Abin da dokar kafa ƴansandan jihohi a Najeriya ta ƙunsa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A ranar Alhamis ne Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da ƙudurin dokar ƙirƙiro ƴan sandan jihohi.
Ƙudurin zai sa a yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, gyaran fuska, inda za a fitar da tsarin aikin da kuɗaɗen da hukumomin za su kashe da kafa hukumar da za ta sanya ido kansu.
Ƴan majalisa 288 ne suka amince da ƙudurin, yayin da 4 suka ƙi amincewa. Majalisar Dattawa ma ta amince da ƙudurin bayan yi masa karatu na biyu, inda za su kaɗa ƙuri'a a zama na gaba.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya buƙaci majalisun tarayyar guda biyu da su yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima domin samar da tsarin doka da zai bayar da damar kafa 'yansandan jihohi.
Batun samar da ƴansandan jihohin a Najeriya na ci gaba da haifar da cece-ku-ce musamman yadda wasu ke ganin za a yi amfani da jami'an wajen take haƙƙin ɗan adam da kuma dakushe tasirin ƴan sandan tarayya.
To amma me wannan ƙuduri ya ƙunsa da kuma yadda tsarin aikin zai kasance har kwalliya ta biya kuɗin sabulu? Ga abin da BBC ta tattaro.
Wane aiki ƴan sandan jihohi za su yi?
Sashe na 214 na ƙudurin dokar ya ce majalisar dokokin ƙasar ce za ta fitar da tsarin aiki ƴansandan jihohin, da yadda tsarin aikin zai kasance tsakanin ƴansandan gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma ka'idojin da za su tafiyar da hukumomin.
Dakta Kabiru Adamu na kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, mai nazari kan lamuran tsaro a nahiyar Afrika, ya ce a yanzu ƙudurin da aka amince da shi ya cire amfani da kalmar "tarayya" a sunansu, "sai dai a kira su da ƴansanda kawai".
Amma ya ce tsarin ba zai fara aiki ba har sai an samu amincewar majalisun ƙasar da jihohi sannan shugaban ƙasa ya sanya hannu a kai, wanda shi ne matakin farko a yanzu.
A ganinsa wannan yunƙuri na kafa ƴansandan jihohi siyasa ce kawai.
"Gwamnatin da ke ci yanzu, cikin ƙudurinta, ta yi alƙawarin za ta sauya fasalin ƴansanda, to idan ta samu ta yi wannna ɗin, za ta iya amfani da shi a matsayin dalilin cewa ta yi alƙawari ta cika," in ji Kabiru Adamu.
Sai dai masanin ya ce ba lallai kafa ƴansanda jihohin ya iya magance matsalar tsaron ƙasar kamar yadda ake sa rai ba.
"Yawancin abubuwan da suke jawo matsalar tsaron, matsaloli da suke da nasaba da shugabanci, misali yaran da ba sa zuwa makaranta...ba matsala ba ce wadda ƴansanda jihohi za su iya magancewa, sai idan an samu gwamnati wadda ta fahimci matsalolin ta magance su."
Gwamnoni ne za su riƙa naɗa kwamishinan ƴansandan a jihohi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sashe na 215 na dokar ya ce jami'i mai muƙamin kwamishan ƴansanda ne zai jagoranci rundunar ƴansandan a kowace jiha, kuma gwamna ne ke da ikon naɗa shi bisa shawarar hukumar kula da ƴansanda ta ƙasa, inda majalisar dokokin jihar za ta tantance da tabbatar da naɗin.
Gwamnonin kuma suna da ikon bayar da umarni da suka shafi doka da oda da tabbatar da tsaron al'umma.
Sai dai idan kwamishinan ƴansanda ya ga cewa umarnin ya ci karo da tsarin aikin ɗansanda, za a miƙa buƙatar duba lamarin ga hukumar kula da harkokin ƴansanda ta ƙasar, wadda za ta yanke hukunci na ƙarshe.
Wannan sashen dai ya ba gwamnoni iko kan ƴansandan jihohi da kuma amfani da su a wasu buƙatunsu da abin da masana ke ganin watakila a iya shigar da su cikin harkokin siyasa.
- Tinubu ne zai naɗa babban sufetan ƴansandan Najeriya
Sai dai ƙudurin dokar ya ba shugaban ƙasa damar naɗa babban sufetan ƴansandan Najeriya bisa shawarar hukumar kula da ƴansanda ta ƙasa, inda majalisar dokokin ƙasar za ta tantance tare da tabbatar da naɗin.
IGP ne shugaban ƴansanda a faɗin ƙasar kuma yana da iko da sauran rundunoni a jihohi.
Sashe na 216A ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta riƙa bayar da tallafin kuɗi ga ƴansandan jihohi bisa amincewar majalisar dokokin ƙasar.
