Abu huɗu da za su iya hana ɗorewar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka

.

Asalin hoton, Atta Kenare / AFP via Getty Images

    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, wadda aka cimma a farko-farkon watan Afrilu, yanzu za a iya cewa tana kan gargarar watsewa bayan jerin hare-haren da suka faru a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Amurka Donald Trump da wani babban jami'in Iran sun yi musayar barazana a farkon watan Afrilu, sannan kuma sun sha alwashin ci gaba da ɗaukar matakai kan juna bayan musayar hare-hare.

A ranar Laraba, Amurka ta ce ta kai hari kan na'urorin tattara bayanai na Iran bayan Iran ta kakkaɓo ɗaya daga cikin helikwaftocinta na soji a yankin Gulf.

Dakarun juyin juya hali na Iran na mayar da martani ta hanyar kai hari kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da Jordan, sai dai Kuwait ta ce ta tare wasu hare-haren.

Sake farfaɗowar yaƙin ya zo ne kwanaki bayan Iran ta kai hari da makamai mai linzami kan Isra'ila a ranar Lahadi, lamarin da ya sanya Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare a yammaci da tsakiyar Iran - wanda shi ne karon farko da aka yi musayar wuta kai-tsaye tsakanin angarorin biyu tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

Trump ya buaci angarorin biyu su daina kai wa juna hari.

.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Duk da cewa daga baya ya ce ya dakata, amma da farko shugaban Amurka Donlad Trump ya ce “Iran za ta dandana kudarta”, ba tare da ya yi cikakken bayani ba. Ya ce “an ci galaba kan Iran baki daya” amma tamkar a baki ne kawai.

Hakan na zuwa ne bayan ministan harkokin wajen Iran amAbbas Aragchi ya yi gargadin cewa kasarsa ”za ta mayar da martani kan duk wani hari da aka kai mara”, inda ya ce” Amurka ta sha kashi a filin yaki.”

Ta kai ga cewa kusan dukkanin bangarorin da ke yakar junan sun yi watsi da sharuddan yarjejejiyar, to amma alwai faragabar cewa ci gaba da kaznacewar yaki tsakanin Amurka da Iran zai kai ga rushewar fatar da ake da ita ta cimma dawwamammem zaman lafiya tsakanin kasashen biyu,

To amma me ya sa bangarorin biyu suka gaza martaba yarjejeniyar tsagaita wutar? Ga dalilai hudu da masana suka bayar.

1. Yarjejeniya mai wahala ga Iran

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daya daga cikin dalilan shi ne yarjejeniyar “ba ta warware babban dalilin rikicin ba” a bangaren Iran”, in ji Sina Toossi, babban mai bincike a cibiyar tsare-tsare ta duniya da ke birnin Washington na Amurka.

Ya yi nuni da ci gaban da Isra’ila ta yi wajen ki hare-haren soji kan Levanon, ga kuma matsi na soji da tattalin arziki da Amurka ke ci gaba da yi wa Iran., ciki har da na takunkumai da kuma toshe tashohin jirgin ruwan kasar.

A ranar Talata, Isra’ila ta kai hari kan birnin Tyre na kudancin Lebanon, kwana daya bayan Iran ta bukaci Israila ta daina kai hare-haren.

Tehran na kallon wannan a matsayin wata dabara ta yaki, inda za ta ci gaba da yin wasu abubuwa duk kuwa da ba ta son a sake fantsama cikin yakin sosai - wani abu da shugabannin Iran ke ganin “ba za ta sabu ba,” in ji Toossi.

Ya kara da cewa Iran ta damu cewa idan har Amurka ta ci gaba da kai irin wadannan hare-hare kan kawayen irin din na yankin cikin sauki, to da alama “za ta co gaba da irin hakan”, wani abubda zai zaizaye tasirin Iran a yankin a hankali.

Masana kuma sun ce jagororin Iran na shan matsi ka cewa kada su amince da yarjejeniyar tsagaita wuta wadda za ta bai wa makiyanta dama ta fannin soji da tattalin arziki, yayin da ita kuwa Iran take kaffa-kaffa.

