Gwamnonin Najeriya da ke neman kujerar sanata a zaɓen 2027

Sanat

Asalin hoton, Muhammadu Inuwa Yahaya, Dapo Abiodun, Senator Bala Muhammad/FB

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Daga cikin al'adun da suka fara zama ruwan dare a siyasar Najeriya, akwai al'adar komawa majalisar dattawa da gwamnonin ƙasar ke yi domin zama sanatoci, inda wasu ke su daɗe.

Kamar yadda aka saba a duk kakar zaɓe, a wannan karon ma haka abin yake domin tuni wasu gwamnonin sun bayyana sha'awarsu ta yin takarar majalisar ta dattijai.

Yawancin gwamnonin suna wa'adinsu na biyu ne, kuma daga cikinsu akwai waɗanda daga majalisar dattawar suka zama gwamna, yanzu kuma sun gama suke shirye-shiryen komawa majalisar.

Sai dai wasu na ganin gwamnoni sun fara mayar da majalisar dattawa tamkar wajen ritaya, inda ake hasashen nan da wani lokaci majisar za ta zama matattara tsofaffin gwamnoni.

Daga cikin gwamnonin da suke kammala wa'adinsu na biyu akwai na Kwara AbdulRahman AbdulRazaq da Nasarawa Abdullahi Sule da Adamawa Ahmadu Fintiri da Legas Babajide Sanwo-Olu da Borno Babagana Zulum da Bauchi Bala Mohammed da Ogun Dapo Abiodun da Yobe Mai Buni da Gombe Inuwa Yahaya da Oyo Seyi Makinde.

Haka kuma akwai gwamnan Bayelsa Douye Diri da zai kammal wa'adina na biyu a watan Janirun 2028 da kuma Hope Uzodimma na Imo da zai kammala watan Fabrailun 2028 shi ma.

Sai dai Gwamnan Oyo ya ayyana ƙudurinsa ne na tsayawa takarar shugabancin ƙasar, maimako ta sanata.

Dapo Abiodun – Ogun

Ɗaya cikin zaɓukan takarar sanata da suka ɗauki hankali akwai takarar kujerar sanata mai wakiltar Ogun ta Gabas a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Gwamna Dapo Abiodun ya yi nasara a zaɓen fid-da-gwani na jam'iyyar APC, inda ya kayar da sanata mai ci, Gbenga Daniel, wanda shi ma tsohon gwamnan jihar ne.

Nasarar ta nuna ƙarin ƙarfin ikon gwamnan a tsarin siyasar jam'iyyar APC a jihar ta Ogun.

Muhammadu Yahaya - Gombe

Muhammadu Inuwa Yahaya

Asalin hoton, Muhammadu Inuwa Yahaya/FB

Wata fafatawar, wadda take ɗaukar hankali ita ce takarar gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya.

Gwamna Inuwa ya shiga takarar kujerar Sanatan Gombe ta Arewa ne domin fafatawa a babban zaɓe da tsohon gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo na jam'iyyar PDP wanda ke riƙe da kujerar.

Bala Mohammed - Bauchi

Bala Mohammed

Asalin hoton, Bala Mohammed/FB

Gwamna Bala Mohammed ne kaɗai gwamna da ba na jam'iyyar APC ba da ke cikin wannan jerin takara. Shi ma rahotanni sun nuna cewa zai tsaya takara domin neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APM (Allied Peoples Movement) wadda ya koma bayan ficewa daga PDP.

Gwamna Bala ya kasance sanata daga shekarar 2007 zuwa 2010 a ƙarƙashin jam'iyyar ANPP, kafin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya naɗa shi Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT).

Bayan ministan Abujan ne ya zama gwamnan Jihar Bauchi a shekarar 2015 zuwa yanzu da yake ƙarƙare wa'adinsa.

Abdullahi Sule - Nasarawa

Abdullahi Sule ma na cikin gwamnonin da wa'adinsu ke ƙarewa waɗanda ke ƙoƙarin komawa Majalisar Dattawa.

Gwamnan Jihar Nasarawa na neman kujerar Sanatan Nasarawa ta Arewa, wadda a halin yanzu babu mai riƙe da ita sakamakon rasuwar Godiya Akwashiki, wanda ya wakilci yankin har zuwa rasuwarsa a ranar 31 ga Disamba, 2025.

Ahmadu Umaru Fintiri -Adamawa

Shi ma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa yana cikin masu sha'awar takarar kujerar sanata.

Gwamnan zai tsaya takarar Sanatan Adamawa ta Arewa, bayan sanatan mai ci, Amos Yohanna ya janye daga takarar domin ba shi dama.

Mista Yohanna ya sanar da janyewarsa ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Mubi, inda aka miƙa wa Mista Fintiri fom ɗin tsayawa takara na kuɗi Naira miliyan 20.

Mai Mala Buni - Yobe

Shi ma Gwamna Mai Mala Buni ya samun cikakken goyon bayan a jam'iyyar APC a yunƙurinsa na tsakaya takarar sanata.

Sanatan da ke wakiltar Yobe ta Gabas, Musa Mustapha ne ya janye daga neman wa'adi na biyu, sannan ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Buni domin ya nemi kujerar.

AbdulRahman AbdulRazaq - Kwara

AbdulRahman AbdulRazaq

Asalin hoton, AbdulRahman AbdulRazaq/FB

A Jihar Kwara, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya samu goyon baya daga wasu ɓangarorin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC domin neman tikitin takarar Sanatan Kwara ta Tsakiya.

Sanatan mai ci wato Saliu Mustapha ya tsaya takarar gwamnan jihar ne, amma bai samu nasara ba a zaɓen fitar da gwani.

Hope Uzodimma - Imo Duk da cewa wa'adinsa na gwamna bai ƙare ba

A cikin gwamnonin da suke neman takarar sanata, za a iya cewa na Jihar Imo ya fi ɗaukar hankali.

Gwamna Hope Uzodimma zai takarar ne a ƙarƙashin jam'iyyar APC domin neman kujerar Sanatan Imo ta Yamma duk da cewa wa'adinsa na gwamna ba zai ƙare ba sai a watan Fabrairun shekarar 2028.

A baya, Mista Uzodimma ya wakilci Imo ta Yamma a Majalisar Dattawa tsakanin 2011 zuwa 2019 kafin ya zama gwamna a shekarar 2020.

Tsofaffin gwamnoni

  • Adamu Aliero – Jihar Kebbi
  • Aliyu Wamakko – Jihar Sokoto
  • Abdulaziz Yari – Jihar Zamfara
  • Ibrahim Hassan Dankwambo – Jihar Gombe
  • Abubakar Sani Bello – Jihar Neja
  • Simon Lalong – Jihar Filato
  • Godswill Akpabio – Jihar Akwa Ibom
  • Seriake Dickson – Jihar Bayelsa
  • Adams Oshiomhole – Jihar Edo
  • Orji Uzor Kalu – Jihar Abia
  • Yahaya Bell- Tsohon gwamna n