Hoton mai tsire a Kashmir ya lashe gasar hotunan abinci ta duniya a 2022

An wallafa

Wani hoton mai abinci kan titi ya lashe kyautar hotuna ta duniya ta Pink Lady ta shekarar 2022.

Debdatta Chakraborty aka bayyana a matsayin wanda ya lashe kyautar ta bana a hoton da aka yi wa take da Kebabiyana, da aka ɗauka a Srinagar, yankin Kashmir.

Wani mai ɗaukar hoto na Indiya ne ya ɗauki hoton a kan titi da dare, yayin da mai tsiren ke gashi.

"A wannan duniyar ta yau, fiye da ko yaushe, muna samun jin daɗi da soyayya," a cewar wadda ta ƙirƙiri kyautar Caroline Kenyon.

"Akwai abubuwa da dama a wannan - hoton da aka ɗauka da kyau ya nuna hayaki da dare yayin da yake koƙarin bayar da abinci.

"Hoton, mai sauki amma babba, ya ƙayatar da mu."

Dubban mutane ne suka shiga gasar daga ƙasashe 60 a sassan duniya, kuma an sanar da wanda ya yi nasara ne ta intanet.

Ga wasu daga cikin hotunan da suka yi nasara da kuma bayaninsu daga waɗanda suka ɗauki hotunan.

Champagne Taittinger abincin biki: Ƙwarewar gargajiya, daga Chen Ying, China

Abinci kan tebur: Putting On The Ritz, daga John Carey, Birtaniya

Bikin Fujifilm: Central Park, daga Yuliy Vasilev, Bulgaria

Kyautar Claire Aho ta mata masu ɗaukar hoto: A tebur, daga Marguerite Oelofse, Afirka ta Kudu

A Phone: Shanya kifi, daga Kasia Ciesielska-Faber, Birtaniya

Siyasar Abinci: Where Dreams Fly Away, Daga K M Asad, Bangladesh

Kyautar abinci: Summer Veg Tart, daga Carolin Strothe, Jamus

Sarrafa kifi, daga Rupkotha Roy Barai, Bangladesh

Wanda ya lashe kyautar shekara ta Errazuriz Wine - daga Jon Wyand, Birtaniya

Lambun karas, daga Paolo Grinza da Silvia Vaulà, Italiya

Hoton shekara na Pink Lady (Kudu maso gabashin Asiya): Anchovy Catching, daga Thien Nguyen Ngoc, Vietnam

Dukkanin hotuna daga bikin gasar hotuna ta 2022 ta Pink Lady. A ranar 20 ga Nuwamba za a nuna waɗanda suka yi nasara a Bristol, zuwa 12 ga Disamban 2022.