Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda tafiyar minti biyar a wurin aiki za ta iya sanya ku farin ciki
- Marubuci, Michelle Roberts
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital health editor
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Yawancin rayuwar aiki tana gudana ne alhali mutum yana zaune a kan kujera, walau dai kana rubuta imel ko kuma kana mitin ta kafar Team. Sai dai kuma wannan ɗabi'ar zama na iya cutar da lafiyarmu.
Masana sun ce zama na dogon lokaci na iya ƙara haɗarin ƙiba, da kamuwa da cututtukan zuciya da ciwon sukari na nau'i na biyu.
Abin da bai fito fili ba shi ne sau nawa ya kamata ka riƙa tashi ka motsa yayin da kake ci gaba da aiki yadda ya kamata. Ta yaya za ka daidaita aikinka da motsa jiki?
Bisa wani bincike da Jami'ar Columbia ta yi wanda aka wallafa a wannan mako a mujallar British Journal of Sports Medicine, ɗaukar hutun minti biyar-biyar — ko abin da ake kira "guntun motsi" — a kowace awa shi ne hanya mafi dacewa kuma mafi sauƙi wajen inganta jin daɗi ba tare da rage ingancin aiki ba.
Ƙara ingancin aiki da karsashi da yanayi
Babban mai binciken, Keith Diaz, ya shaida wa BBC cewa a yanzu yawancin waɗanda suka manyanta suna shafe kusan kashi uku cikin huɗu na lokacin farkonsu na yini suna zaune ba tare da motsi ba.
Ya ƙara da cewa, duk da cewa shawarar gaba ɗaya ta "zama kaɗan ka motsa jiki sosai" daidai ce, mutane suna bukatar su san gwargwadon motsa jikin da ya dace.
"Labari mai daɗi shi ne, ɗaukar hutu na tafiya na minti biyar a kowace sa'a ya isa wajen inganta yanayin zuciya da rage gajiya. Kuma mutane sun ga wannan abu mai yiwuwa ne kuma mai sauƙin aiwatarwa," in ji Diaz.
Binciken ya yi nazari ne kan ma'aikata sama da 11,000 a Amurka — mafi yawancinsu masu ayyukan ofis inda suke yin awowi takwas zuwa tara a kowacce rana.
A makon farko, sun ci gaba da ayyukansu na yau da kullum sannan suka cika tambayoyin da ake yi musu na yau da kullum game da gajiya, yanayin da suke ji, da kuma yadda suke gudanar da aikinsu.
A cikin makonni biyu, an buƙace su da su riƙa ɗaukar hutu na tafiya a wurin aiki na minti biyar a kowace rabin sa'a, ko kowace awa, ko kuma cikin sa'a biyu, sannan su cika irin waɗannan tambayoyi.
Tafiya a kowane rabin awa ta taimaka wajen inganta yanayi da rage gajiya, amma ta rage ayyukan nasu na yau da kullum. Tafiya kowace sa'a biyu ta fi rashin tafiya gaba ɗaya, amma masu bincike sun gano cewa yin ƴar tafiya ta minti biyar a kowace sa'a ita ce ta fi kawo babban sauyi mai amfani kuma mai sauƙin aiwatarwa wajen ƙara yawan aiki da ingancinsa da kuma ƙara kuzari.
Daɗewa a zaune na tsawon awanni na iya zama ɗabi'a mai wahalar dainawa, in ji Diaz, inda ma'aikata da dama a binciken suka nuna damuwa kan abin da shugabanninsu ko abokan aikinsu za su ce game da hutunsu.
"Ko da yake yana iya zama kamar ba zai yi tasiri ba, amma hutu ta hanyar motsa jiki a zahiri na iya ƙara ingancin aiki," in ji Diaz.
"Yana iya inganta tunani na jagoranci musamman da shugabanni da kuma mayar da hankali da inganta tunani. Haka kuma yana sa mutane su ji sun fi samun nutsuwa da sabunta tunani."
Ya ce tafiya ba ta da wuya kuma ba dole ne sai an daina aiki ba; ya bayar da misalan amsa waya ko kuma shiga taro alhali kana tafiya ko yawo yayin yin kiran waya — ko a waje ko a cikin ofis.
Emily McGrath, babbar ma'aikaciyar jinyar zuciya a Gidauniyar Zuciya ta Biritaniya ta British Heart Foundation, ta yaba da sakamakon binciken, inda ta ce "ƙarin motsa jiki na iya inganta lafiyar gaba ɗaya."
Sai dai ta yi gargaɗi cewa, "binciken ya dogara ne da bayanan da mutane suka bayar da kansu kuma na ɗan gajeren lokaci ne, don haka ana buƙatar ƙarin bincike na dogon lokaci domin tabbatar da tasirinsa ga lafiyar zuciya."