Wadanne kungiyoyi ne za su fara Gasar Zakarun Turai?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A ranar Talata ne kungiyoyin gasar Firimiya biyu, Liverpool da Spurs, za su fara wasansu a gasar Zakarun Turai, a ranar da ake fara gasar ta wannan kakar.

Tottenham ce za ta fara karawa da Inter Milan ne da misalin karfe 5:55 agogon Najeriya, a kasar Italiya.

Ita kuwa Liverpool za ta karbi bakuncin PSG ne a gida a wasan da za su buga karfe 8:00 na dare agogon Najeriya.

Kungiyar Barcelona ta Messi kuwa za ta karbi bakuncin PSV Eindhoven a wasan da za su yi karfe 5:55 na yamma agogon Najeriya.

Borussia Dortmund za ta kai ziyara Club Brugge ne a wasan da za su fafata da karfe takwas agogon Najeriya.

A karfe 8:00 agogon Najeriya da Nijar din ne dai Monaco za ta kara da Atletico Madrid, Red Star Begrade da Napoli, Shalke da FC Porto ita kuma Galatasaray za ta kara da Locomotic Moscow.

Dan wasan gaba na kungiyar Spurs, Harry Kane, ya ce kungiyarsa tana bukatar ta wuce inda ta kai a gasar bara.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Kane ya ce lokaci ya yi da ya kamata kungiyarsa ta sake zage dantse.