Donny van de Beek: Man United za ta sayi dan wasan kan fan milliyan 40

getty

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana tsammanin kammala cinikin ne cikin nan da 'yan kwanaki
An wallafa

Manchester United na daf da kammala cinikin dan wasan tsakiya na kungiyar Ajax Donny van de Beek bayan kungiyoiyin biyu sun cimma 'yar jejeniya kan kudi fam miliyan 40.

Kocin United Ole Gunnar Solskjaer ya nuna bukatarsa kan dan wasan na Netherland mai shekara 23, kuma ya ta zuwa kallon wasan shi a lokuta da dama.

Yanzu dai United na jiran yarjejeniyarta da dan wasan ne da kuma likitocin da za su duba lafiyarsa gabanin kammala cinikin.

Ana tsammanin kammala cinikin ne cikin nan da 'yan kwanaki.

Dan wasan dai zai sanya hannu ne kan kwantaragin shekara biyar da kungiyar, wanda hakan zai ba shi damar buga wasan farko na kakar 2020-21 da united za ta buga da Crystal Palace a ranar 19 ga watan Satumba.

Zai zama dan wasa na farko da Solskjaer zai saya bayan kammmala kakar wasanni, tun lokacin da ya nuna aniyarsa ta daukar dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho wanda aka gaza daidai tawa saboda kudi.

Van de Beek na daga cikin tawagar da ta ba da mamaki da suka kai wasan kusa da na karshe na gasar zakarun Turai a 2019.

Ba a sanya shi a wasan sada zumuntar da Ajax ta buga ba da a karshen mako da kungiyar Union Berlin da Eintracht Frankfurt ta kasar Jamus.