Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dauko hoton tauraruwa mai nisan shekara biliyan 12.9 daga duniyarmu
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Abin hangen nesa na Hubble ya sake kafa tarihi bayan da ya ɗauko hoton wata tauraruwa mafi nisan da aka taɓa ganowa.
Hasken tauraruwar daga duniyarmu ta Earth ya kai nisan shekara biliyan 12.9.
An sanya mata suna 'Earende' wanda ke nufin 'tauraruwar safe' a tsohon harshen Ingilishi.
Masana kimiyya sun ce akalla nauyinta ya fi na rana sau 50, ta kuma nunka rana haske sau miliyoyi.
An ce ita ce tauraruwar da ta fi kowace nisa daga duniyarmu da aka taɓa ganowa zuwa yanzu.