Trump ya buƙaci Majalisa ta amince masa kashe dala biliyan 67 kan tsaro
Fadar White House ta buƙaci ƴan majalisar su amince ta kashe dala biliyan 87.6, akasari kan abin da ta kira "buƙatun gaggawa" da ke da alaka da yaƙin da Amurka ke yi da Iran, kwana guda bayan da majalisar dokokin ƙasar ta zartar da wani kuduri na tsawatarwa kan yaƙin.
Galibin kuɗin - $67bn - na Ma'aikatar tsaro ta Amurka ne, in ji Fadar White House.
Amma buƙatar na fuskantar ƙalubale a Majalisa.
Rikicin na Iran dai na fuskantar suka daga masu kaɗa ƙuri'a gabanin zaɓen tsakiyar wa'adi na Amurka da za a yi a watan Nuwamba, ko da yake a halin yanzu tsagaita wuta na aiki.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma samu saɓani tsakaninsa da wasu ƴan jam’iyyarsa ta Republican kan batun Iran, kuma an ruwaito cewa ya yi sa-in-sa da wani sanata a ranar Laraba.
Sanatan, Bill Cassidy na Louisiana, na ɗaya daga cikin tsirarun ƴan jam’iyyar Republican da suka bijire wa shugaban ƙasar a ranar Talata ta hanyar jefa ƙuri’a don zartar da wani mataki na neman ya dakatar da yaƙin ko kuma ya nemi amincewar majalisa kafin ya ci gaba da ɗaukar matakin soji.