Hoton mai tsire a Kashmir ya lashe gasar hotunan abinci ta duniya a 2022

Street food vendor surrounded by smoke as they prepare food

Asalin hoton, Debdatta Chakraborty

An wallafa

Wani hoton mai abinci kan titi ya lashe kyautar hotuna ta duniya ta Pink Lady ta shekarar 2022.

Debdatta Chakraborty aka bayyana a matsayin wanda ya lashe kyautar ta bana a hoton da aka yi wa take da Kebabiyana, da aka ɗauka a Srinagar, yankin Kashmir.

Wani mai ɗaukar hoto na Indiya ne ya ɗauki hoton a kan titi da dare, yayin da mai tsiren ke gashi.

"A wannan duniyar ta yau, fiye da ko yaushe, muna samun jin daɗi da soyayya," a cewar wadda ta ƙirƙiri kyautar Caroline Kenyon.

"Akwai abubuwa da dama a wannan - hoton da aka ɗauka da kyau ya nuna hayaki da dare yayin da yake koƙarin bayar da abinci.

"Hoton, mai sauki amma babba, ya ƙayatar da mu."

Dubban mutane ne suka shiga gasar daga ƙasashe 60 a sassan duniya, kuma an sanar da wanda ya yi nasara ne ta intanet.

Ga wasu daga cikin hotunan da suka yi nasara da kuma bayaninsu daga waɗanda suka ɗauki hotunan.

Short presentational grey line

Champagne Taittinger abincin biki: Ƙwarewar gargajiya, daga Chen Ying, China

A family making red coloured dumplings

Asalin hoton, Chen Ying

Bayanan hoto, "An ɗauka a wani gidan gona a ƙauyen Qianlian Village, gundumar Xiangyou, birnin Putian City, a lardin Fujian.
1px transparent line

Abinci kan tebur: Putting On The Ritz, daga John Carey, Birtaniya

"Irin wannan abincin a tebur babban abu ne da ba za ka manta ba a gidan cin abinci na Ritz."

Asalin hoton, John Carey

Bayanan hoto, "Irin wannan abincin a tebur babban abu ne da ba za ka manta ba a gidan cin abinci na Ritz."
1px transparent line

Bikin Fujifilm: Central Park, daga Yuliy Vasilev, Bulgaria

"Wannan hoton na cikin wani aiki da ake kira Foodtopia - wani abin da aka samar da kayan abinci"

Asalin hoton, Yuliy Vasilev

Bayanan hoto, "Wannan hoton na cikin wani aiki da ake kira Foodtopia - wani abin da aka samar da kayan abinci"
1px transparent line

Kyautar Claire Aho ta mata masu ɗaukar hoto: A tebur, daga Marguerite Oelofse, Afirka ta Kudu

A girl peeling fruit at a table, next to a bouquet of flowers

Asalin hoton, Marguerite Oelofse

Bayanan hoto, "Murna da asalin Afirka, daga Bafaranshe Henri Matisse.
1px transparent line

A Phone: Shanya kifi, daga Kasia Ciesielska-Faber, Birtaniya

Fish hanging outside to dry, in front of red buildings and a distant snow-covered landscape

Asalin hoton, Kasia Ciesielska-Faber

Bayanan hoto, "A Lofoten archipelago, Norway, kifi ya kasance yanayi na kasa. Ana shanyawa a wani wuri babba ba tare da gishiri ko hayaki ba
1px transparent line

Siyasar Abinci: Where Dreams Fly Away, Daga K M Asad, Bangladesh

"Wata yarinya na ɗibar ruwa tare da ƴar uwarta a a Chad Uddan a Dhaka, Bangladesh a watan Satumban 2021

Asalin hoton, K M Asad

Bayanan hoto, "Wata yarinya na ɗibar ruwa tare da ƴar uwarta a a Chad Uddan a Dhaka, Bangladesh a watan Satumban 2021

Kyautar abinci: Summer Veg Tart, daga Carolin Strothe, Jamus

Colourful vegetable tart

Asalin hoton, Carolin Strothe

Bayanan hoto, "Lokacin bazara tare da gayyaki – samansa ya kunshi tumatus da albasa da mozzarella,
1px transparent line

Sarrafa kifi, daga Rupkotha Roy Barai, Bangladesh

Two women and a child squat outside as they process fish

Asalin hoton, Rupkotha Roy Barai

Bayanan hoto, "Wasu matan ƙauye na sarrafa kifi da suka samo."
1px transparent line

Wanda ya lashe kyautar shekara ta Errazuriz Wine - daga Jon Wyand, Birtaniya

A man in a misty vineyard gathering prunings

Asalin hoton, Jon Wyand

Bayanan hoto, "Winter prunings gathered in the vineyards of Corton Hill in Burgundy."
1px transparent line

Lambun karas, daga Paolo Grinza da Silvia Vaulà, Italiya

"Hoton yana cikin jerin hotuna daga gidan abinci na Etiko Bistrot (Turin, Italiya) a madadin Plastikwombat - Photography Art and Concept."

Asalin hoton, Paolo Grinza and Silvia Vaulà

Bayanan hoto, "Hoton yana cikin jerin hotuna daga gidan abinci na Etiko Bistrot (Turin, Italiya) a madadin Plastikwombat - Photography Art and Concept."
1px transparent line

Hoton shekara na Pink Lady (Kudu maso gabashin Asiya): Anchovy Catching, daga Thien Nguyen Ngoc, Vietnam

An aerial photograph of smoke rising from a boat, with green nets in the water below

Asalin hoton, Thien Nguyen Ngoc

Bayanan hoto, "Haske da hayaki da ya turmuke a wani kwale-kwale na kamun kifi tare da abin kamun kifi mai launin kore a cikin ruwa lokacin da mai kamun kifi ya baza ragar kamun kifi

Dukkanin hotuna daga bikin gasar hotuna ta 2022 ta Pink Lady. A ranar 20 ga Nuwamba za a nuna waɗanda suka yi nasara a Bristol, zuwa 12 ga Disamban 2022.