Juventus za ta karbe Serie A na Inter na 2006

Juventus Inter

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kungiyar Juventus ta shigar da sabuwar kara kan cewar sai an ba ta kofin Serie A na 2005/06 da Inter Milan ta lashe.

Juventus ce ta yi ta daya a kakar 2006, amma aka bai wa Inter kofin, saboda samunta da aka yi cikin rikicin cefanar da wasa, inda aka hukunta kungiyoyi biyar da suke buga Serie A.

Wannan karon Juventus ta shigar da kara gaban wata kotun sauraren kararrakin wasanni da ke Italiya, bayan da a baya ta sha yin hakan amma ba ta yi galaba ba.

AC Milan ce ta yi ta biyu a 2005/06, amma saboda an sameta da hannu cikin badakalar aka bai wa Inter Milan kofin a kakar.

A kuma kakar Juventus ta kammala Serie A da maki 91, AC Milan ta hada maki 88, ita kuwa Inter Milan ta uku keda maki 76.

A lokacin aka hukunta Juventus da AC Milan da Fiorentina da Lazio da Reggina daidai da laifin da suka aikata.

Hukuncin ya shafi Juventus daga mataki na daya ta koma ta karshe a kasan teburi ta koma buga gasar Serie B, ita kuwa AC Milan aka karbi maki 30 a wajenta.

Hakan ne ya sa Milan ta koma ta uku a teburi aka bai wa Inter kofin Serie A na kakar 2005/06 lokacin da Roberto Mancini.

Juventus wadda take ta biyu a kan teburin bana za ta karbi bakuncin Inter Milan a gasar Serie A ranar Lahadi.