Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Wijnaldum, Magalhaes, Dalot, Smalling, Brooks, Maitland-Niles

Asalin hoton, Getty Images
Sabon kocin Barcelona Ronald Koeman yana son dauko dan wasan Liverpool da Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 29, domin kawo shi Nou Camp. (Algemeen Dagblad, via Express)
Dan wasan Lille da Brazil Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, ya jinkirta yanke shawarar karshe kan tafiya Arsenal bayan Manchester United ta soma zawarcinsa. (Telegraph)
Manchester United ta rage burinta na karbo aron dan wasan Juventus da Brazil Douglas Costa, mai shekara 29, kuma yanzu tana duba yiwuwar zawarcin dan wasan Bournemouth da Wales David Brooks, mai shekara 23. (Manchester Evening News)
An gaya wa United cewa dole ta biya Bournemouth £40m idan tana son dauko Brooks. (Sun).
Paris St-Germain tana sanya ido kan dan wasan Manchester United da Portugal Diogo Dalot, mai shekara 21. (O Jogo - in Portuguese)
Dan wasan Manchester United Chris Smalling, mai shekara 30, yana son komawa Roma domin zaman aro bayan ya kwashe kakar wasan da ta wuce a can. (La Gazzetta dello Sport, via Mirror)
Tattaunawa ta yi nisa tsakanin United da golan Ingila Dean Henderson, mai shekara 23, kan sabuwar kwangilarsa. Rahotanni sun ce za a rika biyansa fiye da £100,000 duk mako. (Sky Sports)
Liverpool na duba yiwuwar dauko dan wasan tsakiyar Bayern Munich Thiago Alcantara inda aka ce za a sayar da dan wasan mai shekara 29 dan kasar Sufaniya a kan £30m. (Independent).
Dan wasan Watford Troy Deeney, mai shekara 32, yana son ci gaba da zama a kungiyar, duk da yake an yi waje da su daga gasar Championship. (Talksport)
Tottenham na shirin dauko dan wasan Arsenal Ainsley Maitland-Niles - dan wasan mai shekara 22 ya murza leda a baya da kuma tsakiyar Arsenal a kakar da ta wuce. (Mail)
Dan wasan Brazil Felipe Anderson, mai shekara 27, yana duba yiwuwar barin West Ham. (Sun)











