzu - ta yaya za a maye gurbin wanda babu mai maye gurbinsa?

'Gwani', 'na musamman', 'dan baiwa'

Abokan wasa da 'yan hamayya da magoya baya da kuma masu sharhi na ta tururuwar bayyana kwarewar da Silva ya nuna a wasansa na karshe a Premier.

Tsohon kyaftin din Ingila Alan Shearer ya shaida wa BBC cewa Silva ya cancanci a rika tunawa da shi a matsayin "daya daga cikin manyan 'yan kwallon Premier da ba 'yan kasar Ingila ba a tarihi da Thierry Henry da Eric Cantona da kuma Sergio Aguerp".

"Za ka iya jayayya kan cewa ya ma fi dukkansu wadannan da na lissafa," domin za a sanya shi cikin tarihin wadanda suka fi cin kwallo a Premier.

Kocin City Pep Guardiola - babu wani bako da zai iya rike manyan 'yan kwallon kafar duniya kamarsa - yana cewa Silva "na daga cikin manyan 'yan kwallon duniya da ya taba gani".

Tare da Joe Hart da Vicent Kompany da Yaya Toure da kuma Sergio Aguero, ya matukar taimakawa kan nasarar da kungiyar ta samu wadda ba a taba zato ba.

Alkaluman kokarin da ya yi cikin shekara 10 sun tabbatar da hakan.

Sama da shekara 10, ya bayar da kwallon da za a iya ci sama da kowanne dan wasa a Premier.

Tabbas, ya buga wasa da yawa sama da duka sa'anninsa, duka damarmakin da ya samar na cin kwallo 793 sun haura na kowanne dan wasa fiye da sau 200, sai tsohon dan wasan gaban Chelsea Eden Hazard (595) da ke biye masa.

Duka kwallayen da ya bayar aka ci 93 sun ninka na abokan kwallonsa sau 30, yayin da takwaransa na kungiyar Kevin de Bruyne na da (66).

Lokacin da City ta dauko Silva daga Valencia a iya cewa dan wasan gefe ne. Amma yana buga kusan ko'ina karkashin mai koyarwa Roberto Mancini da Manuel Pellegrini, kuma suka mayar da shi kamar lamba 10 wanda hakan ya zamar masa alkhairi.

Amma a salon kwallon Guardiola na 4-1-4-1 da na 4-3-3 yana buga tsakiya ne, kawai dai lamba takwas yake bugawa - wani aiki ne da yake matukar bukatar taimakawa 'yan baya.

Wannan ba karamin aiki ba ne idan muka kalli tasawirar wasansa na karshe a City.

David Silva - ya mamaye ko ina a wasansa na karshe bayan shekara 10

Asalin hoton, Opta

Bayanan hoto, Wannan yana nuna yadda Silva ya taba kwallo kusan a ko'ina cikin rabin filin wasan - wata mahaɗa tsakanin baya da tsakiya da kuma sauran bangarorin da ke filin

Damarmakin da ya samar a 2019-20 ta kai kashi 8.9 cikin 100 a kungiyar a duka kakar - wadda wannan ne taimakon da ya bayar mafi karanci a zamansa na Ingila.

Ya yi gaba kuma dole City ta nemi mafita.

Matsashi 'mai salon Iniesta'?

Phil Foden ne ke sauya David Silva a wani kokarin Pep Guardiola na cike gibin Silva

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Phil Foden yana kara buga wasanni kowacce kaka tun lokacin da ya fara buga wasa a Premier a 2017

Duk da rikicinta da Uefa kan dokar kashe kudade, City na da kudi sama da wasu kungiyoyin da ke yunkurin daukar Silva.

Hakan ya jefa kungiyar rikici amma Guardiola a watan Yuni ya ce: "Yayin da David ya shiga shekararsa ta karshe, na fada wa shugabannin kungiyar Phil Foden, ba sai mun kashe kudi ba."

A wani kokari na ganin ta ƙara ƙarfafa kungiyar ta wani bangaren - tuni suka kawo dan baya Nathan Ake kan kudi fan miliyan 41 tare da dan wasan gefe Farren Torres daga Valencia, kuma nan gaba kadan za a fara neman magajin dan wasan gaban kungiyar Aguero.

Duk da kokarin da ya yi a wasan kofin duniya na 'yan kasa da shekara 17 a 2017 da kuma kwallon da ya ci wadda ta ba da mamaki, dole ne Foden ya jira lokacin da zai samu wuri na dindindin a City.

Ya yi matukar kokari a kakar wasanni ta 2019-20, inda ya ci kwallo biyar ya kuma ba da tara aka ci wanda hakan ke nuna yana bukatar karin lokaci a kakar wasanni ta gaba.

Kuma Foden ba kamar Silva yake ba, don haka ba zai iya maye gurbin dan wasan ba, ko hakan zai faru ba nan take ba.

"Foden na da duk abin da ake bukata a wajen dan kwallo, zai iya zama duk abin da yake son zama, amma ba zai iya maye gurbin Silva ba," in ji tsohon dan wasan kungiyar Micah Ricard.

TAswirar kokarin Phil Foden a gasar Premier 2019-20 a wasannin da aka fara da shi

Asalin hoton, Opta

Bayanan hoto, Taswirar kokarin Foden kenan a wasa tara na Premier da aka fara da shi a 2019 tare da taimakon da ya bayar aka tara maki

Guardiola ya ce "muna da Phil Foden" ba yana nufin zai maye wurin Silva ba ne kai-tsaye a 'yan wasa 11 na farko, amma dai da bukatar matashin ya kara kokari.

A gefe guda kuma akwai 'yan wasa masu matuƙar kwarewa kamar Ilkay Gundogan da kuma Bernardo Silva wanda duka sun fi Foden ƙoƙari a tsakiya tare da De Bruyne wanda shi ne asalin magajin Silva da zai iya hawa karagar mulkinsa.

Sauya fasali ba ruguza kunya ba

"Abin da zai iya taimaka musu shi ne, ba kowane mako Silva yake buga wasa ba," in ji Danny Murphy tsohon dan wasan Ingila. sukan kawo sauyi a kungiyar a tsakiya, don haka ba wai sun gina kungiyar ba ne a kansa.

"Akan samu sauyi a babbar tawagar kungiya lokaci zuwa loaci, don haka dole a koyi kawo sauyi."

Lokacin hutun kirsimeti sau daya aka fara wasa da David Silva cikin wasa shida da ya buga, sauran duka Barnardo Silva ko kuma Gundowan ne ke farawa.

Babu mamaki Guardiola na da kwarin gwiwar saka Bernardo ya buga wasa kusa da De Bruyne a wasannin da ake ganin za su lashe cikin sauki, inda yake son ganin kwallo a mafi yawan lokaci a kafar Gundogan domin bai wa bangaren hagu tsaro a bayan Foden ko kuma a salon wasa na 4-2-3-1 idan ana fafatawa da manyan kungiyoyi.

In ka ga Guardiola ya sanya Barnardo da De Bruyne a wasa, to wanda yake neman zira kwallaye ne nan da nan kuma da yiwuwar ya fi karfin daya kungiyar da ake wasan da ita.

Amma idan aka fara da Gundogan ana bukatar kariya ne, sai a sanya Foden ya rika bin bangaren hagu, lokacin da ake buga salon 4-2-3-1 idan kungiyar da ake wasan da ita mai karfi ce.

Manchester City starting XI options for 2020-21

Asalin hoton, BBC Sport