Hakan na nufin duk da haka, gwamnatin tarayya na da iko kan harkokin ƴansandan jihohin da kuma abubuwan da suka shafi tsaron ƙasa.
Me ya sa wasu ke fargaba kan ƙirƙiro ƴansandan jihohi?

Asalin hoton, Getty Images
Wasu masu sharihi na ganin samar da ƴansandan jihohi zai iya haifar da matsaloli da dama fiye da gyaran da ake tunanin za a samu ta fuskar tsaro.
Ƙungiyoyin farar hula musamman na kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya da ma na ƙasashen waje sun yi ta sukar matakin.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta ƙasa da ƙasa International Human Right Commission- Relief Fund Trust na cikin waɗanda suka fito suka nuna fargaba game da samar da ƴansandan jihohi a Najeriya.
Ƙungiyar ta yi suka ne saboda illolin da take ganin suna tattare da hakan ta fuskar tsaro da kare haƙƙin ɗan'adam, ciki kuwa har da fagabar ana iya yin amfani da ƴansandan na jihohi a harkokin siyasa wajen muzguna wa abokan hamayya.
"Muna ganin gwamnoni ko ƴansiyasa za su iya amfani da su wajen siyasantar da tsarin musamman wajen amfani da ƴansandan wajen murƙushe abokan hamayya da kuma haifar da rikici da bambanci na kaɓila da addini," in ji Abdullahi Bakoji Adam, shugaban IHRC Relief Fund Trust reshen Najeriya
Ƙungiyar ta kuma yi la'akari da yadda wasu jihohin ba su da ƙarfin kuɗin kula da hidimar ƴansanda, wanda take ganin hakan zai iya ƙara yawaitar cin hanci da rashawa.
Yadda za a ci moriyar ƴan sandan jihohi
Dakta Kabiru Adamu ya ce ƴansanda jihohin za su fi tasiri ne a matakin ƙananan hukumomi da karkara, inda ba kasafai aka cika ganin ƴansanda gwamnatin tarayya ba.
Ya ce matakin zai taimaka wajen magance rashin isassun jami'an tsaro a ƙasar.
"Duk wani ɗan Najeriya ya sani, idan ka bar birane ka je ƙauyuka, za ka ga babu isassun jami'an tsaro."
Amma akwai wasu matsaloli da ya ce za su iya haifar da cikas ga tsarin. Daga cikin matsalolin akwai:
- Matsalar siyasa
- Matsalar tsaro
- Matsalar tattalin arziki
- Matsalar amantakewa
Ya ce: "Dole ne a magance su" idan ana son wannan tsarin ya yi tasiri.
Wasu masana na ganin idan har gyara ake so ana iya inganta jami'an tsaron da ake da su tun daga ƴansanda da masu tsaron farin kaya ƴan civil defence ta hanyar ƙara musu makamai na zamani da horo da kuma inganta rayuwarsu.
Tsaro zai inganta idan aka kafa ƴansanda jihohi - Gwamnati

Asalin hoton, Policeng/X
Ita dai gwamnatin Najeriya ta ce samar da yansandan jihohi wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ƙasar ke yi na inganta harakokin tsaro.
Shugaban Tinubu ya sha nanata cewa gwamnatinsa za ta samar da ƴansandan jihohi a matsayin wani mataki na magance matsalolin tsaron da Najeriyar ke fuskanta.
Sufeto-Janar na 'yansandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya kafa wani kwamiti wanda zai yi nazari kan batun da ya ce zai karfafa tsarin tsaron cikin gida na Najeriya da inganta ayyukan 'yansanda ta hanyar kai shi kusa da jama'a.
Ya ƙara da cewa an ɗora wa kwamitin alhakin yin nazari kan ayyukan yansanda a ciki da wajen Najeriya da tantance buƙatun tsaro na al'umma da kuma bayar da shawara kan tsare-tsaren da suka dace wajen kafawa.
Mece ce makomar ƴansandan tarayya?
Ƙudurin dokar ya ba da damar ci gaba da amfani da ƴansandan gwamnatin tarayya duk da ƴansandan jihohin, inda za su ci gaba da aiki tare da taimakawa juna a fannoni daban-daban.
Ƴansanda gwamnatin tarayya za su ci gaba da kula da tsaron al'umma a faɗin ƙasar kamar yadda doka ta tanada.
Ƙudurin bai rushe yadda tsarin aikin ɗansanda yake a yanzu ba. Sai dai tsarin zai ci gaba da aiki ne kamar yadda ake yi a sauran ƙasashe na kula da tsaron ckin gida a jihohi, sai dai idan abu ya fi ƙarfinsu.
Alal misali, idan ana taka doka da oda, gwamna zai iya buƙatar tallafin ƴansandan tarayya ko kuma suna fama da matsalar shugabanci ko rashin kuɗi. Kuma kafin su tallafa sai an samu amincewar hukumar kula da ƴansanda ta ƙasa.











