Zai wuya kungiyata ta lashe Champions League - Sterlin

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun tabbatar da cewa kocin Arsenal Unai Emery na zawarcin dan wasan bayan RB Leipzig Dayot Upamecano, tun kafin sabuwar kakar hada-hadar 'yan wasa ta kama, sai dai babu lissafinsa cikin kasafi. In ji jaridar (Sun)
Manchester United na ci gaba da zawarcin dan wasan Leicester City James Maddison, mai shekara 22, kan kudi Fan miliyan 80. (Mail)
Dan wasan Barcelona Ousmane Dembele, na daga cikin 'yan wasan gaba uku da kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ke zawarcin su. domin kara gina kungiyarsa (Manchester Evening News)
Solskjaer na kwadayin dan kasar Norway Martin Odegaard, mai shekara 20, cikin sabuwar tawagarsa - sai dai dan wasan tsakiyar Real Madrid din kungiyoyin Arsenal da Liverpool da Manchester City na zawarcinsa. (Sun)
Tottenham na fargabar Harry Kane, mai shekara 26, zai shiga sahun manyan 'yan wasanta da ke kokarin ficewa. (Times - subscription required)
Dan wasan gaban Manchester City da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 24, ya yi amannar cewa lokaci suke bukata kafin kungiyarsa ta lashe gasar cin kofin nahiyar zakarun turai ta Champions League, sai dai ya bukaci abokan aikinsa da su kara hakuri da kuma dagiya. (Mirror)
Shugaban Tottenham Daniel Levy ya ce za su ci gaba da bai wa Kocin Spurs din Mauricio Pochettino goyon baya, duk da cewa da kafar hagu kungiyar ta fara fafatawa a kakar wasa ta bana, inda ake ganin hakan ka iya shafar kujerarsa. (Telegraph)
Tsohon dan wasan Tottenham da Manchester United Dimitar Berbatov ya ce akwai yiwuwar Levy za su yi zaman tattaunawa da Pochettino "a makon nan" domin lalubo hanyoyin dakile matsalolin da suka dabaibaye Spurs din. (Star)
Shi kuwa dan wasan bayan TottenhamToby Alderweireld cewa ya yi kungiyarsa ta samu koma baya karon farko cikin shekara biyar, yayin da take da maki biyar a bayan Liverpool a teburin Premier, yayin da aka yi waje da su a gasar Carabao Cup, da kuma shan kayen da suka yi a hannun Bayern Munich da ci 7-2 a gasar Champions League. (Mirror)
Tsohon kocin Juventus Massimiliano Allegri na kokarin koma wa kungiyar a kakar wasa ta badi bayan da ya tafi hutun shekara guda. (Sun)
Shi kuma tsohon kocin Chelsea Maurizio Sarri na fatan sake haduwa da dan wasan tsakiya N'Golo Kante. Kocin Juventus din dai na ganin cewa zai sayo dan wasan kan kudi Fan miliyan 70m. (Mail)
Kocin Ingila Gareth Southgate na ganin cewa akwai yiwuwar dan wasan bayan Chelsea Fikayo Tomori, zai shiga tawagar da za su wakilci kasar a wasan cancantar shiga gasar Euro 2020 da za su fafata da Jamhuriyar Czech da Bulgaria. (Telegraph)
Ita kuwa mai tsaron ragar Ingila Carly Telford, 32, cewa ta yi ta yi mamakin yadda al'ummar kasarta ke yabon tawagar 'yan wasansu, bayan da suka gaza tsallaka wa zagayen karshe na gasar cin kofin duniya ta mata. (Guardian)
Kocin Arsenal Unai Emery ya ce dan wasan Ivory Coast Nicolas Pepe yana bukatar karbar horo sosai kan yadda zai rika takawa kungiyar leda, wannan na zuwa ne bayan da dan wasan mai shekara 24 ya sanya hannu kan kudi Fan miliyan 72 na kwantaragin da Arsenal din ta sayo shi daga Lille. (Mirror)
Chelsea kuwa na kokarin cimma yarjejeniya da dan wasan tsakiyar Monaco Benoit Badiashile, mai shekara 18, da zarar wa'adin dakatarwar da aka yi wa kungiyar ya kawo karshe. (Le 10 Sport, via The Sun)
West Ham ta sanya Fan miliyan 80 a matsayin farashin da za ta sayo dan wasan Declan Rice, mai shekara 20, yayin da dan wasan ke sha'awar barin kungiyarsa. (Star)
Bayern Munich ta kasar Jamus kuwa na zawarcin Jude Bellingham, inda sha'awar dan wasan mai shekara 16 ya taka mata leda daga tsakiya a gasar Bundesliga ta badi . (Sun)
Juventus ta yanke shawarar tattaunawa da Blaise Matuidi mai shekara 32 domin tsawaita kwantaraginsa, shekara guda ya rage wa'adin da suka cimma da dan wasan a baya ya kawo karshe. (Calciomercato)











