Yadda mutuwar Janar Rabe Abubakar a hannun ƴan bindiga ta yamutsa hazo a Najeriya

Janar Rabe Abubakar

Asalin hoton, NDHQ

Bayanan hoto, Janar Rabe Abubakar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya a hannun masu garkuwa da mutane ta haifar da ce-ce-ku-ce tare da sake jawo hankalin jama'a kan matsalar tsaron da ke ci gaba da addabar wasu sassan Najeriya.

Janar Abubakar, wanda ya taba rike mukamin Daraktan Watsa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, ya rasu ne bayan shafe kwanaki yana tsare a hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da shi tare da matarsa a Jihar Katsina.

Labarin rasuwarsa ya bazu cikin sauri a fadin kasar, inda ya janyo martani daga ƴan kasar, da masana harkokin tsaro.

Mutane da dama sun bayyana alhini tare da nuna damuwa kan yadda babban jami'in tsaro kamarsa, da ya shafe shekaru yana aiki a fannin tsaro har ya zama mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya zai iya fadawa hannun masu garkuwa da mutane har ya rasa ransa a hannunsu.

Ga wasu 'yan Najeriya, mutuwar Janar Abubakar ta zama wani abin da ya sake fito da matsalar tsaro fili. Sun ce lamarin ya nuna cewa matsalar garkuwa da mutane ta kai wani mizani da kowa ma zai iya fadawa cikin hadari ba tare da la'akari da matsayinsa a cikin al'umma ba.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce mutuwar tsohon janar din ta kara jaddada yadda matsalar garkuwa da mutane ke ci gaba da zama daya daga cikin manyan kalubalen tsaro a Najeriya. A cewarsu, duk da hare-hare da jami'an tsaro ke kai wa maboyar 'yan bindiga da kuma wasu nasarori da aka samu a lokuta daban-daban, har yanzu masu aikata irin wadannan laifuka na ci gaba da gudanar da ayyukansu a kasar.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Barista Abdu Bulama Bukarti, mai sharhi kan al'amuran tsaro a Afrika, ya ce akwai wani babban darasi dangane da mutuwar Janar din.

''Babban darasin shine yan bindigar nan suna ganin sun yi karfin da za su iya tunkarar kowa, kuma suna ganin sun yi karfin da za su iya tunkarar gwamnati, a ce tsohon Janar din soja, kuma tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya za a yi wa irin wannan cin kashi? har su yi dalilin mutuwarsa?''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya kara da cewa ''Mutanen nan fa kullum kara karfi suke yi, kuma ba a kan Janar Rabe aka fara ba, ba a jima ba aka kama Janar Maharazu Tsiga, ya yi kwana 56 a hannun 'yan bindiga a bara, kuma rahotanni suka tabbatar da sai da aka tara makudan kudi aka ba wa 'yan bindiga kafin a sake shi, amma bamu ga an kama wadanda suka tsare shi ba''.

''Haka kuma kafin shi 'yan bindiga sun tare Major Janar Alkali a hanyar Jos, suka kashe shi suka jefa gawarsa a rijiya kuma daga karshe sai da aka gudanar da bincike aka gano gawar, aka kama wadanda ake zargin sun kashe shi har suka amsa laifinsu, suka kuma nuna rijiyar da suka jefa shi a ciki har aka nuna mana hotuna da bidiyo, amma yanzu kusan shekaru nawa, har yau ba a hukunta su ba, don haka me ake koya wa 'yan bindigar nan ? shine za ku iya taba Janar din soja, za ku iya kashe shi babu abun da zai same ku, kuma wallahi idan aka ci gaba da tafiya a haka za su ci gaba, har ma su koma kan ministoci da Sarakuna da sauran manyan mutane'' inji shi.

Janar Rabe Abubakar

Asalin hoton, NDHQ

Bayanan hoto, Janar Rabe Abubakar

Shima wani dan jarida mai binciken kwakwaf kan ayyukan ƴan bindiga a Najeriyar Munir Fura Girke, ya ce akwai abun ta'ajibi yadda rundunar sojin kasar ta kasa ceto Janar din duk da cewa an san wurin da ake tsare da shi.

A kafafen sada zumunta ma jama'a na ta tafka muhawara kan lamarin, inda mutane da dama ma ke ta bayyana cewa idan har babban hafsan soja ma bai tsira daga hannun masu garkuwa da mutane ba, to ina kuma ga su?.

Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana mutuwar Janar Abubakar a matsayin wata babbar asara ga kasa, yayin da wasu suka ce lamarin ya kamata ya zama abin da zai sa hukumomi su sake duba dabarun da suke amfani da su wajen yaki da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Kafin rasuwarsa, wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna Janar Abubakar tare da matarsa suna neman taimako yayin da suke tsare a hannun masu garkuwa da su.

Daga baya an sake ganin bullar wasu hotunansa suna yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna ciwo a kafarsa.

Ita dai rundunar Sojin Najeriya ta bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga rundunar da kuma kasa baki daya.

A cikin sakonnin ta'aziyya da suka biyo bayan mutuwar tasa, rundunar ta yaba da gudunmawar da Janar Abubakar ya bayar a lokacin da yake aiki, tare da jaddada kudurinta na ci gaba da yaki da masu aikata laifuka a fadin kasar.

Wadanda suka san shi, sun bayyana shi a matsayin mutum mai kishin kasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Najeriya hidima. Sun ce rasuwarsa ta bar gibi ba kawai ga iyalansa ba har ma ga rundunar da ya yi wa aiki tsawon shekaru.

Sai dai ga wasu 'yan Najeriya, mutuwar tsohon janar din ta sake tayar da tambayoyi kan tasirin matakan tsaro da ake dauka. Wasu na ganin cewa har yanzu akwai bukatar kara karfafa hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro, al'ummomi da hukumomin gwamnati domin magance matsalar garkuwa da mutane da sauran laifukan da suka shafi tsaro.

Masana na cewa lamarin na iya kara matsin lamba ga gwamnati da hukumomin tsaro domin sake zage dantse a kokarin da suke yi na dakile ayyukan 'yan bindiga. Haka kuma suna ganin mutuwar Janar Abubakar za ta ci gaba da kasancewa daya daga cikin abubuwan da za su rika tunatar da jama'a girman kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta.

Yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike da kuma kokarin cafke wadanda ake zargi da hannu a lamarin, mutane da dama na ganin cewa mutuwar Janar Rabe Abubakar ta wuce labarin rasuwar tsohon hafsan soja kawai. A ganinsu, ta zama wata alama da ke nuna irin matsalolin tsaro da har yanzu suke bukatar mafita mai dorewa a Najeriya.