2. Rawar da Isra’ila ke takawa

.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Masana na ganin cewa ayyukan Isra’ila sun kara dagula lamurra a kokarin tabbatar da yarjejeniyar.

“Isra’ila na da sha’awar ganin ba a cimma wata yarjejeniya da za ta bar Iran da sauran tasiri ba a ya ki ‘l in ji Dr H A Hellyer, babban mai bincike a cibiyar binike ta Amurka da ke Birtaniya, i da ya bayyana Isra’ila a matsayin wadda za ta iya dagula lamurra a yunkuri warware matsalar ta diflomasiyya.

”Suna tarwatsa duk wata yarjejeniya - ba kawai don Amurka na kokari ta fannin doflomasiyyar ba, sai dai saboda diflomasiyyar ta Amurka.

Akwai muhawararo kan sau nawa Isra’ila ta kangare wa umarnin Trump, wanda ya gargade ta kan kada ta kai wa Iran hari a ranar Lahadi.

Sai dai masana harkokin soji na cewa Isra’ila ba dogaro ne kacokan kan taimakon soji daga Amurka a duk lokacin da aka samu wani babban rikici mai tsawo da Iran.

”Babu tantamar cewa Isra’ila ba za ta iya yin yakin nan ita kadai ba”’ in ji Yehoshua Kalisku, babban mai bincike a cibiyar nazarin harkokin tsaro da ke Isra’ila, kamar yadda ya shaida wa kamfanin labarai na Reuters.

Wani masanin tarihin harkokin soji Danny Orbach, babu wata yarjejeniya da za a kulla da Iran da za ta yi watsi da nata bukatun.

“Idan (dum wata yarjejeniyar tsagaita wuta) ta ci karo da manyan bukatun Isra’ila , to Isra’ila za ta tuntsurar da ita”, kamar yadda ya fada a wata tattaunawa da Reuters.

A wara tattaunawa ta wayar tarho da BBC, Trump ya musanta cewa Netanyahu ya binire masa ta hanyar mayar da martani kan hare-haren Iran, sum kuwa da ya nemi a yi taka-tsan.

3. Sake dawo da yaki cikin dabara

Abu na uku shi ne tamkar sake barkewar yakin na cikin dabarun tsagaita witar.

Duk da matsin soji da Isra’ila da Amurka suka rika sanya wa Iran, da takunkumai da datse tashohin ruwa, shugabancin Iran bai jijjiga ba kuma matakan tsaron kasar na nan daram, sannan hargitsin da abokan ganatta suka yi hasashen zai tashi a cikin kasar bai tashi ba.

Masharhanta na ganin cewa wannan da alama wannan ya karfafa juriyar Iran. a maimakon kokarin kauce wa fito na fito, a ya zu kasar za ta ga cewa tana da karfin jure wa duk wata takura - kuma a yanzu za ta iya shata mata sharuddan.

4. Iyakokin karfin Amurka

.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Wani abu ma karshe shi ne rawar da Amurka ke takawa - da kuma irin karfin da take son ta yi amfani da shi.

A matsayinta ta babbar mai taimaka wa Isra’ila ta fannin soji. Amurka na taimaka mata da makamai da kudi da taimakon doflomasiyya, wanda hakan ke dora ta a sama a cikin rikicin.

Hellyer ya ce “idan Amurka na son Isra’ila ta canza, tana da damar yin hakan,” ya kara da cewa rage bai wa Isra’ilantallafinkawai ya isa ya zama darasi gare ta.

”Idan har ta ki yin amfani da wannan danar, to hakan na nifin akwai sanya hannunta. Tana da damar hakan, amma ba ta da niyyar yin hakan.”

Hadarin da ke gaba

Masharhanta na gargadin cewa irin wadannan abubuwa za su iya sanyawa cimma dawwamammem zaman lafiya ta zama mai wahala.

A yanzu mutane da dama na ganin cewa diflomaiyya ce hanya mafi dacewa.

Sai dai Hellyer ya yi gargadin cewa idan “ala ci gaba da amfani da diflomasiyya a matsayin mafakar kaddamar da aikin soji”, Oran za ta iya canza nata tsarin ta hanyar mayar da kai mata hari ya zama mai hadari.