Yadda hare haren ƴan bindiga ke neman hana noma a wasu yankunan Zamfara

Asalin hoton, Social Media
Al'ummomin garuruwa da dama na yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfarar da ke Najeriya, na ci gaba da fama da matsalar hare-haren 'yan bindiga, wadanda ke tattare da sace mutane don neman kudin fansa, da kashe jama'a, da satar dabbobi da sauran kadarori.
Wannan lamari dai na neman hana gudanar da ayyukan gona a daminar bana, sakamakon yadda matsalar tsaron ta yi kamari.
Wannan matsala ta tsaro dai ta hana jama'ar garuruwa fiye da goma na yankin karamar hukumar Zurmi a jihar ta Zamfara sakat, kuma lamarin sai kara munana yake.
Wani mazaunin yankin da BBC ta tattauna da shi ya ce a yanzu suna cikin hali na tashin hankali da fitina.
Ya ce," A yanzu haka bama kwana a gidajenmu a dazuka muke kwana saboda rashin tsaro, 'yan bindigar nan na kawo mana hare hare ba kakkautawa, kuma a duk shigar da suka yi gari sai sun yi ta'asa wato barna, sun kashe mutane, sun kwashe wasu har sai mun bayar da kudin fansa masu yawa,sannan ga wawashe mana dukiya."
" Akwai wata shigowa da 'yan fashin dajin nan suka yi garinmu sai da suka kashe mana mutane sun kusa hamsin, sannan suka tafi da wasu 118 sai da muka bayar da kudin fansa akalla naira miliyan 27, sannan aka sako su.Daga baya kuma suka sake dawowa suka daukar mana mutum 80, sai da muka bayar da kudin fansa naira miliyan 26, sannan aka sako mana su." In ji shi.
Mutumin ya ce, "a kullum wannan matsala kara tabarbarewa ta ke, domin a yanzu akwai kusan garuruwa sun kai 10 ko 11 da babu kowa duk an gudu saboda tsabar hare haren da ake kai wa."
Matsalolin dai sun kai makura, kuma suna ta addabar hanyoyin neman abincin sauran jama'ar da ta rage, in ji mutumin yankin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce, " a gaskiya sun kassara tattalin arzikinmu saboda a yanzu halin da ake ciki shi ne baka da ikon kaje gona ka yi shuka, domin da fita za a harbeka ko kuma a daukeka., don haka mu yanzu babu batun noma a garemu sai dai zaman gida saboda ba tsaro."
"Muna kira ga hukumominmu na jiha da ma na tarayya da su dubi Allah su kawo mana daukin da ya dace ko ma samu kanmu." In ji shi.
To dangane da waɗannan matsaloli na tsaro da kiran da waɗannan jama'a na yankunan da ke fama da tsaro suka yi, sabon kwamishinan ƴan sandan jihar ta Zamfara, Ahmad Muhammad Bello, ya bayar da albishir.
Cikin wata hira da BBC, kwamishinan ya ce," Mun riga mun san matsalar tsaro na damun mutanen jihar Zamfara daga kowane bangare, to yanzu haka akwai wuraren da muka fara aiki, kuma al.'ummar Zurmi, in sha Allah nan da wani lokaci kankani zamu zo gareku mu yi muku abin da ya dace domin dawo da zaman lafiya a yankunanku."
Jihar Zamfara dai ta kwashe shekara fiye da goma tana fama da matsalar tsaro, wadda ke ci gaba da kassara sha'anin zamantakewa da ayyukan gona da sauran harkokin tattalin arzikin jama'a.











