Akwai hujjojin da ke nuna Isra'ila ta aikata laifuffukan yaƙi a Gaza - Rahoto

    • Marubuci, David Gritten
    • Marubuci, Stephanie Hegarty
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wani kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya zargi Isra'ila da kai hare-hare kan yara Falasɗinawa da gangan, lamarin da kwamitin ya ce aikata kisan kiyashi ne da laifuffukan yaƙi a Gaza da cin zarafin bil'adama a Yamma Kogin Jordan.

A cikin sabon rahoton, kwamitin ya yi zargin cewa da gangan hukumomin Isra'ila da jami'an tsaronta suka "aikata ayyukan da suka jawo mutuwa da kuma mummunar illa ga lafiyar dubban yara Falasɗinawa," kuma an ci gaba da kashe-kashen duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktobar 2025.

Kwamitin ya ce yana da ƙwararan hujjojin da suka ayyana waɗannan abubuwan da Isra'ila ta yi a matsayin "wata dabara ta lalata makomar Falasɗinawa a Gaza ta hanyar kai hari kan yaransu."

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta yi watsi da rahoton, inda ta ce rahoton "ƙage ne marar tushe" kuma "wannan farfaganda ce da kwamitin ya taɓa fitarwa a baya."

Rundunar sojin Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza ne bayan harin da Hamas ta jagoranta a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda aka ce kimanin mutum 1,200 suka mutu yayin da aka yi garkuwa da wasu 251.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza da Hamas ke gudanarwa ta ce, tun daga lokacin hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 73,035 a Gaza, ciki har da yara sama da 21,280, kuma MDD ta ce za a iya dogaro da alkaluman ma'aikatar.

Akwai hujjojin da ke nuna Isra'ila ta aikata laifuffukan yaƙi a Gaza - kwamitin MDD

Majalisar Dinkin Duniya ce ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan yankunan Falasɗinu da Isra'ila da MDD ta kafa a shekarar 2021 ne domin binciken zarge-zargen karya dokokin yaƙi da na haƙƙin ɗan adam.

Sai dai kwamitin mai mambobi uku ba ya magana ne a madadin Majalisar Ɗinkin Duniya kai tsaye.

A watan Satumban bara, kwamitin ya zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi kan Falasɗinawa a Gaza. A wani rahoto da ya fitar, ya ce akwai hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa hukumomin Isra'ila da jami'an tsaronta sun aikata huɗu daga cikin abubuwa biyar da yarjejeniyar Geneva na shekarar 1948 ta ayyana a matsayin kisan kiyashi. Isra'ila ta yi watsi da rahoton, inda ta ce rahoton cike yake da bayanan ƙarya.

A baya ma, kwamitin ya taɓa bayyana cewa Hamas da wasu ƙungiyoyin Falasɗinawa masu ɗauke da makamai sun aikata laifuffukan yaƙi da wasu manyan laifuffuka na dokokin ƙasa da ƙasa a harin da suka kai ranar 7 ga Oktoban 2023, kuma kwamitin ya ce su ma jami'an tsaron Isra'ila sun aikata laifuffukan cin zarafin bil'adama da kuma laifuffukan yaƙi a Gaza.

A watan Oktoban 2025, Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita wuta abayan da ƙoƙarin shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na kawo ƙarshen yaƙin.

Sai dai tun daga lokacin, ɓangarorin biyu ke ta zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar a lokuta da dama. Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce fiye da Falasɗinawa 1,020 ne suka mutu tun bayan cimma yarjejeniyar, ciki har da yara 265. Ita ma Isra'ila ta ce an kashe mata sojoji huɗu.

A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar tare da sabon rahoton a ranar Talata, ya ce girman hare-haren sojin Isra'ila a Gaza na ci gaba da haddasa "mutuwa, da kuma mummunar rayuwar ga yara Falasɗinawa fiye da kowane lokaci."

"Ko bayan tsagaita wutar da aka yi a watan Oktoban 2025, ana ci gaba da kashe yara da jikkata su da munanan raunuka. Isra'ila na ci gaba da ƙin mutunta yarjejeniya da kuma kariyar da dokokin ƙasa da ƙasa suka tanadar wa yaran Falasɗinawa., in ji shugaban kwamitin da ya fito daga India, Srinivasan Muralidhar

Muralidhar ya ƙara da cewa kare yara Falasɗinawa da inganta rayuwarsu haƙƙin al'ummar Falasɗinu ne.

Abin da sabon rahoton ya ƙunsa

Sabon rahoton kwamitin binciken ya yi zargin cewa Isra'ila ta riƙa kai hare-hare kai tsaye kan yara Falasɗinawa a Gaza da harbinsu a muhimman sassan jikinsu, da jirage marasa matuƙi ko amfani da maharba daga nesa.

Rahoton ya kuma ce an yi amfani da manyan makamai masu ƙarfi wajen kai hare-hare kan gidaje, makarantu da sansanonin ƴan gudun hijira, da wuraren da yara da dama ke taruwa.

Bugu da ƙari rahoton ya ce Isra'ila na da alhakin gaza kare yara Falasɗinawa daga hare-haren da sojojinta da kuma yahudawan ƴan kama wuri zauna ke kaiwa a Yammacin Kogin Jordan.

Ya ƙara da cewa an kama yara a Gaza da Yammacin Kogin Jordan, musamman matasa, kuma "an azabtar da su tare da cin zarafinsu a gidajen yari da wuraren da ake tsare mutane na Isra'ila."

Kwamitin ya ce ya tattara bayanai kan wasu lokuta da aka yi wa yara Falasɗinawa cin zarafi wariyar jinsi.

"Isra'ila da kai hare-hare kan asibitocin kula da jarirai da yara a Gaza," in ji rahoton.

Bugu da ƙari, rahoton ya zargi Isra'ila da amfani da yunwa a matsayin wata dabarar yaƙi, inda ya ce takunkumin da aka sanya kan shigar da kayan agaji zuwa Gaza ya haddasa matsanancin rashin abinci mai gina jiki tsakanin yara.

Hare-haren da aka kai kan makarantu, ya tilasta wa mutane yin ƙaura da kuma rufe cibiyoyin ilimi wanda hakan ya hana yara damar samun ilimi, lamarin da ya ce na iya lalata tubalan ilimi da rayuwar al'ummar Falasɗinu.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta yi Allah wadai da rahoton, tana mai cewa kwamitin binciken ba shi da wani tasiri, kuma manufarta ita ce ɓata sunan Isra'ila maimakon gano gaskiya.