Mikel Obi ya yi ritaya daga buga wa Super Eagles wasa

Asalin hoton, Getty Images
Kaftin din Super Eagles ya tabbatar da jingine takalmansa daga buga wa Najeriya wasa.
Dan wasan tsakiyar mai shekara 32 ya buga wa Najeriya wasa 89 tun daga shekarar 2005 zuwa 2019, inda ya zura kwallo shida kacal.
Tun da farko dai ya shaida wa BBC cewa gasar cin Kofin Afirka ta 2019 ita ce gasar karshe da zai halarta a jesin fari-kore-fari ta Super Eagles.
Ba dadewa ne kuma ya kulla yarjejeniya da kungiyar Trabzonspor ta kasar Turkey.
"A matsayina na dan shekara 32 ya kamata na yi ritaya daga buga wa kasata wasa domin bai wa matasa dama, wadanda suka yi namijin kokarin lashe tagulla a AFCON 2019," Mikel ya bayyana a shafinsa na sada zumunta.
"A kasar Masar na fara harkar kwallota kuma a nan na kammala. A shekarar 2006 na fara buga wa kasata wasan farko a wata gasa.
"Gasar AFCON 2019 ita ce gasa ta karshe da zan halarta tare da kungiyar Super Eagles.
"Na fara buga wa Najeriya wasa a 2003 a kungiyar 'yan kasa da shekara 17, kuma ina godiya ga Super Eagles bisa damar da suka ba ni na haskaka a idon duniya da kuma wasanni masu kayatarwa da na buga a matakin kasa-da-kasa."

Asalin hoton, Getty Images
Matakin nasa ya zo ne jim kadan bayan kocin Najeriya Gernot Rohr ya bayyana cewa yana fatan Mikel zai taimaka wa kungiyarsa wurin samun cancantar shiga Kofin Duniya na 2022 wanda za yi a Qatar.
"Ina jinjina ga dukkanin magoya bayana a Najeriya da ma kasar bisa yardar da suka nuna min da kauna a tsawon shekara 15."
Mikel Obi ya lashe kofin kasashen Afirka a shekarar 2013, kuma yana cikin tawagar Super Eagles da ta zo ta uku a gasar ta shekarun 2006 da kuma 2010.
Kazalika, yana cikin tawagar 'yan wasan da suka kai Najeriya wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekara 20, inda ya zo na biyu a matsayin dan wasan da ya fi kowa taka rawar gani bayan Lionel Messi na Argentina.
Sannan kuma ya jagoranci matasan 'yan wasan Najeriya da suka lashe tagulla a gasar Olympics ta 2016 a birnin Rio na kasar Brazil.
Wasa biyu kacal ya buga a gasar AFCON ta 2019 da za a kammala a yau Juma'a a kasar Masar, inda kungiyar ta zo ta uku kuma ta dawo gida da kyuatar tagulla.











