FA ta tuntubi Man City kan kalaman wariyar da Silva ya yi

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafar Ingila ta Football Association (FA) ta rubuta wa Manchester City wasika tana kokarin jin ta bakinta game da sakon Twitter da Bernardo Silva, dan wasan tsakiyarta, ya wallafa.
Silva ya kwatanta abokin wasansa Benjamin Mendy da wani hoton jikin alawar Conguitos - wata 'yar matumbirar agwagwa ce baka da kamfanin alawar ke amfani da ita a jikin jakar alawar da ake sayarwa a Portugal da kuma Sifaniya.
Tun farko kungiyar masu gangamin yaki da wariyar launin fata ta Kick It Out ta yi kira ga FA da ta dauki mataki bayan hukumar ta tabbatar da cewa tana binciken lamarin.
Zuwa yanzu dai Manchester City ba ta ce komai ba kan batun.
"Ranmu ya baci sosai da ganin sakon da Bernardo Silva ya wallafa," in ji Kick It Out.
Ya wallafa sakon ne da karfe 12:44 agogon Nijar da Najeriya ranar Lahadi amma sai ya goge shi da karfe 13:30.
Daga baya Silva ya sake wallafa cewa: "Shikenan mutum ba zai yi wasa da abokinsa ba."
Dan wasan bayan Faransa Mendy da Silva abokai ne na kusa kuma sun yi wasa tare a kungiyar Monaco tare kafin dukkaninsu su koma City a 2017.
Mendy ya mayar da martani ga sakon amma bai nuna alamun bacin rai ba. Kazalika an nuna wa FA wani bidiyo na Silva suna kakaci tare da Mendy.










