Pillars ta raba maki da Warri a gasar Firimiya

Nigerian League

Asalin hoton, Npfl

An wallafa

Kano Pillars ta tashi wasa 1-1 da Warri Wolves a wasan mako na 12 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria da suka kara ranar Lahadi a Sani Abacha Kofar Mata Kano.

Tun a minti na biyar da fara tamaula Pillars ta ci kwallo ta kafar Auwalu Ali, sai dai kuma daf da za a tashi daga wasan ne Warri ta farke ta hannun Charles Atsimene.

A ranar Laraba ake sa ran ci gaba da gumurzun mako na 13, inda Pillars za ta ziyarci Abia Warriors.

Wasu sakamakon wasannin da aka yi ranar Lahadi:

  • Lobi 2-0 Sunshine Stars
  • Rivers United 2-0 MFM
  • Plateau Utd 4-0 Enyimba
  • Kwara Utd 2-0 Abia Warriors
  • Nasarawa United 3-2 FC Ifeanyiubah
  • Heartland 2-1 Rangers
  • Dakkada 4-1 Adamawa United
  • Wikki Tourist 1-1 Katsina United

Tun a ranar Asabar Jigawa Golden Stars 0-1 Akwa United