Akwai jan-aiki a gabanmu a La Ligar bana – Suarez

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaban Barcelona Luis Suarez ya ce "akwai jan-aiki" a gaban kungiyarsu a La Liga ta bana biyo bayan rawar da suka fara takawa mafi muni cikin shekara 25.
Tawagar Ernesto Valverde, wadda ita ce zakarar La Liga sau hudu cikin biyar na baya bayan nan, ta sha kashi a karo na biyu a bana a hannun Granada ranar Asabar kuma ta koma mataki na bakwai.
Maki bakwai da Barca ta samu a wasa biyar na bana shi ne mafi karanci da ta samu a farkon gasar La Liga tun a shekarar 1994/1995 a karkashin mai horarwa Johan Cruyff.
"Rashin nasarar abin damuwa ne kwarai, babu dadi," Suarez ya shaida wa AS.
"Ya kamata mu kalli abin da niyyar gyara abubwa da dama. Akwai jan-aiki a gabanmu amma irin wadannan wasannin su ne za su ba ka nasara a lig.
"Lallai sai mun kara azama idan muna son mu ci lig."
Barcelona tana fama a wasannin waje bayan shafe wata biyar ba tare da cin wasa ba, sannan kuma ba ta ci kwallo ko daya ba a wasa shida na baya-bayan nan a La Liga.
Teburin La Liga:

Shot daya kacal ta yi a cikin minti 90 na wasanta da Granada duk da shigowar Messi bayan hutun rabin lokaci - shi ne wasansa na farko a La Liga bayan dawowa daga jinyar rauni a idon-sawunsa.
Suarez ya ce kungiyarsu tana bukatar sauya salo wurin tunkarar wasannin waje domin su kara karfi a gabansu.
"Abin da ya kamata mu duba shi ne yadda muke buga wasa idan mun je bakunta saboda karancin cin kwallonmu ya yi yawa," in ji Suarez.
Ya kara da cewa: "Barcelona ne fa mu, wajibi ne mu ci wasa a waje - bai kamata mu ci gaba kamar yadda muka fara ba."











